```MAKASHINKA...```
29-30
©Rabiatu sk msh
A hanyarsu ta komawa gida, sadeey tayi shiru tana sauraren Shamsuddeen yana ƙara mata nasiha, ba ƙaramin burgeta yayi ba.
Tace "Anma deen daman kana karatun hausa ne?
"A'ah, littafin A YINI ƊAYA, ma labarinshi naji shiyasa na karanta, kema ki karantashi duk da naa baki labari zaki fi ƙaruwa.
Ta jinjina kai "Anma dai kaayi zurfi a karatun addini ko?
"Tun kafin na gama j.s, na hardace Alƙur'ani, kuma Alhmdlh nasan wasu littafan da hadisai"
"Tohm karatun boko fa? Daman na daɗe inason sanin unguwar da kake "bai samu bata amsa ba, sai dai uban burkin da yaja, fuskarshi cike da firgici, itama sadeey ɗaga idanunta tayi saboda faɗuwar gaba tana kallon gabanta, take nan ta zaro ido, tana riƙe ciki saboda fitsarin da taji ya kusan zubo mata.
Daɗin labari bai saka sun hango ƴan fashin da wuri ba, saida sukazo gab dasu, gashi basu ida shiga gari ba, wurin shiru ba kowa motarsu ma ce kaɗai.
Kuka ta farayi mai ƙara harda ɗaura hannu akai tace "na shiga uku na" shima shamsuddeen yana cikin damuwa yace "miye na tada hankali kuma sadeey? Duk da tashin hankalin da take ciki harara ta aika mishi tace "ay naga kai naka kwance yake, yanzu meya jawo maka kawo mu wurinnan? Ni wlhy tsoran ƴan fashi nake ko a cikin film.
Yace "duk ba lokaci bane yanzu na wannan maganar, mafita zamu nema kinga yanda suka zagayemu dai suna matsowa inda muke harda bindiga a hannunsu,"
Idon sadeey suka ƙara fitowa saboda tsoro tace "kaja motar mu koma mana"
"dubara taa ƙare mana tunda mun kawo kanmu, kedai kiyi sauri ki duƙe tunda basu hangoki ba...." tun kafin ta gama jin abinda zai faɗa ta lahe ƙarƙashin kujera.
"Zan rufe motar ko ina, in fita da gudu, kinga idan suka biyoni su duka sai kija motar ki tafi, ki tsira da rayuwarki, komai ya sameni ƙaddara na ne" kafinta ta yunƙura yaa buɗa motar yaa fice da gudu, tana faɗin "karka fita ka barni ni kaɗai shamsuddeen, don Allah ka dawo" Anma har yayi nisa.
Da sauri ta miƙe jikinta na kyarma ta fara leƙawa don bataji alamar sun bishi da gudu ba, a cikin duhun ta hangoshi yayi nisa sosae da gudu, ta dafe ƙirjinta "shikenan shamsuddeen kawoni yayi a kasheni, ƙilama wannan haɗa baki ne kawai tunda ba saninshi mukai ba" take kuma zuciyarta ta fara ƙaryata ta, ay kuma shamsuddeen mutumin kirkine, tohh meyasa ya tafi ya barta?
Tunaninta ya tsaya jin sun buɗe motar, cikin tsoro har saida guntun fitsari ya zubo mata, ga mukullin mota a hannun ta kuma taa rufe ta ciki yaya suka buɗe? Kafin ta nemo ma kanta amsa sai dai taji an jawo ta an wurgo waje.
Ƙara ta fasa, abinda ya harzuƙa wanda ya jawota kenan ya kai mata bugu a baki, nan take jini ya fara zuba ta hanci ta baki, nan fa ta ƙara rikicewa jin taa taɓo jini a bakinta, wannan bai hanata ƙara fashewa da kuka ba cikin tausayin kanta take magana.
"Don Allah ku taimakeni ku ƙyaleni in tafi, ga motarnan da duk abinda ke cikinta, don Allah karku cutar dani" ogan ne ya ƙaraso cikin tafiyar taƙama, da sauri cikin biyayya suka ajiye mishi kujera ya zauna gefen titi.
Cikin muryar riƙaƙƙun ƴan daba wani yace "Oga wanda suke tare ya gudu, kuma da alama bai fita da komi ba shiyasa bamu bishi ba, sai dai wannan yarinyar kaɗai ta rage"
Tace "Wlhy daman babu komi a tare damu, idanma motan ne ga mukullin don Allah ku barni in tafi" wani irin tsawa ogon ya daka mata, da saida ta daina jin komi na lokacin kafin ta dawo da jinta.
Yace "Wani ya faɗa miki muna karɓar mota? Idan baku da komi ai gakinan," ya kalli sauran yana zuƙar taba, ya hura mata a fuska sannan yace "ku shigarmin da ita, na samo mai tayani kwana"
Cikin ƙarfin hali tace "dawa zaka kwana? Wlhy bazanje ba, don Allah ku barni in tafi su momma na jira na" wani wawan mari ya kai mata, da sauri ta kauce hucinshi ya wuce.
Ganin bai sameta ba ya sanyashi cukuikuyota cikin after dress ɗin ta faɗa jikinshi, Yace "idan bazakije ba sai ayi komi anan mana, kinga suma har sai su ɗana"
Sadaukarwa ga Sadeey S Adam (kishiya)
©Rabiatu Sk msh
0 comments:
Post a Comment