New Post

Saturday, 5 November 2016

A YINI ƊAYA 13-14

[8:20pm, 27/09/2016] Amrah💓Pinky💓durling😘: 💀 *A YINI 'DAYA* 💀

   👹💀            💀👹
                 👺

           *®NWA*
     *Na Princess Amrah*
     *Da Rabiatu sk msh*

          Page1⃣3⃣

Wata irin k'ara ta saki da k'arfin gaske tare da yin wulli da Feenat can nesa da ita,
     Wannan blue hawayen ne yaci gaba da kwaranya daga idonta, tsantsar damuwa ce k'arara a yamutsatssiyar fuskar ta,
    A razane ta koma inda ta jefar da Feenat ta sake d'aukar ta ta matse ta tam a hannun ta, tsananin girmanta yasa kamar bata rik'e komai a hannun ta ba,
      Sosai Feenat ke kuka, a wannan karen ma sai ta kasa yin ko addu'ar ma, a nan ne ta samu damar dunk'ule ta wuri d'aya ta nad'e ta kamar gammon kifi, ta d'aga ta zata jefa a cikin ruwa saboda yanda ta b'ata mata rai, duk cikin su babu wanda yayi k'ok'arin hana ta abunda take yi sai Feenat, hakan yasa kawai ta yanke hukuncin ta jefar da ita a cikin ruwa yanda tasan babu ita babu fita saboda girman ruwan bama za'a gane akwai mutun a ciki ba,
    Daidai ta d'aga ta zata jefar kenan Feenat ta sake bud'e baki tace
    *"LA HAULA WALA K'UWWATA ILLAA BILLAH, U'I'DHU KUMAA BI KALIMATULLAHI TAAMMAAT WA MIN KULLI SHAID'AANIN WA HAAMMAAT WA MIN KULLI AININ LAAMMAAT, ASTAGHFIRULLAHI WA ATUBU ILAIK, YA ALLAH NASANI NI MAI LAIFI CE, INA NEMAN GAFARAR KA YA ALLAH, ALLAH KAI KAD'AI KAKE DA IKON TSERATAR DANI DAGA WANNAN AL'AMARIN, ALLAH NA ROK'E KA DA SUNAYEN KA TSARKAKAKKU, KA CECE NI DAGA K'ANGIN DA NAKE CIKI",*
    Tana kaiwa nan tayi shiru sai wasu zafafan hawaye dake fita daga idon ta, kawai ta barma Allah al'amarinta ne dan tasan shine kawai zai iya fitar da ita, bata da k'arfi ko wata dabara sai Allah.

      Da mamaki sai ga wannan halittar ta ajiye Feenat k'asa a hankali tana sauke ajiyar xuciya,
     Sumbatar ta tayi a goshi wanda yayi daidai da saukar hawayen ta akan fuskar Feenat,
    Da sauri Feenat ta d'ago kanta ta kalle ta tace "yake wannan halitta, nasani mu masu laifi ne ga Allah kuma laifin da muka aikata ne yake bibiyar mu, ina so ki bud'e bakin ki ki fad'a min abunda muka miki saboda mu rok'i gafarar ki" jiki na rawa tayi maganar bayan ta sunkuyar da kanta k'asa saboda halittar fuskar tama kanta abun tsoro ce, just imagine halittu da yawa su dunk'ule su zama guda d'aya, ya girmanta zai kasance?

        Kanta ta gyad'a alamar baxata fad'i komai ba, Feenat tace "dan Allah idan kina jina kuma zaki iya magana tou ki fad'a min, wannan ishara ce ga wasu mutanen masu hali irin namu, zan so naji komenene saboda gaba".

     Wata irin k'ara ta saki da k'arfi wadda ta k'ara gigita Feenat, hatta da ruwan dam d'in sai da ya canja launi, itatuwan gurin kuwa ganyen su suka ringa cirewa da kansu suna fad'uwa k'asa, jijjiga kanta ta hau yi baki na rawa tana k'ok'arin yin magana amma ta kasa,
    Da k'yar ta iya bud'e baki zatayi magana kenan sai ga wani irin ruwa yana fita daga bakin ta, wannan ruwan da yake fita shi ya hana ta fad'in komai amma da alama tana son yin maganar babu hali ne,
     Hanya ta nuna ma feenat da hannun ta da alama tana nufin ta tafi ne, amma Feenat tak'i tafiya sai kad'a mata kai take tana hawaye,
"Bazan iya tafiya in bar 'yan uwana anan ba, bazan tafi ba har sai kin fad'a min abunda muka miki",

       Itama kan taci gaba da kad'a mata tana yunk'urin magana ta kasa,
    Dogon tunani Feenat ta tafi a wani lokaci tun kafin ta shiga group d'in *AREWA STARS,*
    Wata rana suna zaune da Ummah tana mata karatu, bayan sun gama ne take bata k'issoshi ciki har da na aljanu a ciki, anan ne ummah ta shaida mata da cewa duk ranar da taji zahirin muryar aljani tou sai ta kurumce, haka kuma duk ranar da kikaga aljani da idon ki sai kin makance ko kuma ki haukace",
     Saurin zabura tayi tare da fad'in "bama sai kinyi magana ba amma ki sani nayi nadama, nayi nadamar sanin *AREWA STARS* ina mai baki hak'uri idan akwai abunda muka miki wanda ba daidai ba, zan tafi gida zan shaidama iyayen mu dan suzo su tafi da gawarwakin wanda suka mutu, wanda sukaji rauni kuma a kaisu asibiti" tana kaiwa nan ta kama hanyar tafiya k'afarta babu takalmi kanta ko d'ankwali babu.

      Tayi tafiya mai nisa kafin ta isa bakin titi, mutane ne sosai wurin tamkar da rana ne saboda wani mai sai da shayi daya tada gen, daga gefen shi kuma wani mai tsire ne shima da tashi tawagar, ganin haka yasa feenat tayi hamdala tare da k'arisowa inda suke.

     Suna ganin ta kuwa suka hau daddarewa, su a tunanin su mahaukaciya ce, sallamah tama sauran da basu gudu ba amma suka k'i amsa mata,
   "Dan Allah ku taimake ni wallahi ni ba mahaukaciya bace ina buk'atar taimakon ku ne",
    Da sauri wani yace "dama kin tab'a jin inda mahaukaci yacewa kansa mahaukaci ne?  Ki gafara ki bamu wuri dallah can kn kore mana mutane daga majalisa",
     Kuka ta b'arke dashi sosai tare da tafiya a ranta tana tunani "banga laifin ku ba saboda nayi kama da mahaukatan, duk abunda muka shuka shine muke girbewa, ya Allah mun azabtu hakanan, Allah ka sassauta min".

       Wata mota ta gani irin babbar nan (j5) an sako dabbobi a ciki, hannu tasa ta tsaida ita ta tsaya, driver'n ne ya lek'o ta window saboda ta gefen shi take yace "malama lafiya?",
"Lafiya k'alau malan, dan Allah idan cikin katsina kayi ina neman taimako ne ka taimaka ka tafi dani ka sauke ni ko bakin roundabout d'in farko ne"
   Mamaki k'arara a fuskar shi yace "ke amma kin raina min hankali, a cikin tsohon daren nan zakice na taimake ki, wata k'ila ma ke aljana ce, ke ban yarda dake bama inga k'afarki" ya fad'a yana nuna k'afar da yatsa.
    "Wallahi malan kaga k'afa ta ni mutun ce" ta fad'a tare da nuna mashi k'afar tana kuka.
   "Katsina zanje, amma kinga motar duk dabbobi ne daga kasuwar Mai_adua nake nayi dare, sai idan kin yarda zaki shiga cikin su to",
  Da sauri tace "wallahi na amince",
Bud'e mata yayi ta shige cikin su tsamo tsamo, sauk'in ta d'aya ma dare ne akwai duhu duk sunyi bacci. A cikin kashi da fitsarin su ta kwanta tana sauke ajiyar xuciya.

Amrah and Rerbeeart sk novels,
Admns
ONLINE HAUSA READERS📚
[8:29pm, 27/09/2016] Amrah💓Pinky💓durling😘: 💀 *A YINI 'DAYA* 💀

   👹💀            💀👹
                 👺

           *®NWA*
     *Na Princess Amrah*
     *Da Rabiatu sk msh*

            Page1⃣4⃣

Nan da nan kuwa suka isa katsina, cike da tausayi yace mata "baiwar Allah!"
   Amma ina, tayi nisa da baccin ta,
   Sake kiranta yayi "ki tashi mun iso katsina ki fad'a min wace unguwa zan kaiki?" Nan ma shiru.
    Parking yayi da motar ya fito ya zagayo ta bayan inda take kwance cikin dabbobin ya bubbuga ta a hankali ta bud'e idon ta da suka kumbure sosai,
    "Nace mun iso katsina ina zan kaiki?",
   Tunani ta farayi inda zata je, nan ta yanke shawarar kawai ta fara zuwa gida wurin Ummanta,
   Har ta bud'e baki zata fad'i haka kuma ta tuna da Ummah zata iya yi mata komai idan taje, ta fara zuwa ko gidan su Afnan ne yanda koda sunje gida daga baya  baxata mata komai ba a gaban iyayen AFnan,
    "Goruba road zanje wurin kalamu waheed shopping mall",
    Fita yayi ya koma gaban motar yaja ta sai goruba road.

*K'arfe 12:30am.*

     A daidai k'ofar gidan su Afnan aka dire Feenat, a hargitse tama mai motar godiya tare da shigewa gidan duk ta daburce,
    Kai tsaye cikin gidan ta dosa, securites d'in suka nemi hana ta shiga d'aya daga cikin su ne yace "k'awar Afnan ce fa, kuma kun san ana case na b'atar su Afnan, ku barta ta shiga wata k'ila tana da masaniya ma".
    "Shiga" ogan nasu yace mata, da sauri kuwa ta shiga jiki sai rawa yake mata, tashin hankali k'arara a fuskar ta.

     Sallamah tayi murya na rawa ta shiga cikin parlor'n,
   Hankalin tane ya dad'a tashi yanda taga manyan mutane zazzaune sunyi tagumi har da masu yin kuka, daga gefe kuwa Ummah ce da momy suna ta faman kuka babu mai rarrashin wani,
     Daga can k'arshen kujerun kuma mami (maman Ruky) ce tayi tagumi ta zurfafa a tunani.

     Sai da tayi sallamah har sau uku amma babu wanda yaji ta saboda duniyar tunanin da suka lula,
    Ata hud'un ce duka suka amsa mata a tare,
    Kasantuwar duka mazan basu san ta ba yasa suka bita da kallo dan yanda take a rikice kamar mahaukaciya.

      Da sauri Ummah ta d'ago kanta daga kukan da take, cikin hanzari ta isa inda Feenat take ta rungume ta da k'arfi tana sauke ajiyar zuciya,
     Wani sabon kukan taci gaba dayi tana mai tausayin ummanta, lokaci d'aya tabi ta xube kamar ba ita ba.

      Momy ma tasowa tayi da k'yar ta iya fad'in "Safeenah! Ina kika baro min Afnan? ina fatan kuna tare da ita",
    Sakin ummah tayi ta koma ta rungume Momy tana ta faman ajiyar xuciya ta kasa fad'in komai,
    Dady jin haka yasa ya tabbatar da itace k'awar Afnan, mik'ewa yayi ya isa inda take tare da fad'in "Safeenah kiyi hak'uri ki daina kukan nan ki mana bayanin inda yaran nan suke"
   Nan ma shiru tayi dan bata san ta inda zata fara ba,
   Alhaji Abdallah yace "ki taimaka mana kiyi shiru kiyi bayanin inda suke, idan basa raye ne ko gawar su muna da buk'atar gani dan mu sallace su"
    Da sauri Alhaji Ma'aruf yace "haba Alhaji Abdallah! Ya zaka ringa fad'in haka? Insha Allahu yaran mu basu rasu ba, suna lafiya aduk inda suke".

     Ummah ta share hawayen ta tace "Safeenah ki kwantar da hankalin ki ki mana bayani kinji?",

     Mami ce ta taso daga kan kujerar da take tace "duk wannan bashi zaisa tayi bayani ba, idan kun kula ai a rikice take, ya kamata a bata lokaci ta samu tayi wanka taci abinci ko zata samu natsuwa",
     Momy tace "hakane kam, muje kiyi wanka idan ana binki bashin salloli ma sai kiyi".

      D'akin Afnan momy ta kaita, da k'yar ta iya yin wanka tayi alwala, koda ta fito har momy ta fiddo mata wata doguwar riga ta Afnan, cif ta mata a jiki kuwa sannan ta kama yin sallar isha dan itace kawai a kanta,
    Da gamawar ta tayi shafa'i da wutri, ta rok'i Allah gafara sosai sannan ta fita parlor da hijabin a jikin ta.

     Ta samu iyayen sun kasa zaune sun kasa tsaye, kowa yana tunanin inda yaron shi yake,
    Da fitowar ta duk suka mik'e idon kowa a kanta, kowa cike da son jin inda yaron shi yake.

       Zama tayi akan carpet d'in dake tsakiyar parlor'n, wani sabon kuka taji amma a haka ta daure ta fara fad'in
  "Da farko ina mai neman gafarar ku a bisa k'arya da muka maku baki d'ayan mu, birthday'n k'awar mu Kerry ne yau sai sa muka shirya maku k'arairayi domin mu samu kubar mu mu fita,
    Sai gashi Allah ya gwada mana iyakar shi, ya nuna mana mummunan aikin da muka aikata tun a duniya duk da yake wannan bashi ne na farko ba".

    Cike da k'osawa Alhaji Abdallah yace "go to the staright point, ina yaran suke yanzu!?"
    Cikn rawar murya tace "suna *Ajiwa dam,* but am sorry to say, duk basa cikin hayyacin su, tayi kaca kaca dasu dan bana sa ran akwai rayayyu a cikin su" tana kaiwa nan tayi shiru sanadiyyar salatin da suka d'auka duka d'akin.

      Alhaji Ma'aruf ne yayi k'arfin halin cewa "wacece ita!? Wacece ta mana kaca kaca da yara? Wallahi sai nayi ajalinta matuk'ar ta kashe min yara, yara na 'yan biyu su kenan na mallaka fa, wallahi sai ta raina kanta, zata san ta tab'a iyalin Alhaji Ma'aruf Sale, ku tashi mu tafi wurin ta ni zan maku maganin koma wacece ita, ko ubanwa ya haife ta a fad'in k'asar nan sai ta raina kanta" yana kaiwa nan ya fice sauran ma suka mara masa baya,
   Ganin za'a tafi abar su yasa Ummah da Feenat ma suka bi bayan su.

Amrah and Rerbeeart sk novels,
Admins
ONLINE HAUSA READERS📚

Related Posts:

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts