New Post

Sunday, 16 October 2016

ABDUL WAHAB 11

ABDUL WAHAB 11

©Rabiatu sk msh
         ®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION

Suna tafe suna hira, Fatima na nuna masa hanya, tun ahanya Abdul yasa Fatima taiwa Kadija waya gatanan zuwa gidansu,  cikin murna Khadija tahau shiri don tanaso ace anzo gidansu, momynta kanta tafahimci haka, binta kawai take da dariya.

Da isarsu gate aka bud'e masu, Abdul yayi parking mota, sai zuba ido yake yaga ta inda zata fito, waya Fatima taduba zata kuma kiranta, sai gata tafito, tafiya take d'ai-d'ai tamkar batason taka 'kasa, Abdul sakar baki yayi yana kallonta, kullum 'kara kyau take, duban  Fatima  Khadija tayi, "sai kicemin tare da yayanku kike".

Murmushi Fatima tayi "to meye aciki?" Iso tai masu zuwa ciki, har 'kosawa ta farayi da kallonda abdul ke mata

Zama sukai baki d'aya, suna hira da Fatima, Khadija sai satar kallonshi take, Abdul najinsu bai tankaba, can aka hau Jere masu kayan snacks da drinks, sund'ansha drink kad'an, Fatima tasake duban Khadija da murmushi " ke inma fad'a maki gaskiya, wannan zuwan na yayanmu ne, banawaba ni rakiya nayo" Murmushi Khadija tayi, tad'an saci duban Abdul tagefan ido, Fatima tai dariya"wallahi kunfiye gulma, anaso ana kaiwa kasuwa" tami'ke "nibari inje ingaida momy, inkun gama kikirani" tafice tana dariya.
           
Shiru falon yayi, kowa yakasa cewa komai, can dai Abdul yadaure, yana kallonta duk da ta'ki yarda su had'a ido, Yace "rannan sai kishi ya hanako tsayawa muyi magana ko? Kin barni cikin tunani da zullumi, gaskiya KHADIJA, ada dai banyi tunanin son wata 'ya maceba, banyi zaton zanfad'a soyayyaba, amma yau sai gashi nafad'a soyayyah, alokacin da nafad'a soyayyar ban gas-gataba sai yanzu_" Khadeejah!" Yanayin daya kira sunanta, saida tsigar jikinta ta tashi, d'ago kaitayi suka had'a ido, da sauri tad'auke kanta, murnushi Abdul yayi  "khadija yau gashi nafad'a sonki, khadija inasonki so d'aya tak, wlhy ban ta'ba furtama wata mace wannan kalmar ba, kenake yiwa soyayyar da bata misaltuwa, kinzamo wani 'bangare ajikina" nan yadinga zayyano mata sirrin zuciyarsa, Wanda baisan yanayi ba, ita kuwa khadija wani sanyine kawai ke lullu'beta, murmushi kawai take.

Dubanta yayi, had'e da ajiyar zuciya, "bakice komaiba, maine ra'ayinki akaina_?" Shiru tayi, amma kanta na'kasa tana aikin murmushi, harya gaji yadubi agogo duk jikinshi yayi sanyi yace "kiramun Fatima mutafi" da sauri ta dubeshi, sai kuma tamu'ke, tafita mintuna biyar sai gasu tare, mi'kewa yayi, ya dubeta "shikenan mungode, ki cema mama ina gaisheta!

Fatima talura jikin Abdul amace yake, dariya tahauyi "Allah sarki sokenan" harararta Abdul yayi, Yace "sadeey sarkin surutu, ke kuma sarkin daria ko?

Tace "ba haka bane yayanmu, Kasan wani abu? yayanmu, Khadija takar'bi numberka, tace kayi ha'kuri zata baka amsa awaya, wai ita yanzu kunyarka takeji" murmushi Abdul yayi, "haba da gaske, kicemin kawai nayi nasara! Murmushi Fatima tayi tace "naace, don Alama khady na sonka, daman naga alamr tana sonka, kun kasa yarda ne"

wani burki Abdul yatake yace "da gaske 'kanwata, kai wallahi naji dad'i, da duk jikina ya mutu" dariya take mishi sosae, itakam mamaki yake bata, gaskiya so dabanne, gaba d'aya Abdul yaa canja kamar bashi ba, yaa koyi surutu da yawan fara'a wanda duk da baidasu!

Sadeey ce ta fad'o mata a rai, Allah sarki, koya zataji a ranta?

Dedicated to Mr. Smiles😃

❤❤Rabiatu sk msh❤❤

Related Posts:

  • MATATAH CE 65♡MATATAH CE♡    ♡♡♡♡♡♡             65 ©Rabiatu sk msh       ®NWA   … Read More
  • MATATAH CE 68♡MATATAH CE♡    ♡♡♡♡♡♡              68 ©Rabiatu sk msh       ®NWA  … Read More
  • MATATAH CE 66♡MATATAH CE♡    ♡♡♡♡♡♡              66 ©Rabiatu sk msh       ®NWA  … Read More
  • MATATAH CE 65♡MATATAH CE♡    ♡♡♡♡♡♡             65 ©Rabiatu sk msh       ®NWA   … Read More
  • MATATAH CE 67♡MATATAH CE♡    ♡♡♡♡♡♡              67 ©Rabiatu sk msh       ®NWA  … Read More

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts