💕💕 *```HAKA SO YAKE```* 💕💕
💗💗💗💗💗
💕 *_7 - 8_* 💕
💗💗💗💗
*Na*
*_Rabee'at sk mash_*♥
```_And_```
*_Mr, smiles_*😃
'Dakinta ta shige ta rufo, har 'kofar d'akin yazo yana knockn anma taqi bud'ewa, yasan tanajinshi kuma fushi ba halinta bane duk yanda aka 'bata mata rai bata nunawa, hakan ya sanyashi magana cikin taushi da rarrashi, yace "kinga fa qanwatah, ni da wasa nake miki, ban fad'i wani abu dazai saka kiyi fushi ba, plz ki share hawayenki ki fito mu 'karasa".
Banza ta mishi kamar bata jinshi sai shesshekar kukanta da yake jiyowa kawai, haka ya haqura da lallashin ya koma kitchen, dagewa yayi ya 'kwala ihu yanda zataji yana cewa, wayyo hannunah....!!!!!!!
Da gudu ta fito har tana tuntu'be ta isa kitchen d'in, yana ganinta ya fara dariya harda ri'ke ciki, Yace "nidai nasan qanwata bazataso ta ganni cikin wani yanayi ba," kallonshi kawai take ta rasa samo maganar da zata furta mishi, ji take kamar ta bud'e baki ta fad'a mishi abinda ke zuciyarta.
Yana dariya ya d'an bangaji kafad'arta yace "yadai? Nasan yanzu kin huce ko? Kai kawai ta d'aga mishi tare dayin murmushin 'karfin hali, ta juya taci gaba da aikace aikacenta.
*** ***
Suwaiba da Abdul Abokan wasa juna ne, da mahaifiyar Abdul da mahaifin suwaiba uwah d'aya suke uba 'daya, 'yan asalin wani 'kyauyene dake jahar yola, akwai zumunci da son juna sosae a tsakaninsu, momie ce taje har 'kyauyensu ta nemi alfarmar mahaifin subeey d'aya bata ita tayi karatu a birni, da yaso ya hanata yace shi aure zaiyi mata babu maganar karatu, da'kyar ta lalla'bashi ya bata ita anma da sharad'in duk sanda ta samu miji zaiyi mata aure, momie ta amince da hakan!
Tun daga sanda subeey ta fara mallakar hankalinta ta tsinci kanta da zazzafar 'kaunar yayanta Abdul, sai dai matsalarta shine zurfin ciki bazai barta ta bayyana mishi ba, da kuma matsalar data tabbatar da ita zata hanashi soyayya da ita watau matsalar idonta.
Via OHW📚📲
0 comments:
Post a Comment