New Post

Sunday, 16 October 2016

ABDUL WAHAB 16

ABDUL WAHAB 16

©Rabiatu sk msh
          ®NWA

Haka soyayya mai 'karfi taci gaba tsakanin Abdul da khadija, sun sha'ku sosae ta yanda bai iya d'aukan lokaci mai tsawo ba tare da yaa kirata ba, har mamakin kulawar da yake mata take.

Sadeey kam yanzu ta lura zaman gidan ya fara yima Abdul wahala, duk taa damu bata wani samun lokacin da zata mishi fira, idanma yana gidan ko yaushe da waya a kunnenshi ko a hannunshi suna musayar kalamai da khadija duk da taa kasa fahimtar halin da yake ciki.

Barci ne ya gagareta da dare saboda tunanin daya mata yawa, kwanannan duk taa canja taa ko surutun ma taa rage saboda tunanin da take, fatima ce gefenta tana ta sharar barci hankalinta kwance, lokacin ya rage bikinta saura 2month, kaasa daurewa tayi sai da ta d'an bubbugi fatima ta farka cikin nutsuwa ta bud'e ido tace "yadai matar yayanmu? Tace "ba dai dai ba fatima, ke kanki kinsan bani da nutsuwa kwanannan, naa rasa laifin da nayima yayanmu, ko kad'an yanzu bai tsayawa muyi magana, don Allah ko kunyi magana dashi yaa fad'a miki wani abin da nayi mishi?

Girgiza kai fatima tayi tace "ba wani abu da aka mishi, Qila dai yanayin aikin nashi ne, anma ay kinga koda hajia ya daina zama ya dade, ki fidda tunanin koma a ranki ki kwanta kiyi barci, kindaisan halin yayanmu daman can ba yawan magana ne dashi ba.

Jinjina kai kawai tayi ba yare data gamsu da bayanin da fatima ta mata ba, ta 'kudurta a ranta koma miye gobe zataje ta tsareshi sai taaje, wani tunani ne yazo mata a ranta, hawaye suka zubo mata da sauri ta share.

Washe gari tunda tayi sallar Asuba bata koma barci ba, gajiya tayi da jiran lokacin tashinshi tasan weekend ne bazaije wurin aiki ba.

8pm ta shiga falon d'akinshi, har zata zauna jiran fitowarshi ta jiyoshi yana dariya cikin nishid'i da sauri ta 'karasa wurin bedroom d'inshi, abinda ta jiyo ne yayi matu'kar tada mata hankali, jikinta har kyarma yake, tabbas da mace yake musayar kalamannan, Yayanmu ya fara soyayya kenan? Wata yakeso? Tambayoyi da yawa ne ke mata yawo a 'kwalwa, duhu ne ya fara mamaye mata idanu, kanta ya mata nauyi, wani abu ya tsaya mata a 'kirji.

Bata 'kara sanin meke faruwa ba ta yanke jiki ta fad'i.

Abdul naa can yana waya da khadijanshi, sai dai ya jiyo 'karar fad'uwarta da sauri ya fito, ganin sadeey a kwance bata ko numfashi ba 'karamin rud'ewa yayi ba, fridge ya wuce ya d'auko robar faro ya 'bude ya fara kwarara mata anma ko motsi batayi.

Wayarshi ya ciro ya kira fatima, tare da hajiya suka shigo kowanne tashin hankali 'karara a fuskarshi.

Hajia ce tace ma fatyma tayi sauri ta kira family doctor su.

🔆Kuyi ha'kuri da yanayin rubutun, karatun exam ne ya sanyoni gaba, ina bu'katar Addu'arku plz👏🏻🔆

Dedicated to Mr. Smiles😃

❤❤Rabiatu sk msh❤❤

Related Posts:

  • HAFSATUL KIRAM 40-43[5/2, 10:29 AM] ✍🏻rerbee'art sk msh: 🎄🎄HAFSATUL KIRAM🎄🎄                     &nb… Read More
  • HAFSATUL KIRAM 33-35[6:17PM, 4/23/2016] Rerbee'art: 🎄🎄HAFSATUL KIRAM🎄🎄                        &nbs… Read More
  • HAFSATUL KIRAM 38-39[5/1, 10:54 AM] ✍🏻rerbee'art sk msh: 🎄🎄HAFSATUL KIRAM🎄🎄                     &nb… Read More
  • HAFSATUL KIRAM 44-45[5/4, 3:48 PM] ✍🏻rerbee'art sk msh: 🎄🎄HAFSATUL KIRAM🎄🎄                     &nbs… Read More
  • HAFSATUL KIRAM 36-37[4/28, 3:50 PM] ✍🏻rerbee'art sk msh: 🎄🎄HAFSATUL KIRAM🎄🎄                     &nb… Read More

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts