[4:45pm, 2/10/2016] Amrah💓Pinky💓durling😘:
💀 *A YINI 'DAYA* 💀
👹💀 💀👹
👺
*Na Princess Amrah*
*Da Rabiatu sk msh*
Page1⃣6⃣
Da sauri Ummah ta k'ara matsawa inda take tace "dan Allah kar kiyi magana",
Duka hankulan su suka dawo kan Ummah suna mamakin dalilin da yasa ta hana halittar yin magana,
A tsorace Feenat tace "nasan dalilin hana ta magana Ummah, amma kuma ya zama dole tayi magana domin sanin musabbabin abubuwan data mana".
Duk kanin su kallon Ummah da Feenat suke, babu wanda ya iya yin magana saboda yanda suke cike da tsoro, tun da suke a rayuwa basu tab'a ganin halitta mai girman ta ba, ko a frictions films basu tab'a gani ba, amma sai gasu yau a gaban ta bayan ta illata masu yara.
Ummah ta juyo gare su tace "tabbas idan muka bari ta mana magana duk kan mu muna cikin hatsari, duk da bani da tabbas amma wannan aljana ce, ta b'oye halittar ta ne saboda matuk'ar muka ga zahirin ta tou no more us, da zarar muka bari tayi magana har mukaji muryar ta komai zai iya samun mu, saboda jin zahirin muryar ta zai iya saka mu kurumce ko ma mu haukace baki d'aya, ina mai bada shawara da indai magana kuke son yi da ita tou mu rok'e ta ta shiga jikin d'aya daga cikin mu sai ta mana bayanin komai".
Kallon Ummah suke sosai saboda furucin ta, Alhaji Ma'aruf daya gama tsurewa yace "indai har sai ta shiga jiki na tou sai dai ta tafi bamu son jin bayanin kuma mun yafe mata",
Dady ma bayan ya ajiye Afnan yace "ai wallahi na yafe, mu dai dan Allah kiyi hak'uri ki tafi kawai, ki bar mu mu koma gidajen mu dare nayi sannan kuma bamu san ya lafiyar yaran mu ba", bayan ya miyar da kallon sa ga halittar.
Momy ta d'aga kai alamar maganar da Dady yayi gaskiya ne.
Alhaji Abdallah yace "bai kamata mu tafi haka kawai ba, mu dai daure ta shiga jikin wanin mu, kunga tanan ma zamu iya samu ta warkar mana da yaran mu data illata",
Mami cikin kuka tace "kayya! Babu maganar warkarwa a halin yanzu, kaga fa yanda tamin da yarinya, Ruky na ta baro gida lafiya lau amma yanzu jita fa, *Allah ya wadaren zuwa party ma baki d'ayan shi"* ta k'ara fashewa da kuka.
Ummah ta sauke ajiyar zuciya tace "ni nasan bazata iya shiga jiki na ba, amma barin gani", ta koma close to halittan babu alamar tsoro a tare da ita.
Sunkuyawa tayi har k'asa tace "idan zaki iya shiga jiki na ki shiga, ki shige ni dan ki masu bayanin komai".
Wata irin k'ara ta kuma saki bakin ta a bud'e kamar zata had'iye Ummah, hakan bai sa Ummah taji tsoro ta matsa ba, sai ma cewa da tayi "ke nake jira".
Kai tahau girgizawa har a lokacin bata rufe bakin ba, wannan blue hawayen sukaci gaba da kwaranya daga idon ta, a hankali ta soma ja da baya kanta sunkuye k'asa tana girgixa kanta.
Mik'ewa Ummah tayi tsaye tace "kun gani! Na fad'a maku bazata tab'a iya shiga jiki na ba, abunda yasa kukaga nace ta shiga d'in nasan wasun ku zasuce k'arya nake kawia dai ina tsoro ne, tou kun gani da idon ku, bazata tab'a koda shafa na ba, haka kuma ina da tabbacin baxata iya shigar Feenat ba, saisa ma kuka ga ita kad'ai ta koma gida ba tare da ta mata wani abu ba".
Kai sukaci gaba da jinjinawa alamar sun gamsu da duk kalaman Ummah,
Dady yace "tou yanzu miye mafita? Nidai a zahirin gaskiya ina tsoron ta shige ni dan kar tak'i fita, tou wai ma baiwar Allah me yasa ta kasa shiga jikin ki da 'yar ki mu kuma kike tunanin zata iya shigar mu?".
Ummah ta ce "ba wai ina da tabbacin zata iya shigar ku bane, ina dai tunanin zata iya d'in ne, akwai wasu abubuwan wanda muka rik'a nida Safeenah wanda ina da tabbacin babu wani abun cutarwa da xai iya cutar damu har sai idan Allah yayi nufin sa akan mu".
*Amrah nd Rerbee'art sk novels📚*
[4:54pm, 2/10/2016] Amrah💓Pinky💓durling😘:
💀 *A YINI 'DAYA* 💀
👹💀 💀👹
👺
*Na Princess Amrah*
*Da Rabiatu sk msh*
Page1⃣7⃣
Dady yace "menene wannan abun da kuka rik'a baiwar Allah?"
Ummah tace ba wani abune mai wahala ba, wasu kalmomi ne wanda baku kad'ai ba hatta da *Amrah and Rabiatu sk Fans* idan suka rik'e su zasu kub'uta daga duk wani aljani namiji ko mace, kai baki d'ayar al-umman musulmai ma nake maka magana. Kalmomin sune:-
*LA-ILAHA ILLA-LLAHU WAHDAHU LAA SHARIKALAHU LAHUL-MULKU WA LAHUL-HAMDU WA HUWA ALA KULLI SHAI'IN KAD'IR* so d'ari ko wace safiya, sai kuma *A'UDHU BI KALIMATULLAHI TAAMMAAT MIN SHARRI MA KHALAK* itama sau d'ari a yini, sai *AYATUL KURSIYYU, BISMILLAHILLADHI LA YA DHIRRU MA'ASMIHI SHAI'UN FIL-ARDI WALA FISSAMA'I WAHUWAS-SAMI'UL ALEEM, U'IDHI KUMA BI KALIMATULLAHI TAAMMAAT WAMIN KULLI SHAID'ANIN WA HAAMMAT WA MIN KULLU AININ-LAAMAT, FALAQ, NAS DA IKHLAS K'AFA UKU UKU* a kowace safiya, idan mutun yana da yara ma yana masu tou insha Allahu babu abunda zai same sa, hatta da sihiri ko kambun baka yana da wuya ya kama mutun matuk'ar ya rik'i wannan adhkar d'in, sune na rik'a kuma koda wace safiya sai munyi su tare da Safeenah inayi tana amsawa kafin ta fita ko ina, kuma kuma inda zaku rik'e su am sure babu abunda zai iya cutar daku".
Dady yace "tabbas wannan wani babban makami ne kuka rik'a, kuma muma insha Allahu daka yanzu mun rik'e su kenan", (ina fatan masu karatu ma zasu rik'e su saboda suna da muhimmanci a rayuwar mu, musamman ma a wannan lokacin da kana baccin ka wasu na maka nasari, Allah yasa mu dace ameen).
Ummah tace "tou yanzu ya kukace? A barta ta tafi ko kuwa akwai wanda zai bari ta shiga jikin sa? Nasan dole tana da maganganu a bakin ta, sannan zamuyi da wajewa in har ta shiga jikin mutun zata fita, idan ba haka ba kuma komai na mata ita taja, ina da babban malamin da zai iya salwantar da rayuwar ta, malam Mu'awuya *(na cikin JINNUL_ ASHIQ)* Zai iya da ita, barin ma nasan bazatayi haka ba".
Alhaji Abdallah yace "babu komai ni ta shiga jiki na, a adhkar d'in da baiwar Allah'n nan ta bamu na rik'e su sosai, kuma nasan koda ta zauna a jikina baxata dawwama ba saboda zan kasance mai yawan yin su insha Allahu".
Dad'i sukaji su duka, Ummah da Alhaji Abdallah suka k'ara matsawa kusa da wannan halittar tace "ga wanda zaki shiga nan, amma ina fatan bazaki cutar dashi ba" kai kawai ta d'aga masu tare da b'acewa b'at daga wurin.
Su duka sai da suka tsorata, har umman ma yanzu ta tsorata,
Bayan 'yan seconds Alhaji abdallah ya fasa wata irin k'ara da k'arfi kamar ba mutun yayi ta ba, nan ya hau jijjikar jikin sa hawaye na fita daga idon sa.
Sun dad'e a haka babu wanda ya iya furta komai kafin ya bud'e baki yace "yaran ku sun illata min duka iyali na (family na), tun daga mamana, babana, yarana uku da miji na, wasu sun mutu a dalilin haihaye su da suka ringayi, babana ya tsufa sosai da mamana, hakan yasa basu da wani k'arfi sosai abu kad'an yana iya yaji masu ciwo, sun mutu baki d'ayan su, sai yaro na d'aya jinjirin da na haifa yau kwana biyu shima ya mutu, miji na da sauran yara na biyu sun ji ciwo sosai. Bayan nan kuma a inda na zauna ina karb'ar gaisuwar mutane ma basu barni ba, sai da suka k'ara kashe min wasu mutanen wasu kuma suka gudu, taya kuke tunanin zan k'yale su? Ni ba muguwa bace saboda bani da ra'ayin shiga bil-adama, Feenat kuwa tafi k'arfi na, a lokacin dana d'auke ta da nufin yi mata wani abu kawai na kasa, kuma ma inda ace na mata wani abun da na cuce tane saboda babu abunda tamin, gefen su take tana dana sanin xuwa wurin da tayi, hakan yasa na bata izinin ta tafi gida, tun kafin ta tafi ta buk'aci na mata bayanin dalilin da yasa na masu haka amma na kasa saboda bana son taji murya na a zahiri, yaran ku kuma babu wanda na kashe sai dai duk sun raunana sosai, zasu farfad'o koba yanxu ba, ku kwashe su ku tafi dasu sannan ku masu gargad'in kar su sake zuwa wurin *party,* koda wani sukaji xaije tou su hane sa da xuwa, ni abun da na masu mai sauk'i ne, na tabbatar da inda wasu ne a cikin jinnu har kashe su zasu iya yi, gashi kuma duk cikin su babu mai neman kariya daga Allah".
*Amrah and Rerbee'art sk novels📚*
[5:03pm, 2/10/2016] Amrah💓Pinky💓durling😘:
💀 *A YINI 'DAYA* 💀
👹💀 💀👹
👺
*Na Princess Amrah*
*Da Rabiatu sk msh*
Page1⃣8⃣
Tayi shiru kafin taci gaba da "akwai abubuwa da dama da mu jinnu bama son su, matuk'ar bil-adama suka rik'e su tou komai muguntar aljani bazai iya ma mutun komai ba, kamar abubuwan da matar nan ta lissafa maku, bayan su kuma akwai yawan amfani da man hulba, bamu son warin shi sosai, sannan kuma akwai miski, shima idan bil-adama yana amfani dashi babu abunda jinnu zasu iya masa, yin addu'ah kafin shiga ban d'aki yana makantar mana da idanuwa, akwai su dai da dama wanda idan na tsaya lissafo su zaku iya kwana anan. Kai kuma bawan Allah" tayi nuni da inda Alhaji ma'aruf yake da yatsa tace "ka kiyaye ni! Zan maimata maka cewa ni ba muguwa bace, inda ace ni muguwa ce da ko gawar yaranka bazaka tayar anan ba, kana tak'ama da kud'i kud'in banza gareka! Sai kuje yanzu kud'in ka su warkar maka dasu ai, na haukatar da uwar birthday d'in saboda itace silar komai, sannan kuma ita da saurayin tane suka kashe min iyaye, saurayin nata ma na haukatar dashi, tunda iyayen su masu kud'i ne sai su neman masu magani, bana buk'atar ku sake nema na saboda na gama daku" tana kaiwa nan Alhaji Abdallah yayi atishawa da k'arfi had'e da yin hamma.
Koda na duba naga duk jikin su a sanyaye yake har dai Alhaji Ma'aruf da hawaye ke kwaranya daka idon sa, fatan shi dai Allah yasa yaran sa zasu mik'e da k'afafun su.
Dady da momy dai kuka ne kawai aikin su, sun tasa Afnan gaba da har yanzu bata da alamar tashi, baccin ta fad'a masu cewa bata kashe su ba da sunce Afnan bata da rai.
Bayanin komai suka ma Alhaji Abdallah, wurin 'yar sa ya koma ya d'aura ta akan cinyar sa yana fad'in "why Ihsan? Mesa kika zab'i wannan rayuwar? Mesa kika d'aukarwa kanki wata tarbiyyar da ban sanki da ita ba? Gashi yanzu kin jawa kanki, ga yanda Allah ya maku, wannan ishara ce ga duk masu hali irin naku, musamman matasan yanzu da suka miyar da *party* tamkar ruwan shan su, suma iyayen su k'arya a kowane lokaci kawai dan su tafi *party,* ga yanda tayi dasu *A YINI D'AYA* ta gama da rayuwar su" yaci gaba da kuka sosai yana jijjiga ta.
Haka Dady ma ya ringa jijjigar Afnan wai a nufin shi ko zata farka amma babu ko alama, Momy da kuka ya gama cin k'arfin ta tace "Afnan ki rasa irin k'aryar da zaki mana sai ta mutuwa? Ki danganta mahaifin k'awarki da rasuwa? Kenan dama ciwon k'arya kike min a lokacin da nace miki ki tafi islamiya? K'arya kike min da kikace zakije school d'in ku siyen kayan practical? Fita *party* kawai kuke zuwa Afnan? Haka kike so yaran ki su miki Afnan? Na gama yarda dake har abada, na gama yarda da duk abunda zaki fad'a min, ina fatan Allah ya gwada min ranar da kema 'yar ki zata miki haka, bana fatan Affan yayi koyi da mugun halink..." Bata k'arisa maganar ba sanadiyyar toshe mata baki da Ummah tayi tana fad'in "kar ki mata baki Hajiya, kefa uwa ce kuma duk bakin da kuka mata zai iya binta, dan Allah kar b'acin rai yasa ki fad'in munanan kalmai akan 'yarki da kika haifa".
Cikin kuka Momy tace "dole ne yasa ni fad'in haka, Afnan taci amana ta taci amanar mahaifin ta, ni a kowane lokaci ina tink'aho da ina bama 'yata tarbiyya mai kyau, ina alfahari da yanda nake basu tarbiyya ita da k'anin ta, ashe duk a banza, tana jefar dasu ne a cikin gida kafin ta fita, aikuwa kinma kanki, 'yar secondary School d'in da kike shekarar k'arshen ma bazaki k'arisa taba aure zan miki, mu koma gida wallahi sai kin fitar da miji, idan ma baki dashi zan kai hoton ki masallaci mai so yazo zan basa sadakar ki"
A hankali Afnan ta fara bud'e idon ta, tana d'ora shi akan Momy da sauri ta rufe tana rewinding d'in abubuwan da suka faru tun daga k'aryar da tayi kafin ta baro gida, casun da sukayi da kuma yanda wannan halittar ta ringa yi dasu, wasu zafafan hawaye suka ringa kwaranya daga idon ta, "tou me ya kawo su Momy nan? Ya akayi suka san muna nan? Me ma ya same ni naji jiki na duk babu dad'i?" Maganar xuci ce tayi amma bata san ta fito zahiri ba.
*Amrah and Rerbee'art sk novels📚*
0 comments:
Post a Comment