New Post

Sunday, 27 November 2016

HAKA SO YAKE 37-38

💕💕  *```HAKA SO YAKE```* 💕💕
            💗💗💗💗💗
               💕 *_37 - 38_* 💕
              💗💗💗💗
           *Na*
    *_Rabee'at sk mash_*♥
           ```_And_```
       *_Mr, smiles_*😃

Nan suka watse kowa yakoma d'akinsa,
A ranar Subeey tayi kuka sosai, yanzu shikenan ta rasa Abdul mafarkinta bazai tab'a zama gaskiyaba, yanzu watace zata mallaki abdul ba itaba, hakadai tayita zancen zuci tana kuka,

Shikumlwa Abdul bayan yabar falon d'akinsa ya shiga yana hawaye shima yayi nadama sosai  akan abinda ya aikatawa Subeey a baya, yanzu gashi yarasata har abada kuma a yanzun ne  wani sabon sonta yake ratsa zuciyarsa daman *HAKA SO YAKE*, amma yazama dole yafita harkarta, kodan yabarta tasamu farin ciki da wanda takeso," duk azuci yake wannan zance, yajima zaune akan gado, sannan yatashi ya nufi toilet yayi wanka, bayan yafito yashirya yazo yayi breakfast sannan yafita yabar gida,

Subeey ma haka wanka tayi bayan tafito daga wanka, tashirya tsaf sannan tayi kokarin kawar dadamuwa dake kan fuskarta, tafito falo a lokacin tasamu ta karya bayan tagama suka zauna suna kallon ita da momy,
  Haka zamansu yakasance ita da Abdul...

*KAUYEN MAYYAMA*

Malam habu yana zaune akan tudun kofar d'akinsa ya zabga uban tagumi yana kallon tsakar gidan sa,
   Matarsa Hauwa tafito daga d'akinta tana kokarin gyaran d'aurin zaninta a lokacin ta hangesa zaune yayi tagumi, tsuke fuska tayi tana harararsa bayan ta kammala daurin zanin takaraso wurinsa, fuskarta d'auke da kalar rashin mutumci, cikin tsawa tace  "kai habu!!!" Tafad'a da karfi saida ya zabura ya d'ago kai yana kallonta,
Hauwa tarike kugu kamar mai shirin fad'a sannan tace " kana sane dacewa yau agidan babu abin zamuci, kuma shine kazo kazauna kana kallon tsakiyar gida"
Habu ya sauke murya yana kallon hauwa yace "nasani hauwa amma ai kinsan halin danake ciki, babu yadda na iya dolena nazauna gida domin zaman gidan yafimun kwanciyar hankali, koso kike nafita wad'an nan kartin su jibgeni" yakara maganar cike da kalar tausayi.
Hauwa ta yi fari da edo "nikam ba ruwana ehe komai zasu maka, ai kai kaja, meya kaika cin bashi, kai kenan kullum baka da aiki sai kwasar bashin mutane,  ni wallahi bazan zauna inajin yunwaba nida d'ana ba, dan haka koka je kanemomin abinci da zanci ko kuma wlh yanzu mufita yawon bara nida yarona muje musamu abinda mukaci tunda kai kazamo lusarin namiji"
Tunda tafad'i kalmar bara malam habu yashiga d'imuwa domin yasan bakaramin aikin hauwa bane zata iya zuwa, da sauri ya mike tsaye yad'aura hannusa daya akan daya yace "dan Allah hauwa karkije wannan wane irin bala'ine da wannan zanji, da zafin talaucin dake damuna kokuma da masifarki"
  Hauwa tace "wannan kuma kaika sani nidai wlh kaji zancena saika zabi d'aya kokafita kokuwa mana abinci kokuma yanzu naja erona mufita yawon maula ehe "
Malam habu ya marairaice fuska kamar zaiyi kuka yace "toh shikenan naji zan fita amma kisani idan aka kawo miki gawata saiki zauna kekidai a gidan" yana kai karshen maganar yajuya yanufi kofar fita gidan,
Hauwa tabishi da kallo tana gwatsinar fuska. Sai bayan yafita tafashe Dadariya "aikin banza aikin wofi, auren talaka ko jaraba, ni kajecen idan sun kasheka aina huta, kukan kwana uku kawai zanyi, wlh nadawo budurwata tsaf, nasamu mai kud'i na aura " takara bushewa dadariya sannan tanufi dakinta tana kiran sunan ero (yaronta )....

*WAYE MALAM HABU*

Malam habu haifanfen dan kauyen mayyamane, mano mine na gaske, yatashi cikin rufin asirin Allah yana kula da iyalinsa sosai,

Malam habu yanada mata guda biyu bintu da kuma hauwa, bintu itace uwar gida sunyi auren soyayyane shida bintu, har Allah ya azurtasu da samun haihuwa sunsamu yarinya d'aya wadda suka rad'awa suna Suwaiba,
   A gurin haihiwartane Allah yayiwa Bintu rasuwa, Malam habu yayi kuka sosai,  amma haka aka lallashesa aka bashi hakuri,
Bayan anyi sadakar bakwai ta matarsa aka mayar da jaririyar gurin kakanninta wato mahaifan malam habu,  acen Yarinya tafara girma haryakai shekara biyar, amma har lokacin malam habu baiyi aureba, iyayensa sun matsa masa sosai akan yakaro aure amma yak'i,
Kwatsam watarana babansa yace yanema masa mata Kuma aurensa nan zuwa sati d'aya dan haka yaje ya  gyara gidansa kafin amarya tazo,
Babu yadda malam habu ya iya dolensa ya je yagyara gidansa,

Bayan sati d'aya aka daura aure akan kawo masa matarsa mai suna hauwa,
Haka ya hakura zauna da ita,

Washe gari aka d'auko yarinyarsa aka kawowa hauwa, anan sukaci gaba da renon 'yarsu cikin kwanciyar hankali, sun masu farin ciki sosai a zaman gidansu,

Kwance tashi hauwa tashare shekara biyar babu haihuwa acikin gidan malam habu abin yayi matukar damunta, hankalinya yatashi, tundaga lokacin zaman gidan yafara chanzawa, tafara chanzawa suwaiba, kullum cikin gallaza mata take,  itace wanke wanke itace shara  kullum batada hutu,
Da malam habu yaga abin yayi yawa shine yayi magana,
Amma sai hauwa tace masa "tarbiyace ake koyawa yarinya, kuma da ayyukan gida"  malam habu babu yadda ya iya dolensa yabarta, haka taci gaba da gallaza mata tana gana maya azaba. Yarinya duk tabi yarame, ta kod'e,

Kwatsam wata rana 'yan uwa malam habu na birni (su momie) suka kawo ziyara gidan, Allah ya jarabci momie dason 'ya macce amma batada ita,
  Suna shigowa gidan suka tarar da hauwa tana jibgar Subeey, momei ce taje tayi saurin karbarta tana yiwa hauwa fad'a, 
Malam habu nashigowa aka sanar dashi abinda Ke faruwa zafin zuciya ya d'ibesa anan Ya aukawa hauwa saki d'aya, dolenta takwashe kayanta tabar gidan,
  Nan momie ta bukaci abata suwaiba taje da ita birni,  da farko har malam habu yace bazai yardaba, amma daga baya da aka lallashesa sai ya yarda, a ranar momie ta d'auko suwaiba suka dawo birni,

Shikuwa malam habu, yashiga damuwa sosai narashin 'yarsa kwaya d'aya kuma gashi ba mata,
Ummansa sace matsa masa akan dole saiya mayar da hauwa d'akinta, domin zaman hauwa adakinta shine rufin asirinsa, bazai iya musanyawa umman saba dolensa yasa aka mayar da hauwa,

Bayan dawowar hauwa da shekara, tabazama zuwa wurin bokaye da malaman tsibbo akan tanason tasamu haihuwa kuma tanason duk dukiyar malam habu gabaki d'aya tadawo a hannunta duk abinda takeso shizai mata,

A haka tasamu wani boka yabata magani, tazo tarika zarar kud'in malam habu, batare daya damuba, duk abinda takeso sai yayi mata shi, koda kuwa baida kud'in yinsa sai yaje yaci bashi yazo yabiya mata bukatarta, a haka har suka share shekara biyar tana azarbar dashi da bashi, ya wahala sosai, yaci bashi harna wahala, amma ita ko a jiknta,

  Wata rana kwasam tawaye gari ba lafiya, aka kaita asibiti a nan suka tabbar  mata da tanada ciki,
  Tayi matukar farin ciki akan samun cikin,

Bayan wata tara tahaifi cikin tasamu santalelen yaro, wanda aka rad'awa suna ibrahim amma suna kiransa da ero, .. Yanzu haka ero yanada shekara 6 a duniya,

bashin malam habu kuwa sai kara hauhauwa yake, yanzu hartakai ga bazai iya fita wajeba domin bashin wani alhajin birni yaci, shine alhajin yabawa yan daban garin kwangilarsa idan suka ganshi yafito, tosu kwamasosa sukawo masa, bayan sun narka mashi duka sosai,
   hakan yasa yayi kwana biyu bai fita konina kullum yana gida_ sai yau da hauwa ta'aza masa masifa yasamu yafita,

*Wannan kenan*
  
_Back to story_
*BAYAN WASU MINTUNA*
Malam habune ya famtamo da gudu cikin gidansa yana ihu da wata leda rike a hannunsa, Yana shigowa yayi saurin ya mayar da kofar gidan yarufe yasa key yadanne yana huci...

Via OHW 📚📲

Related Posts:

  • HAFSATUL KIRAM 3-4[13:29, 4/6/2016] Rerbee'art sk: 🎄🎄HAFSATUL KIRAM🎄🎄                        &nb… Read More
  • HAFSATUL KIRAM 5-6[19:14, 4/7/2016] Rerbee'art sk: 🎄🎄HAFSATUL KIRAM🎄🎄                        &nb… Read More
  • HAFSATUL KIRAM 12🎄🎄HAFSATUL KIRAM🎄🎄                           🎄   &… Read More
  • HAFSATUL KIRAM 7-8[10:05, 4/9/2016] Rerbee'art sk: 🎄🎄HAFSATUL KIRAM🎄🎄                        &nb… Read More
  • HAFSATUL KIRAM 9-11[10:50, 4/11/2016] Rerbee'art sk: 🎄🎄HAFSATUL KIRAM🎄🎄                        &n… Read More

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts