New Post

Sunday, 23 October 2016

MAKASHINKA 1-2

```MAKASHINKA...``` 
            1-2

©Rabiatu sk msh~

Wannan littafin sadaukarwa ne ga ```Sadeey S Adam``` (Kishiya), ban yarda wani ko wata ya canjamin wani abu dake cikinshi ba, ƙirkirarre ne   banyi don kwaikwayon rayuwar wani ko wata ba.√ jinjina ga ```princess Amra``` na gaisheki da yawa dear na.

***
Aminu kano international airport....

A hankali take sauke ƙafafuwanta, fuskarta cike da farin ciki take shaƙar iska.

Ba fara bace, haka kuma baza'a kirata da baƙa ba, tana da manyan idanu farare tas da ɗigon baƙi a cikinsu, da dogon hancinta sai ɗan ƙaramin bakinta mai kyau, gashin girarta gazar gazar, da wani kwantacce a gaban kanta.

Tana sanye da doguwar riga ne, orange colour mai kwalliyan duwatsu, ta yafa wayafin a kanta, taayi kyau sosae kamar baƙar balarabiya.

Fitowa tayi ta fara dogon haske ko ina babu wanda ta sani, babu Abbanta, babu Momie, babu mai kama da yayanta, bataga wani wanda ta sani ba.

Ta ɗanyi jira sannan wani yazo inda take yace "madam Sadeey s adam ko? Ta ɗaga mishi kai kawai tana kallon wani wurin, katin Abbanta ya nuna mata sannan ya nuna mata motoci ukku a jere.

Ba tare da tace komi ba ta tafi ya bita a baya, da sauri ya buɗe mata motar ta tsakiya, ta shiga baya ya zagaya da sauri, suka tada motocin suka tafi.

Wurin mai shagon siyarda waya da recherge card tace mishi ya tsaya ta sayi sabon sim, ba ɓata lokaci duk suka tsaya, ya mishi magana ya kawo mata sim cards da yawa yace ta zaɓa, ɗaya kawai ta zara ta miƙa mishi kuɗin suka wuce.

Ɗaukowa tayi tana duba numban sim ɗin, taji kamar saukar numfashi kusa da ita, da sauri ta juya tana waige waige bata ga kowa ba, sannan ta saukar da ajiyar zuciya, nan take ta fidda sim ɗin wayarta ta sakashi.

Tana kunna wayar message ya shigo mata, ta ɗauka ma kamfanin MTN ne, ga mamakinta sabuwar numbane, ta buɗa da sauri tana kallon rubutun dake ciki.

```nayi farin ciki da dawowarki nigeria, ina cike da kewarki masoyiyata sadeey```
                              ~Masoyi~

Dai dai suna shiga gidan tayi wata irin razana, ta jefar da wayar jikinta sai karma yake, tana maida numfashi cikin tsoro, daga siyan sim yanzu waye yake da numban haka?

Ya daɗe a tsaye bayan ya buɗe mata yana jiran ta fito, da ƙyar ta iya fitowa da gyalenta a hannu tana share zufa don tsoro.

Babban gida ne, daka shiga harabar gidanne mai girman gaske, Ga rumfar ajiye motoci nan itama mai girma da titin da zai kaika har inda take a cikin gidan, ko ina an ƙawata shi da flower's masu kyau da ƙamshi, ga gefen wasanni can, da wurin hutawa, sai hanyar da zata kaika garden, da kuma wacce zata sadaka da cikin gidan.

Ita sadeey tabi tana gudu gudu tana waige, tana zuwa ƙofar ta buɗe ta shiga, momie ta ajiye remote ɗin ƙofar ta taso da fara'arta tana oyoyo, itama sadeey murmushin yaƙe take ta faɗa jikinta ta rungumeta cikin farin cikin ganinta.

Ya Anwar momie ta shiga ƙwala ma kira, "ka fito ga sadeeyn taa iso, tun ɗazu yakenan fa yana jiranki kamar ya biki can ya taho dake duk yaa ƙagara yaga wannan ƙanwar tashi.

Abbah ya riga shi fitowa shima sai fara'a yake, da sauri ta ƙarasa inda yake, ya dafa kanta, yace "sannunki da dawowa ƙasarki ta haihuwa ɗiyatah," tace "Yauwah Abba, da fatan na sameku lafiya.

Anwar ne yake saukowa daga upstairs da gudu duk ya cika gidan da muryarshi, yana Oyoyo ƙanwana sadeey, duk yaa karaɗe gidan, inda Abbanshi yake da sadeey ya tsaya yanata waige, Yace "Momienah tana ina sadeeyn?

Abba ya jawoshi yana daria ya nuna mishi sadeey dake tsaye tana kallonshi, ya juya inda take yace "wow! Nida aka cemin ƙanwata zata dawo daga karatu a india sai in ganta da doguwar riga, kamar ba wayayyar ƙasa taje ba? Ya kwanto jikin Abba yace "anma dai kyakkyawace, Anyway sannunki da dawowa"

Murmushi kawai tayi ganin irin yanda yake na sangartattun yarannan da basu ƙoshi da tarbiyya ba, Abba da momie kam sai dariya suke mishi, buɗa hannu yayi ya matso inda take zai rungumeta, ji yayi kamar an matsar dashi gefe da baya, sharewa yayi ya ƙara matsowa irin hakan ce ta ƙara faruwa, yayi tsaye da mamaki.

Drivern da suka zo tare ne ya shigo, riƙe da wayarta yace "madam kin manta wayarki a mota, saƙo ya shigo ma,"

A tsorace take kallon wayar, ta tafi a hankali bata amsa ba, tana hannunshi ta buda text ɗin, ta karanta.

```ki daina tsorata dani plz sadeey```    ~masoyinki ne~

Komawa tayi da baya hannunta na kyarma harta jingina da kujerar, nan da nan yanayinta ya canja, ya ajiye mata wayar ya juya ya tafi.

Anwar ya ƙaraso inda take ya miƙa hannu zai dafata, kamar wadda aka dungura ta zauna saman kujerar ba shiri.

©Rabiatu sk msh

Related Posts:

  • ABDUL WAHAB 5ABDUL WAHAB 5 ©Rabiatu sk msh~           ®NWA Saida sukayi mai isarsu sannan daqyar fatyma ta iya cewa "wai don Allah yayanah idan daa Yaa raheem yaa qyaleka me zaka yi m… Read More
  • ABDUL WAHAB 6ABDUL WAHAB 6 ©Rabiatu sk msh~           ®NWA Tunda suka fito sadeey bakinta bai qarayin shiru ba, sai yaba kwalliyan Abdul d'inta take, hotuna kam taayi mishi ba adadi d… Read More
  • ABDUL WAHAB 7ABDUL WAHAB 7 ©Rabiatu SK msh        ®NWA Da sauri Abdul ya kashe wayarsa, duk ya tsure cikin duhu yake ma khady alamar ta taimaka mishi, tayi sauri ta danna wayarta tayi kamar ita aka … Read More
  • ABDUL WAHAB 8ABDUL WAHAB 8 ©Rabiatu SK msh           ®NWA Kauda fuskarshi yayi gefe, nan take yanayin khadija ya canja ba tare da taace mishi komi ba ta juya tabar wurin, da sauri yab… Read More
  • ABDUL WAHAB 9ABDUL WAHAB 9 ©Rabiatu sk msh           ®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION Tun daga ranar kullum Abdul neman hanyar da zai 'kara ganin khadija yake, gashi cikin rashin sa'a Ya… Read More

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts