New Post

Sunday, 16 October 2016

ABDUL WAHAB 10

ABDUL WAHAB 10

©Rabiatu Sk msh
          ®NAGARTA WRITER'S ASSOCIATION

Sauke numfashi Abdul yayi sannan ya jingina da kujera, wayarshi ya ciro ya fara neman raheem, tun kafin tayi ringing ya d'auka da yake wayar na hannunshi.

Abdul yace "kai Aboki kamar kana jira," "Yace jira nake mana ay nasan zaka kirani ne ko yaushe, Kaaga Tauraron sadeey, Angon khadija kuma yaya ga fatyma," Abdul yace "kuma babban abokin raheem ba,"

"Yanzu dai ya ake ciki? Shawara nakeso ka bani," raheem yace "ina jinka Abokinah! Shiru yayi yama rasa ta inda zai fara mishi, sai da raheem yace "yadai? Kaayi shru, sannan yace "idan mutum ya yanason mace ta yaya yake bayyana mata? Kuma naasan halinka karka yimun dariya!

Raheem yace "kaima kaasan sai naayi kenan? Ka fad'i abin dariya kace bazanyi ba? Cikin dariya yace "watau yanzu kaa sauko kenan? Kaa yarda kaa fara soyayyah? Ran Abdul yayi matu'kar 'baci, saida yaja dogon tsoki sannan yace "idan kaa gama dariyar kaa nemeni mu 'karasa magana, kai naama fasa neman shawarar taka, dariya ta hana raheem cewa komi har Abdul ya kashe wayar.

*** ***
Da marece ya fito cikin wankan shadda ruwan coffee, yaa had'e matu'ka sai murmushi yake cikin nishad'i, 'kagare yake suje gidansu khadija duk da bai tanaji abinda zai ce mata ba, yana cikin 'kwarin gwiwa.

Fatima ta fito itama a shirye take yace "salon kuma muje kiyita surutu kamar sadeey taa baki aron baki, tace "tohm yayanmu ba qawatah bace? Idan na shiga muka fara gaisawa ay dai sanda ka ganni, Yace "tohh bani adress dinnan kisha zamanki, tana dariya tace "da wasa nake maka yayanmu mu tafi!

Hajiya ce ta fito tace "kunanan har yanzu baku tafi ba? Fatima tace "yanzu zamu tafi hajia, Abduk ya du'ka yana ma fatima magana a hankali yace "ina sadeey? Tace "barci take ko in tasheta? Yace "ke, ki barta tayi barcinta wuce mu tafi.

Bankwana sukama hajia suka fita!!

Dedicated to Mr. Smiles😃

❤❤Rabiatu sk msh❤❤

Related Posts:

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts