New Post

Sunday, 16 October 2016

ABDUL WAHAB 20

ABDUL WAHAB 20

©Rabiatu sk msh
          ®NWA

Sanyashi tayi a gaba ta tsura mishi ido, don shima taaga alamun chanji tare dashi, hajia tace "Ka d'ago kanka magana zamuyi Abdul, ka fad'amun gaskia, miya had'aku da sadeey, don jikina na bani kaine silar daka sanya tabar gidannan, don dama dalilinka tazo, ka fad'amin tsakaninka da Allah me ka fad'a mata daya 'bata mata rai?

Shiru yayi yana share zufa, kanshi ya d'au zafi, yama rasa abnda zai fad'a mata, tambayar duniyarnan taa mishi anma baice komi ba, ta gyad'a kai tace "shikenan tunda bazaka fad'amin ba, anma ka sani iyakar soyayyar gaskiya sadeey taa nuna maka ita, kuma bazaka taba samun macen da zata soka kamarta ba.

Kaa fadamun kaa samu wacce kakeso ba? Naayima Alhaji (mahaifin sadeey) magana tunda ni ka'kijin maganata, koma wacece kaje ka fad'a mishi don ni na haifeka bazan maka dole ba, anma bazakayi ta zamamin a haka bakayi aure ba."

Sai da ta gama tace "ka tashi ka ficemin a d'aki, anma dai ka zama mai tunani da tausayin wanda ya damu dakai Abdul, mi'kewa yayi ya fice, wani 'bangare na zuciyarshi na cike da farin cikin khadija taa kusa zama mallakinshi, sauran 'ban garorin kuma cike suke da tausayin sadeey, da maganganun hajia dake dawo mishi yana 'kara aunasu dana sadeeyn.

'Dakinshi ya shige komi ya shige mishi duhu, wayarshi ya d'auka ya fara neman layin raheem don yana da bu'katar shawararshi a halin da yake ciki, saida ta kusan katsewa ya dauka Yace "yadai mutumina? Abdul yace "dai dai Aboki kana ina? Raheem yace "Kaajika da wata tambaya, dazunnan fa mukai waya na fada maka na sauka garin katsina mai gida ya aikenii shine kake tambaya? Dafe kanshi yayi wannan wane irin Al'amari ne? Harya fara manta abubuwa, Yace "Yi haquri Aboki, mantawar ma sai anyi, abubuwa sunmin yawa duk da banso muyi maganarnan a waya, anma yanzu yafi kamata mu yita.

Raheem yace "kamarya? Meke faruwa? Nan Abdul ya kwashe komi wanda bai sani ba ya fada mishi, hrda maganar da hajia ta 'kara nanata mishi tunda ba sabuwa bace, na ya fito da mata.

Raheem ya jinjina kai don shima al'amarin yaa girmeshi yace "tabbas abokina sadeey na sonka, kuma na tausaya mata sosae, babu abnda yafi son maso wani zafi da radadi a zuciya, Allah sarki sadeey akwai ha'kuri.

Yace "duk naaji wannan, ka fad'amun meya kamata inyi? Raheem yace "duk da da shawarata ka fara soyayya da khadija, ni bazan baka shawarar ka rabu da sadeey ba, don zakayi rashin mata ne mai sonka, kawai ka had'asu duka ka aura.

Abdul har yana sar'kewa yace "what? Anma dai wasa kake ko? Nizan aura mata biyun? Wlhy bazan iya ba, bazan iya da mata biyu ba raheem, bazan taba iya tafiyar da gidana ba, bazanmayi adalci ba.

"sadeey fa taace ta ha'kura dani, duk da yana da wuya in iya mantawa da ita, anma ta wacce fuska zan kalli khadija in fada mata sadeey zan aura? Yanzu ma zan kirata in fad'a mata sa'kon hajiarmu, za'ayi aike gidansu idanta fadi rana sannan inje in fada ma Alhajin.

Raheem ya sauke ajiyar zuciya yace "tohm shknan Allah yasa hakanne mafi Alkhairi,! Jikin kowa a sanyaye suka katse wayar.

Sai bayan isha'i ya kira khadija, ringing biyu ta d'auka, suka gaisa da alamar damuwa tattare da ita, yace mata "ganinan zuwa soulmate da maganar da nakeso muyi dake," tace "A'ah, nima da maganar da nakeso in fad'a maka, Yace "tohm shikenan ki bari inzo, sai muji wazai fara fad'a, don nidai tawa ta farin ciki ce,

Tace "A'ah basai kazo ba, ka fara fad'a sai in fad'a maka anan, Yace "nikam bazan fad'a miki a waya ba, don inaso inga kalar farin cikin da zaki.

Tace "shikenan ni bari in fad'a maka.........kuka na 'kokarin 'kwace mata.

Dedicated to Mr. Smiles

❤❤Rabiatu sk mashi❤❤

Related Posts:

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts