💕💕 *```HAKA SO YAKE```* 💕💕
💗💗💗💗💗
💕 *_45 - 46_* 💕
💗💗💗💗
*Na*
*_Rabee'at sk mash_*♥
```_And_```
*_Mr, smiles_*😃
Abba yayi saurin shiga tsakaninsu yana cewa "A'ah hajia baza'ayi haka ba, shine mahaifinta ya fimu iko da ita, dan haka tun yabukaci 'yarshi kibasa abinsa"
Momie duk hankalinta yatashi jin abba yashigarwa malam habu, bakaramin abu zai iya rabata da subeey ba, da sauri tace "amma nima ina da iko da ita, domin nima 'yatace"
Malam habu yaga momie batada niyar bashi subeey, cikin zafin rai Yace " gaskiya yaya komi zai faru fa yau bazan bar gidannan ba saida ƴ'yata, dan haka subeey tashi kije kid'auki kayanki mutafi" yafad'a yana kallon subeey,
Ba musu subeey ta mike har jikinta yasoma rawa saboda tsabar kukan datake,
Momie tayi saurin mikewa tsaye ta rikota cike da bacin rai tace "ba inda zataje, ke koma kizauna" tafad'a tana mayar da Subeey zaune,
Shima malam habu ya mike ransa a bace yace "dakinsan halin danake ciki da bazaki hanani zuwa da subeey ba kumani danasan hakan abin zai kasance daga karshe dabanzan bayar da 'yataba, dan haka nidai kawai kibani suwaiba" nan dai rigima sosae suke akan subeey, tana gefe sai kuka take cikin tashin hankali, Abdul ma damuwah ce bayyane a fuskarshi, kasa jurewa yayi dasauri yatashi yawuce d'akinsa,
Daƙk'yar Abba yasamu y lallaɓa momie ta amince ta bar subeey ta koma ƙk'auye ba don taso ba, itama ƙk'arfin hali ne kawai ya hanata kuka don ta shak'u da subeey sosae tanajinta kamar ƴ'yar data haifa, malam habu Yace taje ta haɗo kayanta.
Babu musu ta musu ta nufi ɗakinta,
Bayan abdul yashiga d'akinsa hawayen nadama ne da kuma tausayin subeey suka fara zubo mishi, yaf'ada kan gado yana kuka, zuciyarsa tana masa kuna sosai,
Subeey kuwa Cusa kayan kawai tayi cikin jikka da duk abinda zata buk'ata, sannan ta fito tana kuka suka sallama da momie da Abba. Anan kam momie kasa jurewa tayi, kuka ya kubuce mata da gudu tajuya tabar falon, abba yabita baya yana kiran sunanta,
Subeey kuka take sosai malam habu yaja hannunta suka wuce tasha, anan suka shiga mota, suka nufi kauye, tun a cikin motar tadaina kuka, saboda taga mutane sai kallonta suke,
*KAUYE*
Har lokacin da suka isa gidan malam habu subeey hawaye take, hauwa na hangosu ta taso da rawar jiki ta tarbe subeey ta amshi jikkar Subeey, sannan ta kamo hannunta suka shiga ɗaki tana k'ara gyara mata wurin da zata zauna_ sannu dazuwa mutanen birni" hauwa take fad'a cike fara'a
Subeey dai sai kallon ikon Allah take, wai yau itace hauwa keji da ita tana rawar jiki a kanta, zama tayi ta dinga mata labari tana so ta saki jiki da ita
Hardasu abinci mai rai da lafiya ta girka mata, share hawayenta kawai takeyi tana bawa zuciyarta hakuri, azuci tace " tohh miye amfanin damuwar? Komai Allah ya ƙk'addara faruwarsa bazata iya canja ƙk'addararta ba, kuma bataso tana ganin iyayenta na mata rawar jiki tana matsayin ƴ'yarsu, hakan yasa tasaki jikinta komai takeso shi akeyi agidan, tasamu gata sosai, dadare akace kwanciya, suka barwa subeey gado sukuwa suka kwanta a kasa, hakadai ta kwanta bawani bacci kirki tayiba har gari yawaye,
Via OHW📚
0 comments:
Post a Comment