💕💕 *```HAKA SO YAKE```* 💕💕
💗💗💗💗💗
💕 *_39 - 40_* 💕
💗💗💗💗
*Na*
*_Rabee'at sk mash_*♥
```_And_```
*_Mr, smiles_*😃
Yanaji suna dukan kofar suna fad'an kafito malam habu, Allah idan baka fitoba yanzu zamu kira Alhajin birni musanar dashi "
Haka yayi banza dasu saida suka gaji da kiransa sannan sukaga bayada imanin fitowa, suka tattara inasu inasu suka bakar kofar gidan,
Sai alokacin malam habu yasamu yasauke nunfashi sannan yakarasa cikin gidan,
Hauwa tana tsaye a tsakiyar gidan duk tanajin abinda ke faruwa,
Malam habu nashigowa ta bushe dadariyar mugunta,
Uffa baice da ita yafe mata ledar kwakin daya shigo dashi, sannan ya wuce d'akinsa,
Har yakusan shigewa d'akin yaji tana fad'an "malam kullum ace mutum yana cikin gida saikace wata macce, ai wlh nimiji kamar maza yakeyi, kafita mana kafafata da mutanen nan, amma kawai saikazo kazauna gida, wlh Allah dai yawadan ragon namiji" tana kai karshen maganar tawuce d'akinta,
Hawaye suka sauko acikin edon malam habu, yarasa wane irin rashin tausayine hauwa take dashi, ita kullum bata fahim babu,
jinjina kansa kawai yayi yashige d'akinsa tare da share hawayensa,
*BAYAN KWANA D'AYA,*
Tunda safe malam habu yatashi yafita masallaci domin a lokacin ne kawai yake samun damar fita batare dawani yaganshiba,
Bayan sun gama sallah, yadawo gida, dakinsa yashigo yana lazumi, a nan yatarar da hauwa tsaye a tsakiyar d'akin tayi tsaye tana kallonsa a wulaknce,
Saida yakai karshen lazuminsa sannan yadube yace " hauwa lafiya kuwa ? "
Hauwa ta ce " ina kuwa lafiya yau sau nake naje gidan biki, kawatace ta haihu kuma akwai biki tsakanina da ita dan haka yazama dole naje mata dawani abu"
Malam habu yasauke nunfashi yace "yanzu ya kikeson ayi kenan "
Hauwa tayi tako daya zuwa biyu sannan tace "kud'i nakeso a wurinka, kamar dubu ukku zuwa sama haka, zankai mata"
Dasauri malam habu yace "kud'i kuma hauwa kifasan irin halin danake ciki, wanda abinci gidansama gagararsa yake taya za'a yi a yasamu kud'in bayarwa akai gidan biki, dan Allah kidaina wannan Zancen"
Hauwa ta d'aga murya tafara masifa "wlh bazai yuyuba haka kawai, ni bandamu da halin dakake cikiba, kawai nidai kud'i nakeso duk yadda zakayi kafita kaje kaka womin, idan ma sata zakayi ni babu ruwana"
Malam habu yace "Allah yatsareni da inyi sata, hauwa kirika furta kyankyawan lafazi a kan mijinki bawai munanaba, nidai nagaya miki banda kud'i kuma banda mafitarsu dan haka kiyi hakuri,"
Hauwa tafashe da kuka sosai "yanzu saboda Allah ace mijinka baida kud'i bazar dubu uku wai bakada, ni wlh tattara kayana zanyi nakoma gidan mu naje cen nahuta da wannan talaucin naka," tana karasa maganar tafice tabar d'akin, malam habu yana kiran sunanta amma taki ko juyosa_
Bayan fitarta malam habu yayi tsaye yana kallon kofar data fita, zuciyarsa cike da kuna, bayason yana ganin kukan hauwa, tunani barkatai yarika zo masa, ta yadda zai samu kud'in dazai faran tawa matarsa rai,
abokinsa malam idi yafad'o masa arai, yasan dacewa matukar yaje wurinsa da lalara indai ta kud'ice tozai samu kuma bazai takurashiba akan yabashi amma saidai shikuma idan zaka biyashi kudinsa saika nunka masa bashi da ruwa yakeyi,
Jikinsa a sanyaye yafita daga d'akin yakarasa d'akin hauwa koda yaje tana had'a kaya tasaka a ghana mazgo,
Malam habu yakaraso kusa da ita yasauke murya yace "kiyi hakuri hauwa, karkije ko ina dan Allah, yanxu zanje nakawo miki kud'in"
Hauwa tajuyo tashare hawayenta tace "kokaifa haka akeson namiji da sharewa matar hawaye a lokacin datake bukatar hakan, yanxu ina zakaje kasamo kud'in"
Malam habu yace "zanje gurin malam idine nasan zai bani aron kud'i"
Hauwa tayi murmushi "toh shikenan Allah yasa yabayar sai kayi saurin katafi tun safiya bata idar da wayeba, kar wad'an cen An wahalar su ganka"
Malam habu yadube Kofar d'akin, yaga gari yafara haske, sannan yajuyo ya kalli hauwa yace "daukomin hijab, da kuka zani"
Cike da mamaki hauwa tace "mekuma zakayi dasu"
Malam habu yana kokarin cire hularsa yace "zan chanza kaman nune, domin nasan dacewa kafin nakara gidansa gari yayi haske sosai mutanen nan zasu iya ganina, shine zan saka hijab da zani dan sauya kamanni"
Dariya abin yabawa hauwa amma saita gimtse, tace "toh shikenan"
Zura hannu tayi tadauko masa wani hijab da zani ta mika masa,
Haka malam habu yakarba yasaka, abin tausayi yajuyo ya kalli hauwa yace " saina dawo" yana kai karshen maganar yafita yabar d'akin,
Yana fita hauwa ta bushe dadariya, harda tafawa, saida takai zaune akan dariya, cikin dariya ta furta "Allah sarki malam d'ina, gaskiya nayi sa'ar mallakashi, bokana ya iya aiki" takara bushe dadariya hartakai kwance,
Cikin boyon sifa malam habu yakarasa gidan malam idi, yayi sallama malam idi yafito,
Dasauri yajashi suka koma ciki sannan yacire hijab yace "nine malam habu dan Allah taimako nazo kamun"
Malam idi yayi matukar mamaki dasauri yace "wane irin taimako kuma malam habu"
Malam habu yace " kud'i nakeson ka aramun naira dubi ukku, wlh banida ko sisi kuma gidana babu abinci da za'aci"
Malam idi yace "ni kasan banda matsala amma dai kasan irin bashina, ko yaushe mutum yatashi biya na to nunkamin yake, kayarda nabaka"
Malam habu yace "eh nayarda bani"
Malam idi yasa hannu cikin aljihu yaciro kud'i naira dubu ukku yamikawa Malam habu"
Malam habu yayi godiya, sannan yamayar da hijab d'insa yafita yabar gidan,
Koda yakaraso kofar gidansa gari yayi haske sosai, dasauri yashiga gidan, ya mata bai rufe kofar gidanba, saboda tsabar rikicewa haka yashiga a gigice,
Hauwa naganinsa tayi saurin zowa kusa dashi, "malam ansamu kud'in" tafad'a tana mika masa hannu,
Saidao yacire hijab da zani sannan yasamu yayi ajiyar zuciya yace "eh ansamu gasu" yad'auko yamika mata,
Takarba cike da farin ciki, tana kirgawa saida ta gama sannan tad'ago kai ta kallesa tace "kud'i sun cika, yanzu saura kud'in cefane "
Malam habu yajuyo ya kalleta cike da mamaki "haba hauwa yanzu dan Allah baki ko tausayina kijibifa yadda nasamo kud'in nan dakyar, amma shine bazaki iya cire naira d'ari a cikinsu kigirka mana koda dan tamalele bane, yanzu yakikeson nayi"
Hauwa ta ja tsaki "ohonma kaika sani, niba ruwana a ciki, wad'an nan kud'in dai bazan tab'a suba, kuma wlh ni baruwana dajin yunwarka, domin mu yau gidan biki zamu wuni abinci saimun ture, kai sai kazauna da yunwa, nikaga tafiyata "
Malam habu yasaki baki yakallonta, tana kokarin wucewa d'akinta
Kamar daga sama sukaji shigowar karti a cikin gidan,
Malam habu harzai gudu sukace dawo-dawo_
Dolensa yatsaya cak wuri d'aya yana masu magiya,
Alhajin birni ne yashigo gabansu yana kallob gidan malam habu a wulaknce, sannan yajuya ya kalli karta dake bayansa yace " ko bincikemin gidan nan kufitomin daduk wani abu mai amfani, " bamusu kartin nan suka fara Antayo kayan d'akin malam habu da hauwa a waje, saida suka yiwa gidan kacha2 sannan suka dawo gaban alhajin birni,
D'aya daga cikin kartin nan yace "alhaji bakomai a cikin gidan na amfani"
Alhajin birni yadube malam habu yace " kai wane irin talaucine ke damunka, mekake dashi duniya bakada kowane"
Malam habu yadurkusa har kasa a gaban Alhaji yana hawaye yace "dan Allah alhaji kayi hakuri wlh zan mayar maka da kud'inka"
Alhaji birni yace " ai banga alamar hakan ba, kai gashi ba manyan yara maza kake dasuba balle nace kabani d'aya yamun aikin gona kota hakanma na fanshe kud'ina, kai bakada kowane,? yara nawane dakai?"
Malam habu yace " yara biyune alhaji"
Alhajin birni yadube gidan kaf yaga yaro dayane ero, dayake mamkale ajikin Hauwa yana kuka, sannan yadube malam habu yace "toh ina d'ayan yaron yake"
Malam habu muryarsa na rawa yace "d'ayan macice kuma bata hannuna tana hannun kanwa a birni" Alhajin yawashe baki yace "yawwa anzo gurin, daman ina gaf da neman matar aure, kakawomin 'yar taka nagani kaga idan tamun zan aureta, kuma zan yafe maka kud'in danake binka, kuma zan kara nunka maka wasu kud'in kuma zan baka jari zaka fita acikin talauci"
Bakaramin dad'i malam habu yajiba, zuciyarsa cike rakon Allah yasa suwaiba tayiwa Alhaji koda zai fita wannan halin dayake ciki,
Cikin farin ciki yacewa Alhaji "tohm shikenan kabani daga nan zuwa kwana biyar zanje nazoma da ita idan yaso saika dawo kaganta"
Alhajin birni yace "tohm shkenan, a nan yakwashi makaranbansa sukabar gidan," tare da yarjejeniyar bayan kwana biyar zai dadawo yaga 'yar malam habu, SUWAIBA..
Via OHW📚📲
0 comments:
Post a Comment