ABDUL WAHAB 22
©Rabiatu sk msh
®NWA
Bayan sati biyu
Sadeey ce kwance saman cinyar mami tana kwance mata kitso, tana yi mata fira sai dariya take, wayarta ce tayi ringing, sunan fatyma ta gani ta maida wayar ta ajiye.
Mami tace "waye yake kira da bazaki d'auka ba? Tayi er dariya sannan tace "fatyma ce mami, bansan mezance mata ba, nasan maganar bikinta ce kuma ina jin kunyar ince mata bazanje gidan ba, Mami tace "da kunya kam, kinga ki d'auki kiran kiji me zatace.
Maganar Fatima suka jiyo tana shigowa tace "rabu da ita kawai mami, idanma bazata zo ba ayni gani naazo, ni bansan laifin da muka yima sadeey ba.
Da sauri sadeey ta tashi tana rufe ido tace "ai naa'ki d'auka ne don inyi suprising dinki kawai sai dai ki ganni gidan, fatima tace "ba waninnan inda gaskene tashi mu tafi mana, daman zuwa nayi tafiya dake.
Sadeey ta kalli mami tace "Yanzu kuma na fasa sai gobe zaki ganni tunda safe, fatima ta 'bata rai tana kallon mami tace "kinjita fa mami, don Allah sadeey ta kyauta? Idan bikinta ne akeyi tun ana sauran sati nawa kike tunanin zan dawo gidannan? Mami tace "tun yana rage wata guda ma.
Fatyma tace "yauwah mami, kinga sadeey saida ya rage wata gudan ma sannan ta baro gudanmu, Yanzu kuma naa biyota har gida biko taa'ki yarda mu tafi.
Mami murmushi kawai tayi tana saurarensu, duk yanda fatima taso su tafi da sadeey 'kin yarda tayi, don ko kad'an batasan da idon da zata kalli Abdul ba idan taje gidan, batason Abinda zai fama mata ciwon rashinshi.
A haka fatima ta ha'kura sai dai suka fara tsattsara yanda bikin zai kasance, ba tabar gidan ba sai bayan isha'i driver yazo d'aukarta.
A farfajiyar gidan ta wuce Abdul da raheem bayan ta gaida raheem, Abdul daya gama ramewa, duk yaa koma kalar tausayi yana jingine jikin motar raheem yace "soyayya matsala ce frnd, tabbas na gano illarta, daman abnda ya dad'e yana tsoratani da shigarta kenan, khadija taaci amanata, data barni na gama fad'awa ga soyayyarta sannan ta gujeni, bansan da wacce fuskar zan kalli sadeey in bata ha'kuri ba.
Cikin tausayawa raheem ke kallon Abdul, don kwanannan ba 'karamin tausaya mishi yake ba, kullum maganarshi kenan, khadija taaci amanarshi, baisan da fuskar dazai kallo sadeey ya bata ha'kuri ba.
nikam nace "daman ashe maza ma sunajin ciwo a zuciyarsu?
Abdul baida wani sukuni ko wurin aiki yaje tunani baya barinshi komi, har mutane sun fara gane mishi, ko yaushe yana 'kara tuna soyayyar da sadeey ke nuna mishi, ko kad'an bata barinshi da kad'aici, komai hidimarshi taa d'auke a gidan, sai yanzu ya gane irin sha'kuwar da sukai da ita, tabbas baka sanin muhimmancin sai randa baka tare dashi.
Dedicated to Mr. Smiles😃
❤❤Rabiatu sk msh❤❤
0 comments:
Post a Comment