New Post

Sunday, 27 November 2016

HAKA SO YAKE 43-44

💕💕  *```HAKA SO YAKE```* 💕💕
            💗💗💗💗💗
               💕 *_43 - 44_* 💕
              💗💗💗💗
           *Na*
    *_Rabee'at sk mash_*♥
           ```_And_```
       *_Mr, smiles_*😃

Yau da shirye-shiryen zuwan Abba suka tashi, kowa na gidan cikin farin ciki yake, sai k'ara gyaran gidan suke, ga kamshin girke-girke dake tashi.

Da wuri jirginsu ya sauka, Abdul ne yaje ya ɗaukoshi, subeey na falo tana faman jeren Abinci a dinning ya shigo, da murnata tarbeshi sannan ta durkusa har ƙk'asa ta gaisheshi, ya amsa da "Lafiya lau suwaiba, ya gidan?" tace "da bakanan dai Abba....., anma yanzu tunda ka dawo lafiya Alhamdulillahi"

Momie dake safkowa tace "Toh ay baki ƙk'arasa ba maganarba, da bayanan me? Kenan duk kinfi jin daɗin gidan idan Abba nanan ko?" tana dariya tace "A'ah momie ba haka nake nufi ba, kuma inajin daɗi amma gidan kamar bai cika ba idan Abba bainan ko Ya Abdul? Ta juya tana kallonshi, ko ɗaga kai baiyi ya kalleta ba.

Momie tace "kidai gyara maganarki kawai, amma ni nasan kunfiji da Abbannan naku" Abba yana dariyabYace "da ke sai yau kika sani?" sukayi daria gaba ɗayansu, sannan ta rakashi ɗakinshi ya watsa ruwa.

Sun Zauna su dukansu a falo suna cin girki suka jiyo sallamar malam Habu (mahaifin subeey), cikin farin ciki subeey ta tashi ta taroshi tana murna da ganin mahaifinta.

Bayan ya zauna sun gaggaisa, aka ajjiye mishi nashi girkin yanaci subeey na gefenshi sai daɗi takeji saboda tana son babanta sosae,
Sai bayan yagama cin abincin yayi hamdala, sannna, Momie tadubesa  tace " Da Alama Akwai magana a bakinka malam habu"

Abba Yace "Amma ay da kin barshi ya huta ko?" malam habu yace "A'ah Alhaji daman sauri nake in koma da wuri, magana kam akwaita yaya, zuwa nayi zan tafi da suwaiba can ƙauye nayi mata miji, ya faɗa babu ko ɗar a ranshi.

Abba, Momie, Abdul duk suka ɗago suna kallonshi, banda suwaiba data kasa ko motsi saboda tsabar razana ƙk'irjinta na bugawa da sauri, Momie tace "Wacce irin magana ce kakeyi wannan? Subeeyn zan baka kayi mata auren ƙk'auye? Haba wannan abin aiko a mafarki bazai yuyuba"

Malam yanisa yana kallon momie Yace "A'ah yaya shima a birni yake mijin nata, ba'a kauyeba"

Momie duk ranta yasoma baci dasauri tace "koma a ina yake ban amince ba, nice nan zan aurar da subeey, domin ninafi kowa sanin mijin daya dace da ita"

malam habu Yace "Amma yaya ai bamuyi haka dake ba, tun farkoba saida na hak'ura na baki subeey tayi karatu a hannunki, munyi dake zaki zaɓa mata mijine?"

Momie  tace "bamuyi ba, amma babu wanda zai tauye ma suwaiba hak'inta, yarinya tatashi a birni sannan za'ace amaidata kauye haba!!"

Via OHW📚📲

Related Posts:

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts