New Post

Sunday, 16 October 2016

ABDUL WAHAB 17

ABDUL WAHAB  17
                        
©Rabi'atu sk msh 
         ®NWA                       

Nan da nan fatyma ta kira family doctor din su, Hajia ta taimaka mata suka maida ta saman kujerar falon hnklnsu duk a tashe. Ba'a fi 5mnts ba sai gashi ya iso dauke da kayan aiki kasancewar basu da nisa sosai.                                            Nan ya shiga dubata cikin qwarewarsa.  Sannan ya dago ya kalli Hajia,  Hajia tace "Doctor me yake damunta? Dr ya gyara tsayuwa tare da cewa

"Wato Hajia ta fadi ne a dalilin firgici ko kuma ince tsoro na jin wani abu ko kuma gani, wanda hakan ne yayi sanadiyyar faduwarta" Hajia tace "To ynx y jikin nata yaushe kuma xata farfado?" Dortor yace "Insha Allah nan da 20mnts xata tashi".                                           Fatyma ta kalli Yaa Abdul da hnklnshi yayi matuqar tashi don ya tabbata Sadeey taji wayar da sukayi da Khadeejah.

Hajiya ta kalleshi tace "Abdul me ya sameta meye dalilin faduwarta? Abdul kuwa duk ya rude ya ma rasa me xai ce mata ya daga kai ya kalli Hajiar sannan yace" Hajiya nima bansan me ya sameta ba ina cikin bedroom naji faduwarta".                                 Nan Doctor yayi musu sallama ya tafi. Hajia ma ta miqe don xuwa daki ta dawo. Fatyma ta matso kusa dashi tace "Yayanmu me ya faru da Sadeey? ".         Ya kalli Fatyma sannan yace " Ina tunanin taji wayar da muka yi da Khadeejah ne tunda ina cikin wayar ne naji faduwarta".

Fatyma ta dafe kai tace Tab "Akwai matsala kuwa, ynx ya xa'ayi idan Sadeey ta tashi"? Yace " Nima tunanin da nike kenan, ko ya xance mata?".                                        Fatyma tayi shiru kamar tana naxari sai kuma tace"Yayanmu ka dai yi naxarin abinda xamu fada mata don ni kaina gaba daya ya kulle" Abdul yace "Ke kenan ma, ni ina ga barin gidan ma xanyi kafin ta farfado don bansan me xance mata ba.

Dedicated to Mr. Smiles

❤❤Rabiatu sk msh❤❤

Related Posts:

  • A YINI ƊAYA 5-6[11:54pm, 19/09/2016] Amrah💓Pinky💓durling😘: 💀 *A YINI 'DAYA* 💀    👹💀            💀👹  … Read More
  • A YINI ƊAYA 5-6[11:54pm, 19/09/2016] Amrah💓Pinky💓durling😘: 💀 *A YINI 'DAYA* 💀    👹💀            💀👹  … Read More
  • A YINI ƊAYA 9-10[8:02pm, 21/09/2016] Amrah💓Pinky💓durling😘: 💀 *A YINI 'DAYA* 💀    👹💀            💀👹  … Read More
  • A YINI ƊAYA 3-4[11:35pm, 19/09/2016] Amrah💓Pinky💓durling😘: 💀 *A YINI 'DAYA* 💀    👹💀            💀👹  … Read More
  • A YINI ƊAYA 7-8[5:09pm, 20/09/2016] Amrah💓Pinky💓durling😘: 💀 *A YINI 'DAYA* 💀    👹💀            💀👹  … Read More

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts