```MAKASHINKA...```
61-62
Washe gari...
Aka mik'a shamsuddeen a gaban kotu,
*A KOTU*
An cika a kotun kowa yana jiran yaji ya wannan shari'ar zata kasance,
Bayan alkali yazauna agaban jama'a nan ya bukaci lauyoyi sutashi sugabatar da kansa,
Abba yanemo wani kwararren barrister, mai suna br ishak kuma ya narka masa makudan kud'i,
Br ishak ya tashi yagabar da kansa, sannan yazaune,
Alkali yad'aga kansa yakara kallon kujerar da br ishak yake zaune "Kotu tana bukatar ganin lauyan wanda ake kara" yafad'a yana kallom jama'a,
Tsit kaji kotun tayi kamar ba mutane, shiru ya ratsa nad'an wani lokaci kafin alkali ya maida dubansa gurin shamsuddeen dake tsaye a gaban kuliya yace "shamsuddeen kotu tana bukate ganin lauyanka"
Idon shamsuddeen duk sunyi ja saboda zafin dukan dayasha agurin 'yan sanda, a a hankali yake bud'e bakin yace "bana bukatar lauya kokuma wani maikareni , Allah shine shaidana, kuma nasan zai kareni" yana gama fadar maganar saikuma yayi shiru,
Alkali yajima yana kallonsa, sannan ya girgiza kai ya kalli gabansa gurin takardu, "ok shikenan" sannan ya kara d'aga kansa ya dube br ishak yace "br ishak ko kanada tambayoyij dazaka yiwa wanda ake tuhuma"
Br ishak ya mike ya d'an rusuna sannan yace "inada ya mai girma mai shari'a"
Alkali yace "ok go ahead"
Br ishak yafito yakaraso gurin shamsundeen suna kallon juna yace "malam shamsuddeen, banason ka wahalar da kotu, kuma banason ka wahalar da kanka, ka amsa laifinka domin kowa yasamu sauki"
Shamsuddeen yakara tsuke fuska yana rawar munyar yace "ko a mafarki bazan iya amsa wannan laifinba, domin bazan iya jurar ganin sadeey acikin bakin cikiba, koda za'a yanka namana ayi gunduwa-gunduwa dani a kotun nan bazan amsa laifinan ba, domin ba nine na kashe iyayen sadeey ba, kuma wutar gabar fansa har yanzu tanaci a cikin zuciyata, wlh saina daukarwa sadeey fansa"
Br ishak ya tsorata sosai dajin kalaman shamsuddeen, ta yanda yayi irin wad'annan furucin a gaban alkai, a hankali br ishak yasauke nunfashi sannan yakara kallon shamsuddeen yace "ba ka isa karaina kotu da hankaliba, taya za'a gamaka da laifi dumu dumu a hannunka, yanzu kuma saikace bakai bane, kakashewa sadeey iyaye, yanzu kuma kayi yunkirin kashe wanda take rikon sadeey hakan yana nufin duk son sadeey ne yasa kayi hakan"
Cike da zafin rai shamsundeen yace "nafa gayama bani nakeshe suba, meyasa kakasa yarda dani "
Dasauri Br ishak yace "taya zan yarda dakai, banyan ankamaka da laifi dumu2"
Shamsundeen ya girgiza kansa yana kallon br ishak yace "nawa aka bakane, nawane kud'in dazasu saye rayukan bayun Allah wad'anda basuji basu ganiba aka kashesu, karka kuskura ka boye gaskiya dan wasu kananun kud'i da aka baka, kai kasan wanda yakashe su, idan kuwa baka saniba yanzu zan nuna maka" shamsuddeen yadakatar da maganarsa yajuya yana kallon jama' a cen ya hango Abba cikin taron jama' a zaune, hannu yad'aga ya nunashi da yatsa "wancen shine makashin iyaye sadeey, shiya bata mata rayuwa, kuma wlh insha Allah nine ajakinka" yakarasa maganar cike da hargowa,
Nanfa kallon yakoma sama, da hanzari abba yatashi, duk da irin dukan da zuciyarsa takeyi kamar zata fasa kirkinsasa tafito saboda tsoro, dasauri yake fad'an "karya kake wlh, nafi karfin kah"
Nanfa haya niya ta tashi a kotun alkali yadaki tebur "silent pxl," nan kaji kowa yayi tsit,
Sannan Alkali yadube shamsuddeen yace "kaiba alkali bane dahar zaka yanke hukucin da kanka, ka kiyaye lafazinka "
sannan alkali yakara juyawa ya kalli br ishak yace "barisster kanada wasu k'arin tambayoyi da zakayi"
br ishak ya girgiza kai yad'an rusuna "babu ya mai girma mai shari'a"
alkali yace "ok zaka iya zuwa kazauna"
Br ishak yakoma yazauna, sannan alkali yayi wasu 'yan rubuce rubuce sannna yakara dago kansa yadube jama'a yace "za'a d'aga wannan karar sai zuwa nan da kwana ukku, kotu tana bukatar agabatar mata da shedu, sannan kuma ta umurci shamsudeen daya nemo lauya wanda zai karesa, kafin mudawo zama na biyu, sannan kotu tabada damar a ci gaba da tsare shamsendeen har zuwa lokacin da za'a kare wannan shari'ar" yana karasa maganar ya daki tebur, sannan ya mike, nan kaji katun tadau sautin kuttt,
Bayan alkali yafita sannan kowa yafara fita, sadeey duk hankalin yatashi, jikinta yayi sanyi sosai, tana matukar tausayin shamsuddeen,
Tana tsaye Police sukaja shamsudden suka wuce dashi mak'argama,
Sadaukarwa ga Sadeey S Adam
©Rabiatu sk msh
0 comments:
Post a Comment