ABDUL WAHAB 33
©Rabiatu sk msh
®NWA
Har dare yayi bai dawo gidan ba, yana tunanin rigimar sadeey ya rasa ta inda zai b'ullo mata ta yarda da son da yake mata.
Hakane yaci gaba da kasancewa, don kanshi ya daina zuwa inda take iyakarshi da ita duba yanda ta kwana, in kuwa zai mata wata magana yanzu taa fasa mishi kukan ya sauwa'ke mata ta koma gidansu taa gaji da zama dashi.
Yau bai dad'e da fita ba ta jiyo sallamar fatima daga can falo, da gudu ta taho zata mata oyoyo, kuma saita tuna, taja ta tsaya ita bata 'karasa ba, ita bata koma ba.
Fatimar ce ta taho tana murmushi tace "yadai kika tsaya matar yayanmu, ko bakiji dadin gani na bane? Sadeey tace "ehh mana! Don har yau ban huce da abnda kukamin ba! Sai yau kikaga damar zuwa gidan nawa?
Fatyma har tana ri'ke baki tace "kicemin har ya zama gidanki, su matar yayanmu ana so ana kaiwa kasuwa
Harararta sadeey tayi tace "ohon miki, ni kizo mu shiga ba don halinki ba.
Suna shiga falonta sadeey ta fara sharar 'kwalla, fatyma ta kalleta da mamaki tace "mezan gani haka sadeey? Don Allah karki tadamin da hankali mana, tace "eeh ku hankalinku kwance ba, ni baku damu da halin da nake ciki ba, baku so na wlhy fatyma, babu wanda ya damu dani, kowa ya manta dani 'kila shiya sanyama aka li'ka ma yayanmu ni.
Fatyma tace "kamarya? Kima daina maganarnan wlhy kowah ya damu dake sadeey, kullum sai munyita faman kiran wayarki, yanzunma hajia ce ta tadoni tace inzo inga lafiyarki, kinanan kina cin amarcinki da masoyinki sadeey nina d'aukama kin manta damu ne.
Ajiyar zuciya tayi don yanzu taa samu damar da zata rabu da Abdul cikin ruwan sanyi ba tare da kowa yaga laifinta ba, wasu hawayen ne ta 'kara matsowa tace "masoyina fa kikace bayan kowa yasan ba sonah yake ba, kinfi kowa sanin haka fatyma, kullum gidannan banda wani kwanciyar hankali gorin safe daban na rana daban ko kulani baiyi, wazan kaima kukana fatima? Bayan babu wanda yayi shawara dani kafin ayi aurannan.
Dedicated to Mr. Smiles😃
❤❤Rabiatu sk msh❤❤
0 comments:
Post a Comment