ABDUL WAHAB 31
©Rabiatu sk msh
®NWA
Sai da ya fita daga d'akin kuma ta fashe da kukan takaici, Abdul yaa riga yaa gama da ita tunda ya gane mahaukacin son da take mishi, kuka take sosae a ranta tana addu'ar Allah ya kawo mata mafita.
Da dare da wuri ta mishi girki kafin ya dawo, ta shige d'aki tana gama sallolinta tayi shirin kwanciya, doguwar riga ta saka iyakar gwiwa ash, mai santsi dabin jiki, taayi kyau sosae, mukulli ta saka ta rufe d'akinta ta haye gado tayi addu'a ta kwanta ynzu ta fara sabawa da gidan taa d'an fara rage jin tsoro.
Yana driving ne anma fargaba ce a zuciyarshi, sai da ya tabbatar da daman taa gama duk abnda zatayi taa kwanta sannan ya taho gidan, baison ya kalli sadeeynshi da yanayin damuwa, kukanta na ta'ba mishi zuciyah, ga fargabar maganar data tsiro da ita wai sai ya sauwaqe mata, lumshe idonshi yayi ya bud'e yana tunanin yanayin dazu.
Sanda ya isa gidan kamar yanda ya zata, tayi barci ko motsinta bai jiyo ba, d'akinshi ya shiga ya watsa ruwa yayi shirin kwanciya sannan ya fito ya zauna yaci abincin data girka mishi, hankalinshi duk naa wurinta harya gama.
A hankali ya murd'a 'kofar d'akinta, jinta yayi a rufe, komawa d'akinshi yayi ya dauko makullanshi yazo ya 'bude a hankali ya tura 'kofar ya shiga.
K'arasawa yayi inda take, kasa d'auke idonshi yayi a kanta, a fili yake furta, Alhmdlh, Ya Allah ka nunamin ranar da sadeey zata gane irin son da nake mata, tsugunawa yayi saitin fuskarta yana tunanin yanzu da suna zaman lafiya ne zai kwanta da ita ne a 'kirjinshi yanajin lallausar fatar ta, shi kadai yasan yanayin da yakeji idan yana tare da sadeey.
Yatsun hannunta masu kyau taayi musu kwalliya da jan lalle, baisan sanda yakai hannunshi ya had'a da nata ba, yana shafawa a hankali, har wani lumshe ido yake, bata farka ba sai dai motsi da takeyi da ido kamar zata bud'e.
Hannunshi yakai ya shafi fuskarta, ya d'aura hannunshi saman le'banta, runtse idonta tayi sosae ta 'kwalla ihu, da sauri yasa hannu ya rufe mata bakin.
Turashi tayi da 'karfi, ta tashi zaune, hawaye ne suka taru a idonta da sauri ta koresu don yanzu batason kuka gabanshi, muryarta a dake tace "tohh fita ya isa hakanan," sosa 'keyarshi yayi yace "Allah ya huci zuciyarki," girgiza kai tayi tace "zuciyatah bazata taba hucewa ba idan ba barin gidanka nayi ba yayanmu, ka shiga ha'kkina da yawa yayanmu, sai yaushene zaka gane ka sauwa'kemin....?
Da Sauri ya girgiza mata kai yace "dama ki daina wannan maganar, babu rabuwa a tsakaninmu, don Allah ki gane irin sonda nake miki," kuka ta fasa mishi zata 'kara magana yayi saurin barin d'akin don maganganunta na 'kona mishi zuciyah da yawa.
Dedicated to Mr. Smiles😃
❤❤Rabiatu sk msh❤❤
0 comments:
Post a Comment