ABDUL WAHAB 15
©Rabiatu sk msh
®NWA
A harabar gidan ya koma saman resting chair ya zauna, ya fiddo wayarshi yana 'kara duba text din khadija sai murmushin jin dadi yake.
Numbarta ya farayin saving, shima 'soulmate' ya saka mata, gaskiya sunan yahau, sannan ya fara 'ko'karin kiranta, a kashe ya samu wayar duk da haka bai ha'kura ba sai da ya kira yaafi iyakar 'kirgawana, tunda na 'kirga 35 na gaji da 'kirgawa!
Badon yaaso ba haka ya ha'kura ya daina kira, sai dai ya maida mata reply
"Bazan iya kwatanta miki farin cikin da nake ciki ba da amincewarki I feel like the luckiest guy In the whole world to have a beautiful, and honest girlfriend like you. I hope my luck never runs out and I can make you mine forever.
Haka ya yini da wayarshi a hannu yana jiran ta 'kara mishi text ko ta bud'e ya kirata, basuyi waya ba sai wurin 11pm cikin sa'a lokacin ta kunna wayar, itama taa kasa barci tuninin abdul kawai take, da yanayin da zaiji idan yaga reply dinta.
Sai da kiran ya kusan katsewa saboda yanda takeji duk kunyarshi ce taa gama rufeta, da'kyar ta iya d'auka ta saka a kunne, da zazza'kar muryarta ta mishi sallama, saida ya rufe ido ya lumshe sannan ya amsa mata.
Sun dade suna , duk da firar tasu duk tambayoyine yake mata, akan karatunta da kuma gidansu.
Khadija bello jega ne cikakken sunanta, tayi primary dinta da secondry duk a private school dake garin jega, anan ne suka hadu da sadeey da fatyma, sai bata ci gaba da karatun ba, ita kadaice a wurin mahaifanta kuma er gatan a wurin abbanta da mamanta.
Har zasuyi sallama tace "anma baka fad'amin ala'karku da sadeey ba, Yace "meyasa kikeso kiji? Tace "hmm shknan kawai, yace "A'ah daga tambaya? Da mahaifina da mahaifin sadeey uwa d'aya suke uba d'aya, itama ita kad'aice a wurin mahaifanta, mamanta na matu'kar ji da ita komai takeso ana yi mata.
Tun dawowatah daga karatu ta dawo gidanmu da zama, saboda sha'kuwar da sukai da fatima" tace "Uhm kawai! A haka suka gama firar.
Dedicated to Mr. Smiles😃
❤❤Rabiatu sk msh❤❤
0 comments:
Post a Comment