```MAKASHINKA...```
7-8
©Rabiatu sk msh~
A ƙofar ɗakin ta tsaya, tace "bari inyi sauri in shirya ko ya Anwar? Yace "naji anma kiyi sauri plz ƙanwata," tace "an gama yayan.
Sai da ta baje kayan daya kawo mata saman gado, tana kallon rigar tunani take ta yandama zata sakata, 'yar ƙarama ce da bazata kai mata cibi ba, sai wandon shima gani take kamar bazai shigeta ba, gashi shma iyakarshi gwiwa.
A sanyaye ta maida kayan ta ajiye, ta duba saƙon daya shigo mata a waya.
```zan iya karantar alamun rashin gamsuwa da kayannan a fuskarki, zandai ƙara faɗa miki ne bai kamata ki saka suba```
~masoyi~
A hankali ta haɗiye wani abu cike da ruɗani, hannunta na kakkarwa, ta jefar da wayar, ga mamakinta bata kai ƙasa ba, kamar an ɗorata saman cafet, ta ɗora hannu saman kai cike da tsoro.
Yanzu kam ta ida yardarma kanta ~Masoyi~ ba mutum bane, kuma ba fatalwa bane, kawai Aljani ne da yake tare da itane ako da yaushe.
Cikin ƙarfin hali ta miƙe ta nufi toilet tana tafiya tana waiwaye, bata rufe ƙofa ba ko wanke fuska cikin dabara tayi ba tare data rufe ido ba, tana ta juya idanu taga ta inda ~masoyi~ zai ɓullo.
Da sauri ta gama ta fito tana goge jikinta da towel, dubawa tayi inda ta ajiye kayan basunan, duk inda sadeey take tunanin kayan sun shiga bata gansu ba, da sauri ta nufi ƙofa tana ƙwalama Ya Anwar kira taji koshi ya ɗauka kayan, anma ƙofar ma a rufe sai dai ya jiyota ya taho da sauri.
Dagewa tayi ta dinga tura ƙofar, don ita dai batasan sanda ta rufeta ba, kuma babu alamar a rufen take, shima Ya Anwar turawa ya shiga yi anma taƙi ta buɗe ƙofar.
Anwar cikin jin haushi yace "kin kyauta kin jiko sadeey, ban taɓa fuskantar irin wannan wulaƙancin ba, kin sakani naa tara mutane ke kaɗai ake jira anma kin rufe ƙofa bazaki fito ba," muryarta cikin kuka tace "wlhy ni ban rufe ƙofa ba yayanmu, kayan daka kawomin ma nake nema ban gansu ba" yace "kayan dana baki har ƙofar ɗaki na rakoki dasu kicemin baki gansu ba? Daman na lura da bason zuwa kike ba, kinyi dai dai kinji ko," yaja dogon tsoki yayi tafiyarshi ta kifarda kanta jikin ƙofar tana kuka.
Har momie sai da tazo tayi mata magana, anma ƙofar taƙi buɗewa, itama ta gaji tayi tafiyarta.
Wayarta ta gani kusa da ita, ba tare data taɓata ba ta karanta saƙon.
```ba wurin zuwanki bane, kimin afuwa anma hakan shine dai dai```
~masoyi~
Wannan lokacin ja ta dingayi ta baya tana kallon wayar cike da tsoro, illahirin jikinta kyarma yake, tunaninta ya tsaya cak, bakinta na rawa cikin kyarmar ido ta fara bin ɗakin da kallo lungu da saƙo.
Cikin ɗaga murya sadeey tace "waye kai? Me kakeso tare dani daka takurama rayuwatah? A kullum cikin neman tsari nake daku, ko a cikin mutane babu ruwana da rayuwar kowah, don Allah ka ƙyaleni.
Saƙonshi ya shigo, wannan karon da kanta ta rarrafa, ta duba.
```soyayyarki nakeso sadeey da amincewarki, naa rantse miki da Allah ni ba Aljani ba, kuma ni ba fatalwa bane, kuma ba daga waya nake samun bayani a kanki ba, ni mutum ne da soyayyarki ta gama mishi illa, babban burina a yanzu ki amince da soyayyata```
~masoyi~
Suman zaune kawai tayi na wani lokaci, shi ba aljani ba, shiba fatalwa ba, ba daga wani wuri yake samun bayani a kanta ba, anma a haka yake kiran kanshi da mutum yanzu tayi magana yaji ta, ya kuma bata amsa alamar yana tare da ita.
Idan kuwa har da gaske mutum ne, ta tabbatar yana tare da ita koda yaushe, tohh ya akai bata ganinshi? Indai da gske mutum ne ita da kanta zatayi maganinshi, don bataga amfanin ya dinga takurama rayuwarta ba a lokacin da takeso zuciyarta ta samu nutsuwa, ta nisa kanta da duk wani ɗa namiji, da kuma tsanarsu da tayi gaba ɗaya, don ta tabbatar ma kanta da (DUK HAKA SUKE... Littafina mai zuwa) abinda shamsudden yayi mata, bata da wani hujja da zata iya yarda da soyayyar wani namiji.
Haka ta sulale nan ƙasan cafet tayi barci mai cike da tsoro da rashin daɗi, da burika kala kala.
Sai da asuba ta farka tayi sallah, ta zura doguwar riga kawai ta fito da sauri, babu kowa daman hakan ta zata, ta lallaɓa zata fita kenan ta jiyo muryar Abba Yace "wacece nan?" ta dakata sannan ta juyo, har inda yake ta duƙa ta gaisheshi, Yace "sadeey ina zakijene da safiyar nan?
Rasa ƙaryar da zata mishi tayi, sai dai ta fara raba idanu inda inda, Abba yace "ba tun yau ba naa faɗa miƙi banison fitarki ke kaɗai, bawai na canja ra'ayi bane, drivernki nanan, kuma ga yayanki duk inda kikeso zai kaiki, ki kiyaye kinji sadeey" ta ɗaga kai tace "tohm Abba," yace "tashi kije yanzu safiya ce sosae, anjima sai kije duk inda zakije," tace "tohm sannan ta koma saman kujerun babban falon ta zauna don batajin zata iya komawa ɗakinta ba tare da taje inda takeson zuwa ba
Sadaukarwa ga ```sadeey s adam``` (kishia)
©Rabiatu sk msh
0 comments:
Post a Comment