ABDUL WAHAB 2
©Rabiatu sk msh~
®NWA
Ta juyo tana kallonshi duk taayi tsuru-tsuru da ido sai huci take taama rasa me zatace mishi, yana mata kallon mamaki yace "wane irin kallone kkemin haka buguna zakiyi? Watau kimin laifi kuma ki tsattsareni da ido ko? Raheem yace "haba frnd ka qyaleta ka taho muje kana qara bata mana lokaci!
Baice komi ba ya juya ya shige motah itama ta shige tata motar ba tare da tace komi itama sai dai ko wanne ta ciki na ciki, ta janye motarta suma suka wuce!!
Da 'bacin rai ya isa gida, saida ya tsaya qofar d'akin yayi knockn, Da sauri ta qaraso ta bude mishi, bata bashi hanya ba ko lura da 'bacin ran dake fuskarshi batayi ta fara magana "Oyoyo yayanmu! Kasanme? Bnji tsayuwar motarka ba, kawai ynda kayi knockn dinnan jikina ya bani kaine! Sai kuma ta shagwabe fuska, shne kawai zaka fita yayanmu bakamun bankwana ba? Nayi missing ganin kwalliyarka yau har wasu sun rigani gani, anma ko hoto ay daka jira naayi maka"!! Ita kadai keta surutunta, ko motsawa baiyi ba hankalinshi da tunaninshi duk sun tafi ga abnda ya faru yau! Tunanin yake meya kamata yayi ma yarinyar can?
'kara katse mishi tunani tayi tace "yayanah juyo muyi selfie" har taa fito da wayan tana niyyar saitashi ta musu hoto fatyma qanwarshi ta fito da qarfi tace "ke Aku riqe mana bakinki!
Da sauri kuwa ta saka hannu ta riqe bakin ko motsi bata qarayi ba, sai da tazo ta dafa Abdul sannan ya dawo tunaninshi, bai cema fatyma komi ba, sai dai kawai ya wuce dakinshi, itama fatyman ta wuce ta barta anan duk da taaga alaman damuwa a fuskar yayanta, anma bata tsaya tmbyrshi ba tace "koma miye taa tambayeshi idanya dan samu nutsuwa!!
Suna shigewa ta sauke hannunta sannan ta dage kafad'a tace "shikenan SADEEY, sauke hannun!! Ta maida 'kofar ta rufe tana murmushi tace "SADEEY ne sunan ba Aku ba!!
***
Da safe yana tashi har lokacin zuciyarshi bata mishi dadi, can falon d'akinshi ya jiyota da magenshi ita da bata raina abokin labari, duqawa tayi dai dai inda take ta d'aukota tana shafa bayanta, tace "babynah kin tashi lapia? Kinfison yayanmu dani ko? Kullum baki kwana a dakina sai dai ki gudo nan? Ya farka daga barcin?? Mu riga zuwa dakinshi!!
Aykam kafinta rufe bakinta magen ta ruga a guje ta bita tana fad'in "ki tsayani, ki jira nace! Wayau kikamin ban shrya ba kika ruga, Sai da ta shiga bedroom din sannan ta tsaya"
Yana jiyosu yayi saurin janyo blanket ya rufe jikinshi yayi lamo kamar mai barci!!
Dedicated to Mr. Smiles😃
❤❤Rabiatu sk msh❤❤
0 comments:
Post a Comment