[5/4, 3:48 PM] ✍🏻rerbee'art sk msh: 🎄🎄HAFSATUL KIRAM🎄🎄
🎄
🎄🎄
🎄🎄🎄
🎄🎄🎄🎄
🎄🎄🎄🎄🎄
🎄🎄🎄🎄
🎄🎄🎄
🎄🎄
🎄
NA
Rabiatu sk msh
4⃣4⃣
Momie saida ta qaraso gabansu sannan tayi murmushi tace "Duk naa fahimceku, tana kallon Umar tace "bzaka koyama d'iyata rashin kunya ba, ynzu dai dare yaayi kazo gobe ka dauki matarka ku tafi!
Wani irin farin ciki ne ya bayyana a fuskar Umar don tsananin jin dad'i kamar ya rungume hafsatul kiram yakeji, yaa qagara sosae hafsatul kiram ta koma gidanshi ya fara nuna mata soyayyar da yake mata da kulawa....
Washe gari yana dawowa da shirin office gidan momie ya wuce, hafsatul kiram naa zaune ana zana mata qunshi a hannu ya shgo da fara'arshi cikin nishadi ya zauna! Suka gaisa da momie sunata fira, hafsatul kiram kau tunda ya shgo ta gaisheshi ta duqar dakanta!
Tana d'agowa suka had'a ido da sauri ya mata alamar yanason magana da ita, ta waro ido sannan ta girgiza kai tana nuna mishi momie, langabar dakai yayi yana mata alamar ta taimaka, d'aga kafada tayi alamar bzata iya ba sannan ta duqar da kanta.
Sai dai kawai ta ganshi yaa durqusa gabanta saman gwiwoyinshi da sauri ta waro ido taa rasa yanda zatayi don kunya, ya langabar da kanshi yana kallonta yace "nasan bzaki taba mntawa da abubuwan da suka faru a baya ba hafsatul kiram, nasan naa cutar dake, naa azabtar dake, A yau zan d'aukar miki alqawarin kulawa dake, sanyaki farin ciki bzan ta'ba barinki ki kuka ba har abadah! Ina sonki hafsatul kiram!
Duqar da kanta tayi tasa hannu ta rufe fuska, momie kam don tsananin jin dadi sai murmushi kawai take, taa shima Umar Albarka sosae sannan ta musu fatan zaman lafiya da farin ciki mai d'orewa!
Da dare suka tafi gidansu cike da farin ciki, suna isa gidan yana riqe da hannunta, ya bud'e mata qofar, cikin mamaki take kallon falon
Ya qawatashi da fitilu kala-kala yaayi matuqar had'uwa, ta juyo ta kalleshi ya kashe mata ido, tana qarema dakin kallo suka qarasa ciki
Har gaban cake ya kaita yana murmushi sannan yace "Happy birthday to uh my lovely wife! Sannan ya watso mata flowers masu kyau da qamshi ta rufe ido ta bud'e a cikin jin dadin ynda umar ya tuna da birthday dinta!!
Ranar ta zame musu ranar farin ciki, bayan sunyi alwala sunyi sallar miqa godia ga ubangiji, sun dad'e suna jero addu'o'i, kafin cikin zaquwa Umar yaja hannun hafsatul kiram zuwa gado!! Ganin irin kallon da yake mata yasa nasan wannan al'amari bai buqatar in tsaya daukar rahoto cikin hanzari na rufo musu 'kofar!!
Lurv my princess Amrah😘
❤❤Rabiatu sk msh❤❤
[5/4, 5:33 PM] ✍🏻rerbee'art sk msh: 🎄🎄HAFSATUL KIRAM🎄🎄
🎄
🎄🎄
🎄🎄🎄
🎄🎄🎄🎄
🎄🎄🎄🎄🎄
🎄🎄🎄🎄
🎄🎄🎄
🎄🎄
🎄
NA
Rabiatu sk msh
4⃣5⃣
Soyayyah sosae da kulawa hafsatul kiram ke samu daga wurin mijinta Umar, ko motsi tayi yace "me take buqata?? Wani irin so yake mata fiye da duk tunanin mai karatu, ynzu bata da kewar gida duk sanda take da buqatah yana kaita don duk abnda zai sakata farin ciki yakeyi!
Bayan shekara shida 6..
Hafsatul kiram ce kwance saman qirjin Umar sai zuba mishi shagwaba take yana wasa da gashin kanta yace "kin shgo cikin rayuwatah kin canjata da kyawawan halayenki, i'm a changed person, koda yaushe inajin sonki a cikin zuciyatah, kome kike qaramun sonki yake...na yrda dake hafsatul kiram, ina sonki sosae! Ina matuqar alfahari dake.
Murmushi tayi ta d'ago tana kallonshi suna shaqar numfashin juna tace "ba zuciyatah kawai na baka ba yaa umar, naa mallaka mka kaina, ruhina, da dk wani abu dana mallaka komi naka ne, bnda abnda ya ragemin kullum cikin yi mka addu'ah nake mijinah, da ina da kyautar data wuce zuciyatah da naayi mka, ngde sosae da soyayyar da kakemun! Zan soka har abada, babu abnda zai rabani dakai, ta kwantar da kanta jikinshi!
Ya shafi gashin kanta yana murmushi yace "ke mace ta gari ce hafsatul kiram, ina Alfahari dake!! Da sauri Abubakar da qanwarshi zainab suka rugo suka rungume iyayensu nasu, tare suka had'a baki sukace, "Muma muna Alfahari dake sosae momie, muna alfahri da samun uwah ta gari!!
Hawayen farin ciki na share sannan na musu gyaran murya dk suka juyo suna kallona, Abubakar da zainab suka rugo sunamin oyoyo! Na kalli Umar nace "Don Allah ka qara riqe mana hafsatul kiram amana, mace d'ayace a cikin miliyoyi!
Girgiza kai yayi yace "A'ah aunty rabiatu, hafsatul kiram d'ayace a cikin duniyar nan, tun bayan labarin Rabiatul badawiyya da naji, bn ta'ba jin labarin macen dake matuqar biyayya ga mijinta ba kamar hafsatul kiram!!
Murmushin jin dadi nayi hafsatul kiram ta taso saitin kunne na ta rad'amun "Aunty yaa kamata kiyima masu karatu sallama hakanan, Allah yasa zasuyi koyi da Abnda suka karanta!!
Alhmdlh....
Anan na kawo qarshen wannan littafi nawa hafsatul kiram, ina fatan Abnda nayi kuskure Allah ya yafemun!!
🌿Hafsatu kiram🌿
Taa samu soyayyar mijinta babu boka, babu malam ba tare data bi wata hanyar ba ta nuna zaqewar, sai tsantsar addu'ah, haquri, juriya, biyayya, sadaukarwa, kau da kai, tunani da hangen nesa, mutumtawa da girmamawa!! Babu wanda zakaima wannan a soyayyar bai daukeka da qima da daraja ba ya fifita ka akan komi, duk mai haquri dk dadewa zai samu wadata, biyayya na da matuqar amfani a zaman aure! Allah ya bamu ikon farantama mazajenmu, yasa mana haquri dasu ya bamu ikon yi musu biyayya!! Allah ya bmu ikonyin amfani da abnda muka karanta muka qaru dashi
Sadaukarwa!!
Wannan littafi sadaukarwa ne ga hafsat Ahmad tijjani, Allah ya rayaminke da kyawawan halaye irinna hafsatul kiram, ya baki miji na gari ba irin Umar ba..ameen!!
Saqon godia ga..
Khausar luv da
Nana disco
Taki ta dabance:
My lovely sis princess amrah, kalamai bzasu iya bayyana ynda nake jinki a raina ba, kina tare dani a duk lokacin da nake da buqatar qawa ko er uwah! Allah ya barni dake
Jinjina ga duk
Online hausa writer's extreme hausa writers
Wisdom hausa writer's
Excellent hausa writer's
Best writer's
Da duk group din da nake ciki
Dole na ambace ku
Sis ummeterh
Zahra bb
Sadeeya afka
Khadija candy
Haneefa usman
Shafa'atu
Mrs Umar
Rash kardam
Asmeey b Aleeyu
Meesha luv
Baby Amrah
Sadeey
Autar hajia
Maman Abideen
Stylish
Jeeddah Aleeyu
Munay
Qurratul ayni
Bebeelo
Hajar
Allah ya bar zumunci, ya qara baseera!!
Ya za'ay na manta da?..
Abdul jega (mr smiles😃) Amanar Aure!! Allah ya qara maka hazaqa da baseera Ameen!!
WANI ZAMA ne tsakanin MARYAM KO MARYAMA, shin QADDARA ce KO RA'AYI?? Sai dai babu wadda taci AMANAR AURE a cikinsu, ko MIYE SANADI? DAN BAUTAR QASA Yace "BANI BANE. PRINCESS AMRAH tace "wacece MAI FARIN JINI a cikinsu? 'YAR AUTAH tace "tabbas HAFSATUL KIRAM ce tauraruwa! Hafsat tace "bani bace don duk qayatuwar labarina bzai kai LABARIN RABIATU ba!!
Littafan marubuciyar kenan!!
Wani Zama da
Labarin Rabiatu zasuzo muku tare da wasu mazan wasu matan!!
SUNANA ABDUl ma yananan tafe!! Ngde sosae masoyah na!! Kuci gaba da kasancewa dani, ina qaunarku gaba daya..
Domin gyara ko fad'in ra'ayinku
👇🏻
08032133670
Taku ce a koda yaushe
❤❤Rabiatu sk msh❤❤







0 comments:
Post a Comment