ABDUL WAHAB 23
©Rabiatu sk msh
®NWA
Hidimar bikin fatima kawai ake, kullum basu da zama, shirye shirye kawai suke da tsarin yanda bikin zai kasance, ga rabon i.v da gyaran jikin amarya, itama sadeey ba'a barta a baya ba don akwaita da son gyara.
Duk hidimar bikinnan bata yarda ta 'kara zuwa gidansu Abdul, har fatima taayi nacinta taa gaji, sai dai ta biyo mata su wuce.
Koda satin bikin ya kama aka fara programmes babu wanda sadeey taje, fatima har fushi tayi da ita, Mami ma har fad'a tayi mata ta saka mata kukan ita ba zata iya zuwa ba, bata son duk wata hanya da zata had'a ta da Abdul.
Shima duk hidimar bikinnan baida wani aiki sai zaman d'akinshi, gashi yanzu hajia ko kad'an bata sakar mishi fuska, tun tuni taso a had'a bikinshi dana fatima anma yaa'ki ya kawo mata, yanzu gaisuwarshi ma da'kyar take amsawa, duk damu taa taru taayi mishi yawa.
Raheem ne yace "Abokina dolene fa kayi abnda hajia zata huce dakai, kuma sadeey ma ka wanke laifin da kayi mata," Yace "ta wacce hanya kenan? Banji me yace mishi ba sai dai Abdul yace "kana ganin hakan zai yiwu? Raheem yace "sosae ma kuwa, don kai kanka kasan sadeey na matukar sonka, Alhajin kawai zaka samu da maganar, ko kanaso ka cemin kai baka fara sonta ba?
Sai yanzu naga murmushin Abdul Yace "ba farawa ba Raheem, sai yanzu na gane soyayyar da nake yima sadeey, da da na kasa ganewa, tabbas nayi kuskure, anma kai zaka taimakamin wurin gyarota.
Yace "shikenan anjima nizan rakaka wurin Alhajin.
Koda sukajema Alhaji da maganar, kasa 'boye farin cikinshi yayi, don shima yasan irin sonda sadeey ke yima Abdul kuma yaa dad'e da sha'awar had'asu aure, hajia ma taaji dad'i sosae koda Alhaji ya nemi shawararta cewa tayi komi yayi dai dai ne su duka yaranshi ne.
Mami ce ta bada shawarar kar a fad'ama sadeey yanzu, kowa ya amince da shawararta.
Dedicated to Mr. Smiles😃
❤❤Rabiatu sk msh❤❤
0 comments:
Post a Comment