New Post

Wednesday, 16 November 2016

HAKA SO YAKE 23-24

💕💕  *```HAKA SO YAKE```* 💕💕
            💗💗💗💗💗
               💕 *_23 -24_* 💕
              💗💗💗💗
           *Na*
    *_Rabee'at sk mash_*♥
           ```_And_```
       *_Mr, smiles_*😃

www.babymsh.blogspot.com

Tajima a hakan tanata sharar kukanta, saida aka fara kiran sallar azahar sannan tatashi jiki ba k'wari tanufi toilet tayi alwala sannan tafito ta fara sallah cikin natsuwa da kwanciyar hankali,
****            ****             ****
Bak'ar macece mai kyau da fasali tanad'an da 'yar kiba kad'an, zaune take cikin wani tangamemen falo,
  Falon ya k'awatu da kayar more rayuwa iri-iri, sanyi ac nadukanta tayi wani irin zaman kasaita tana kallon tv hankalinta kwance,

Ahmed yaturo kofar falon yashigo, yana tokara sandarsa harya karasa bakin kujera yazauna, sannan ya sauke nunfashi,

Matar ta dubesa bayan ta'ajiye remote d'in da ke hannunta "Yau kuma sallamar ma bazamu samu bane?"
Takarasa maganar tana kallonsa tare da girgiza masa kai,

Ahmed yasosa kansa cike da kunya ya dago kansa yadubeta yana murmushi "sorry umma wlh na mantane,"
Ya gyara zamansa sannan yace "Assalamu alaikum"
Umma ta amsa masa tana murmushi "yawwa my son kokaifa, daga ina naga kamar duk agajiye kake" umma tafada tana murmushi,
Ahmed yad'anja tsaki yana kokari jingina jikinsa a jikin kujera yace "wlh kuwa umma kamar kinsan a gajiye nake, jira kawai nake nadan hutu saina tashi naje d'aki nayi wanka"
Umma tace "ok aikam yafi kaje kayi wanka ka huta"  saida yayi mika sannan yace "wlh kuwa," yakara gyara zamansa akan kujera,
Umma sai kallon yanayin fuskarsa take, da dukkan alamu tagano cewa akawai magana abakinsa, tayi gyaran murya sannan tace "fuskarka takasa boye damuwar dake cikin zucuyarka, fad'amun meyeke damun Ahmaduna"
Ahmed yayi saurin d'ago kansa yana murmushi "hmm umma na kenan, kina saurin gano damuwata a duk lokacin dana kasance acikinta," yad'an tashi xaune yana kallon umma sannan yaci gaba dacewa "yau gamo nayi"
Umma tad'an zare edo "gamo kuma, !!! Allah yasadai bada aljanba "
Ahmed yana murmushi yace "a  a umma ba aljan bane, watace sunanta subeey, a bakin super market muka had'u yau"

Umma tad'an gimtse fuska domin ba dad'i maganar tayimataba, tayi ajiyar zuciya sannan tace "Ahmed!!, kai bazaka gaji bane, mata nawane suka cuceka, nafa gayama kafita harkar matan zamanin nan, basa yiwa mutum son tsakani da Allah, nifa ina tsoron karkaje wata rana wata tarabani dakai"
  Murmushi ahmed keyi yana kallon umma "umma wannanfa ba irinsu bace, kallo d'aya namata nagane cewa tanada natsuwa ga kamala da kuma ilimi, gaskiya umma ina ji a jikina wannan itace matar aurena, kuma itace tadace dani, domin itama iri nace"
Umma tayi saurin gyara zama tana cewa "itama gurguwarce "
Ahmed ya girgiza kai "a a ba gurguwa bace, sumul take da kafafunta biyu, saidai tanada matsala, amma bazan gaya miki matsalarba a yanzu sai tafiya tayi nisa, "
"Tohm shikenan, na yarda amma idan lokacin da zaka fad'amin yayi toh bazanso fad'aminba saidai kakawo min ita nagani da edona, naga meye matsalar surukar tawa "
Ahmed yana murmushj ya mike tare da riko sandarsa, yana tokarawa harya mike sannan yajuyo ya dube umma yace "shikenan na yarda, nizan wuce ciki nayi wanka, dan wlh jinake duk jikina ba dadi"
Umm tace "toh a fito lafiya, "

Tohm" Harya fara tafiya saikuma yakara juyowa ya dube umma yace "amm umma!! kicewa babba ladi ta had'amin tea kafin nagama wanka, domin harda yunwa nakeji bayan gajiyar,"
Umma tace "sarkin shan tea kaje zangaya mata," takarasa maganar da zolaya,
  Yana dariya yanufi d'akinsa,
Tunda ya bud'e kofar d'akin na zare edo ina kallon yadda d'akin ya tsaru ba datti saikace dakin macce komai a mazauninsa, d'akin yana kamshi turaren larabawa ga sanyi ac yana ratsa mutum,
  Yakarasa bakin gado yazauna tare da ajiye sandarsa gefe, yana furzar da iska abakinsa, a hankali naga yafarayin murmushi wanda shikansa baisan yanayiba, sunan subeey yasoma furtawa yana maimaitawa,
Yadda tagaya masa sunan yatuna, saida ya lumshe edo saboda yadda ya tuna irin zakin muryarta, bakaramin dadi yaji muryar tamasaba, zaiso yakarajin muryar,
  Yana murmushi yaciro wayarsa, number subeey yayi dailing sannan ya kara a kunnesa,
Matar nan mai turanci a cikin waya taturanta masa cewa wayar a akashe take, a hankali yasauke numfashi, zuciyara cike da zargin ayya kuwa ba numbar bogice subeey tabashi ba, sai kuma yatuna dacewa shifa da kansa yakarbi wayarta yakira kansa kuma saida yaga tashigo sannan ya mika mata wayarta,    
     Kara sauke nunfashi yayi sannna ya jefar da wayar kan gado, ya mike tsaye yana kallon d'akin zuciyarsa cike dadamuwa,
  Yajima a tsaye yanata tufka da warwara, sai cen yajanyo sandarsa dake gefen gado  sannan yanufi toilet,

Wanka yayi sosai, sannan yafito duk da shi bakine amma saida fatarsa tayi kalli saboda tsabar hutu dayake samu dakuma kwanciyar hankali,
  Bakin mirror yazo ya shafa mai sannan yataje sumar dake saman kansa, yagyarata sosai,
    bayan yagama yajuya yakarasa bakin drowar ya janyo wata doguwar jallabiya yasaka, sannan yakoma kan gado yazauna,
  Kara janyo wayarsa yayi, yakara kiran number subeey, sai yaji tafara ring, kamar yasaka ihu dan dad'i, yayi saurin gyara zamansa kamar mai shirin kwasar karatu,...

Via OHW📚📲

Related Posts:

  • A YINI ƊAYA 34-40[12:31pm, 20/10/2016] Amrah💓Pinky💓durling😘: 💀 *A YINI 'DAYA* 💀    👹💀            💀👹  … Read More
  • A YINI ƊAYA 26-33[5:18pm, 16/10/2016] Amrah💓Pinky💓durling😘: 💀 *A YINI 'DAYA* 💀    👹💀            💀👹  … Read More
  • HAKA SO YAKE 1-2💕💕  *```HAKA SO YAKE```* 💕💕             💗💗💗💗💗        &nbs… Read More
  • A YINI ƊAYA 41💀 *A YINI 'DAYA* 💀    👹💀            💀👹             &… Read More
  • A YINI ƊAYA 34-40[12:31pm, 20/10/2016] Amrah💓Pinky💓durling😘: 💀 *A YINI 'DAYA* 💀    👹💀            💀👹  … Read More

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts