New Post

Sunday, 16 October 2016

ABDUL WAHAB 1

ABDUL WAHAB   1

©Rabiatu sk msh~
        ®NWA

Cikin sauri suke tafiya shida abokin nashi anma cikin tsari da nutsuwa! Kyakkawan gaskene fuskarshi cike da qwarjini, kallo d'aya dana mishi na tabbatar ba mai son yawan mgn bane! Firar da sukeyi da abokinshi ne yaja hankalina hrna matsa dauko muku rahoto...

Saida ya yamutsa fuska sannan yace "me ake da soyayyah? Kawai 'bata lokaci ne don ko kad'an ni ban yrda akwai soyayyar gaskiya ba! Ban yrda anayin auren soyayyah ba! Abokin nashi yace "anma ka yrda anayin aure ba?? Daria yayi sosae sannan yace "nima ay bnce bzanyi aure ba! Tunda su mum sun matsa, anma dai bana soyayya ba, don har yau banga macen data ta'ba zuciyatah da sunan soyayya ba! Tun daga uganda da nayi karatu har nan nigeria!

Yace "Abdul knan, kana nufin dk en matan 9ja babu wacce tayi maka da sunan syy?? Yace "mgnrka hakan take! Ba kamr ynzu da mata suke zubar da ajinsu ni abnma har dariya yake bani! Zo kaga ynda 'ya'yan aminan momie dana en uwanta ke zarya gidan dga dawowanah ko wacce da nata salon!! Yace "kai kuma ba wacce ta maka! Yace "har ynzu babu ita a duniyar nan!!

Gani nayi yaa had'e rai lokaci d'aya yanayinshi ya canza, da sauri nakai idanuwa na inda yake kallo, cikin 'bacin rai yake kallon inda yayi parking motarshi yana fad'a, "ko motar uban waye yazo ya saka ya rufe mu? Wlhy wasu mutanen neman magana ne dasu! Ba'asan uzurin mutum ba za'a kama rufeshi!! Abokinshi raheem ya dafa kafad'arshi yace "calm down mna Abdul! Fad'anka ay bzai kawo wnda yayi parking dinba! Kafin ya rufe baki Abdul ya jiyo wurin raheem cikin masifa kamar shiya mishi laifin yace "shruna ne zai kawoshi ba? Kai knka kasan saurin da nake! Ka nemo mna wnda yayi parking dinnan!

Ganin raheem baida niyyar motsawa yasa Abdul ya qara shaqa gashi har lokacin baiga alamar mai motar na zuwa sai faman kallon agogo yake, shikam raheem abnma dariya ya bashi don ko kadan Abdul bai iya fad'an ba, donshi bamai yawan magana bane!

Juyawa kawai Abdul yayi da niyyar shiga restaurant din idanunshi rufe saboda 'bacin rai ko kan raheem bai qara bi ba, yana shiga dai dai lokacin tana fitowa babu wanda ya kula da wani sai da sukayi wani irin karo dk suka bugu da juna tayi wani irin juyawa tana niyyar faduwa cikin zafin nama ta dawo tana niyyar fad'a mishi, ya turata da iyakar qarfinshi ta fad'i da bayan har saida qafarta tayi qara itama qarar ta saki kamar zatayi kuka!

Ba tare daya kalleta ba yace "m srry" kawai ya tafi cikin d'aga murya tace "srry? Abnda kawai zaka iya cema wnda ka buge knan? Ya juyo yana kallonta cikin mamaki ta miqe daqyar ta qarasa inda yake! Tana magana ita kadai! "sufa mazan 9ja dinnan dk hka suke! Bzasu ta'ba kauda kai ba idan sukaga mace

Ya dakatar da ita da hannu yace "karki kuskura kice zaki fad'amin magana! Na riga da naa baki haquri, a hnkali yace "matan 9ja dk inda suke sai sunyi qoqarin shge maka!

A harzuqe tace "kai, kasan ko ni wacece? Sunana KHADIJA baka isa ka wulaqantani ba! Wlhy saina rama!! Tsoki yaja kawai ganin tana qara 'bata mishi lokacin ya juya kawai ya fita!!

Itama jikkarta ta d'auka kamar zata tashi sama ta fita dga wurin gashi dk mutanen kallonta suke!!

Kusa da motarta ta hangoshi tsaye ta qara sauri ta qarasa da niyyar shiga motarta! "lallai yarinyarnan! Daman ita ta rufe mu dk ta 'bata mna lokaci? Bari ka gani ya matsa inda take! Raheem na riqeshi anma saida ya qarasa inda take ya fizgota ta baya

Dedicated to Mr. Smiles😃

❤❤Rabiatu sk msh❤❤

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts