[10:42am, 13/10/2016] Amrah💓Pinky💓durling😘: 💀 *A YINI 'DAYA* 💀
👹💀 💀👹
👺
*Na Princess Amrah*
*Da Rabiatu sk msh*
Page 19-22
"Lokacin tonuwar asirin ku ne yayi" momy ta fad'a tare da watsa mata wani mugun kallo.
Duka wurin shiru kake ji babu mai magana in banda sautin kukan Afnan dake tashi,
Da k'yar ta iya furta "momy sharrin shaid'an ne dan Allah kiyi..." Bata gama maganar ba sanadiyyar tsawa da ta yi mata da k'arfi dolen ta tayi shiru.
Nan iyayen suka hau harhad'a su wuri d'aya suna k'ara tausaya masu musamman ma Md da cinyar shi ta fita daga gangar jikin sa baki d'aya duk jini ya gama b'ata shi.
Alhaji Ma'aruf ne yayi waya a asibiti yace a kawo masu mota, ya kwatanta masu inda suke sannan ya kashe wayar yaci gaba da kukan shi, babban tashin hankalin shi bai wuce yanda yaga jikin Reesha duk ya zagwanye ba, babu fata kwatakwata a jikin kamar ya k'one, ga kanshi babu ko alamar gashi yayi fari fat. Reeshat ma can jikin k'arfen shiga ruwan ya gano ta jikin ta duk ya fashe har a lokacin jini bai daina zuba ba, kuka kawai yake yi kamar k'aramin yaro.
Ba'a wani jima ba sai ga Ambulance taxo, take a ka fara saka su a cikin motar baki d'ayan su sannan aka tayar suka tafi, suma iyayen bin bayan su sukayi a motocin da suka xo ciki. Nan da nan sai gasu bakin Federal medical center, ciki suka shige basu zarce ko ina ba sai accident and emergency.
********
An dudduba su sosai dan manyan likitoci aka kira dan su duba su amma babu nasarah,
Duk wanda ya kamata ama d'inki anyi amma wurin baya d'inkuwa, da zarar an d'inke sai ya dare, su kansu likitocin abun ya d'aure masu kai.
Md kuwa duk iya k'ok'arin su sunyi amma abu yaci tura, sun samu sun tsayar da jinin dake fita daga jikin shi amma cinyar baxata tab'a komawa a jikin sa ba, shikenan ya zama gurgu.
Nuratu, Shamow da Sally kuwa in banda wari babu abun da sukeyi, idan aka fasa maruran jikin su sai wani ruwa mai yauk'i ya ringa fitowa, sai kuma marurun ya koma yanda yake. Sosai suka tsorata da wannan al'amarin, ga wasun su har yanxu basu farfad'o ba amma kuma suna jin alamar suna numfashi kad'an kad'an.
Samir kuwa nashi yafi na kowa illah shikenan yanxu ta raba shi da mazakuntar sa, babu shi babu aure, haka likitocin suka ringa fita dan basu da yanda zasuyi masu.
Da sauri Dady ya tari wani likita yace "Dr. Ya ake ciki? Ina fatan an samu nasarah"
Kai kawai ya kad'a masa yace "sai dai mu jira zuwa safe in sha Allahu zasu farfad'o, wasu sun farfad'o a cikin su wasu kuma shiru ne, mun samu anyi d'inki amma ya ringa daddarewa, Alhaji akwai al'ajabi a wannan abun, mesa d'inki zaina warwarewa idan anyi shi?",
Dady yace "shikrnan Dr. Mun gode sosai sai goben".
Momy kuwa ta koma gida saboda har asubah ta kusa gashi kuma Affan shi kad'ai ne a gida. Ummah da Feenat ma sun koma gida da nufin sai da safe zasu dawo.
*Gidan su Kerry*
*4:56am*
Har a lokacin iyayen Kerry sun kasa bacci, babban tashin hankalin ma yanda suke ta neman number d'inta amma yak'i shiga, daga farko tana ta ringing ne ba'a d'auka ba, daga baya kuma sai ma suka daina samun ta kwata kwata. Mom d'in ta banda kuka babu abunda take yi, shima Dad d'in k'arfin hali ne kawai baya so matar shi taga yayi kuka hankalin ta zai k'ara tashi,
Ko sanda suke America Kerry bata tab'a kwana wani wuri ba, duk inda taje komai dare bata kwana acan sai ta dawo gida, kuma idan taga alamar xatayi dare sosai ma tana kiran su ta shaida masu zatayi dare sosai dan kar hankalin su ya tashi, wannan dalilin ne yasa suka k'ara rikicewa ganin har asubah ta gabato amma babu ita.
K'arfe shida na safe iyayen suka tattaru a asibitin, wanda suka farfad'o d'in su suka bayar da adress d'in sauran ciki kuwa har da na Kerry,
Dady, Alhaji Ma'aruf da Alhaji Abdallah suka ringa bin addresses d'in suna sanar wa iyayen yaran, a rikice suka ringa tafiya asibitin suma.
Gidan su Kerry ne k'arshe saboda shine wajen gari, horn Dady yayi sai ga mai gadi ya bud'e masu gate suka shiga daga ciki, umurni suka masa da ya shiga yayo sallama da mai gidan.
Koda ya shiga ya samu Mom kwance a cinyar Dad kamar zautacciya sai sumbatu take tana kiran Kerry,
Cikin girmamawa yace "Oga kayi bak'i",
Da sauri Mom ta tashi daga jikin shi tana share hawayen ta,
"Je kace gashi nan zuwa"
Tafiya yayi inda Mom kuma ta mik'e tace "mu tafi tare, may be ko maganar Kerry ne".
Fita sukayi hannun ta rik'e dana Dad saboda wani jiri jiri da take gani kamar zata fad'i tsabar kukan da tasha.
Hannu Dad ya mimmik'a masu suka gaggaisa,
"Ince dai ko lafiya" Dad ya fad'a yana kallon Alhaji Ma'aruf.
"Ehh tou, lafiya ba lafiya ba, wata magana ce muke tafe da ita" Alhaji Ma'aruf ya fad'a.
"Duk kan mu sai dai mu taru muyi hak'uri mu mik'awa Allah al'amarin sa.." Dady bai gama maganar ba Mom tayi saurin katse sa da cewa "kar dai kace min 'yata Kareemah wani abu ya same ta" cike da firgici idon ta kan Dady.
"Duka yaran mu da suka je wurin Party'n ne suka had'u da wahalar rayuwa, sun tab'o ma kansu *JINNU* ne, so kun san su kuma basa yafiya sai sun d'auki fansa, indai aka tab'a su, yanzu dai maganar da nake maku suna asibiti su duka yaran, wasu sun farfad'o wasu kuma har yanzu shiru ne, shine muka karb'o address na wanda basu tashin ba dan mu sanar dasu saboda mun san hankalin iyayen su ba a kwance yake ba, yara tun jiya sun bar gidajen su amma shiru basu dawo ba dole hankali zai tashi".
Tuni wani kukan ya kufce ma Mom, da k'yar ta iya furta "ai dama na fad'a maka haka, ni nasan kerry ba lafiya ba, bata tab'a zuwa wani wuri ta kwana ba" taci gaba da kuka jikin ta sai rawa yake. (Inda zaku san akwai k'arancin ilimin addini har yanzu fa daga Dad har Mom d'in babu wanda ya ambaci sunan Allah).
Tasu motar suka shiga suma take suka rankaya sai FMC. Nidai Amrah biye nake dasu dan ganin yanda iyayen kerry zasuyi idan suka samu labarin 'yar su ta haukace, gasu da jahilci kuma jahilin mutun bai iya d'aukar k'addara ba. Muje zuwa dai.
*Amrah nd Rerbee'art sk novels📚*
[10:54am, 13/10/2016] Amrah💓Pinky💓durling😘: 💀 *A YINI 'DAYA* 💀
👹💀 💀👹
👺
*Na Princess Amrah*
*Da Rabiatu sk msh*
Page 23-25
D'aya bayan d'aya suka ringa farkawa duk kansu da hawaye bushe a fuskokin su ga wani irin rad'ad'in ciwo dake damun su.
A daidai isowar su Dad d'akin ne yayi daidai da farkawar Kerry,
Da k'arfi ta fasa wani irin ihu wanda sai da duka d'akin ya amsa, take kuma ta k'yalk'yale da dariya tana kallon su.
Gadon da take kai ta fara lilawa da k'arfi kamar zata karya shi, zanin dake shimfid'e jiki ma ta cire ta nannad'e shi ta jefa shi sai kan Mom d'in ta da k'arfi.
Kayan jikin ta kuwa tuni ta fara k'ok'arin cire rigar amma saboda yanda ta kama ta sosai yasa ta kasa cirewa, ganin ta kasa cirewa yasa ta fashe da kuka wanda babu ko alamar hawaye, can kuma ta k'ara fashewa da dariya mahaukaciya dai sak.
Hankalin Mom da Dad ya k'ara tashi sosai ganin abunda ke faruwa, da an ganta an san bata da hankali, gashin kanta duk tayi tuzu tuzu dashi lokaci d'aya kamannin ta suka soma sauyawa,
Da sauri Mom ta fara k'ok'arin nufar inda take amma ta bud'e baki tace "idan kikaxo min nan sai na kashe ki, ni ban sanku ba" ta b'ata fuska kamar da gaske bata san sun ba.
Duka hankali ya koma kan su, ganin yarinya mai gata wurin iyaye ga abun da ya same ta yasa Afnan fashewa da wani irin kuka mai tsuma zukata.
Ana cikin haka ne sai ga wani likita ya shigo,
Cike da damuwa yace "ina iyayen yaran nan da suka had'e wuri d'aya?"(Mc da Dj),
Da sauri suka ce "gamu",
"Tou gaskiya munyi bakin k'ok'arin mu dan ganin mun raba su amma abun yaci tira, mafita d'aya ce nake tunanin in har akayi tou za'a samu solution d'in abun",
Da sauri sukace "mecece mafitar likita?"
"Ina ganin dole sai dai a raya d'aya d'aya kuma ya mutu saboda yanda aka matse su da k'arfi yasa komai nasu ya had'e, har xuciyar su ma ta had'e ta zama amfani d'aya take yi, idan ba haka ba kuma sai dai suci gaba da rayuwa a haka har lokacin da wani zai mutu cikin su sannan a raba",
Malan Liman (mahaifin Dj) yace "inna lillahi wa inna ilaihi rajiun! Yaron yau kenan! Ka haife shi baka haifi halin sa ba, kullun nasiha ta d'aya da yaron nan akan yaji tsoron Allah saboda a kowane lokaci mutuwa zata iya riskar mutun, ashe abun da yake aikatawa kenan, ishara ce Allah ya nuna masu tun a duniya, kuma ma Allah yana son su da rahama tun da har haka ta kasnace, da baya son su da rahama da haka zai barsu suci gaba da aikata alfasha har sanda mutuwar su zata zo, kuma ishara ce ga sauran al'ummah masu halin iri nasu".
Alhaji Amiru (mahaifin Mc) yace "ka daina wannan maganar malan, yanzu miye abun yi?".
Likita yace "kuje kuyi shawara a tsakanin ku, duk yanda kuka yi zaku iya samu na Office d'in shine na biyu daga gefen dama idan kun fita daga nan" yana kaiwa nan ya fice hannun shi rik'e da takardu.
Sautin kuka kawai kake ji a cikin d'akin, iyayen kerry kuwa sai kallon ta sukeyi kamar ba ita ba, a rud'e mom tace "Alhaji wannan ba 'yata bace, sun canja min 'ya wallahi, ni yarinya ta lafiya lau ta baro gida babu abun da ya same ta, saboda me za'a ce min wai itace wannan? Ban yarda ba sun dai siyar min da yarinya shine suka musanya min ita da wannan, 'yata bazata tab'a cewa zata kashe ni ba" wasu zafafan hawaye sukaci gaba da ambaliya daga fuskar ta.
Dad yace "haba Mom Kerry! Mesa zaki fad'i haka? Baki ji abun da sukace ya samu yaran bane? Bafa ita kad'ai ta samu matsala ba, yanzu kika ji wani likita yana bayani akan abun da ya samu wasu daga cikin yaran, kiyi hak'uri ki daina kuka, ko birnin sin (China) ne zan kai Kareemah indai zata samu lafiya, ki daina kukan nan bana so kina yin sa",
Cikin damuwa tace "inda gaske ne ita waccan mesa babu abunda ya same ta?" Tayi nuni da Feenat dake zaune kusa da ummanta.
"Nace ki daina maganar nan fa, kiyi shiru mana Kerry zata samu lafiya" (duk maganar da zasuyi basa ambaton sunan Allah).
Shiru d'akin yayi cike da damuwa Dady yace "tou wai ma menene asalin k'ungiyar nan tasu ne?",
Alhaji Abdallah yace "nima dai tambayar da nake wa kaina kenan, su wannan yaran har sun san wai su fitar da wata k'ungiya a tsakanin su"
Feenat tace "yanzu kuwa zan baku labarin asalin k'ungiyar *AREWA STARS* da dalilin bud'e ta da kuma shugabannin k'ungiyar".
Hankalin kowa ya koma kan Feenat dake share 'yar k'wallar data soma fito mata,
Hankali na ya tashi dana duba naga ruwan biro na ya k'are gashi kuma ina son d'auko wa fans rahoton komai, da sauri nacewa sis R. "Sis kije ki siyo min pen yanxu dan kar labari ya wuce mu",
Fuskar ta ta b'ata tace "ke sis Amrah kin san fa biro tayi tsada yanzu, gaskiya sai kin kawo kud'i na gaji da siye da kud'i na",
D'an murmushi na mata nace "ki karb'o bashi zan baki kud'in idan mun koma gida". Murmushi tayi sannan ta nufi hanyar shago domin siyo biro d'in.
Ku biyo mu idan mun siya wata zaku jimu insha Allahu.
(lol..)
*Amrah nd Rerbeeart sk novels📚*
0 comments:
Post a Comment