New Post

Monday, 31 October 2016

MARYAM KO MARYAMA 141-155

[10:05, 3/20/2016] Rerbee'art: 🌿MARYAM KO MARYAMA🌿
❣soyayyar whatsapp❣
@OHW
141-145
Washe gari wurin azahar maryama kwance tana tunanin Ahmad, Yaro ya shgo yace wai ana sallama da Maryama, gwaggo tace "gatanan zuwa! Maryama ta zari mayafi ta fita tana tunanin waye zaizo wurinta da tsakar rana hka, ita ko fira ma bata tabayi b a qauyensu
Ahmad ta hango jingine a motarshi, fuskarshi cikin da annuri yasha kyau! Mamaki ne ya kamata tohm ya akai ahmad yaxo gdan guggo? Wani ya fada mishi garin da take?? Cikin kame kame tace "Aboki kaine? Gsky naayi mamaki?? Waya maka kwatancen nan? Wani yace mka nan garin nake? Yace "wannan tambyar dk ni kadai kamar bakiyi farin ciki da gani na ba? Kin kama waya kin kashe Abokiyah kuma kinsan babu wanda yasan inda kke? Driver na dana taba sanyawa ya kaiki gida shiyaimin kwatancen nan Yace ko bn sameki ba za'a fadamin inda kke! Tace "tohm sannu da zuwa abokii gsky naaji dadin ganinka, nan gdan kakatah ne! Yace "tohm mu shga in gaidata Abokiyah don zuwa nayi in tafi dake Maryam bata lpy sosae! Da hanzari ta kalleshi tace "ya salam meya sameta? Yace "babu lokacin bayani kedai ki musu bayani mu tafi!!
Cikin hanzari ta shrya bayan taayima guggo bayani, Gwaggo tace "suma sunanan tafe tunda dama basu zo biki ba!!
Basu suka isa katsina ba sai ana sallar isha'i, basu zarce ko ina ba sai gdan Maryam cikin saurinta ta fito yana gama parking ta ruga cikin gdan saboda yanda ta qagara taga Maryam, tsayawa tayi hango Maryam da tayi durqushe kusa da deen da yake kwance dk yaayi zuru-zuru saboda wahalar ciwo! Ga en uwanshi dana Maryam zazzaune!
Maryam tasowah tayi tana kuka ta fada jikin Maryama tana cewa ki yafemin namcy tabbas bn cancanci zama qawa a wurinki b, na zama maci amana muguwah mai raba masoyah! Maryama tace "bngane ba meke faruwah takwarah? Cikin kukah Maryam tace shams dinnan da kke kalla a matsayin mijina, deen dinki ne, ta basu lbrn dk Abnda tayi!! Cikin hawaye ta qarasa
Maryama kasa cewa komi tayi, sai hawayen da takeyi, deen kuma Maryam yake kallo cike da tsana dajin haushi, momie kuwah tashi tayi ta qarasa inda Maryam take ta rufeta da duka tana cewa "tarbiyyar da mukai miki knan Maryam?? Maryama na zaune dake da zuciah daya sakayyar da zaki mata knan? Deen ta kallah tace "ka saketa kawai babu amfanin zama da munafukar yarinyar nan! Sadda kai yayi cike da alkunya dk da damn shima abnda yake niyyaryi knan! Daddyn deen ne Yace "A'ah hajia wannan ba shne mafita ba!
Ahmad ne ya qarasa inda Maryama take tsaya hawaye na sharara a fuskarta bata ce koma ba, Yace "tunda nake Maryama bn taba yrda da soyayyar gsky ba sai yau, tabbas deen Masoyinki ne na gsky, Soyayyarku hadine dga Allah babu wanda ya isa ya rabaku, juyawa tayi tana kallonshi cikin ido tace "Ahmad ba maganar wani ya fiso ake ba, cancanta zaka duba, na yrda shams shne deen dina anma kuma mijin Maryam ne! Taya kake tunanin zan zauna da Maryam a matsayin kishia? Momien Maryam ce tace "bzaki zauna da ita ba, dole ne ya saketa ta gane kuren da tayi!
Girgiza kai Maryama tayi tace "nipa momie na riga dana haqura da deen, ta kalli Ahmad tace "meka dauki zuciah ne? Zuciah ba Abune da za'a dinga cnja ma tunani da ra'ayi ba dk sanda akaso, jiya na amince da aurenka Yau kuma kana kallon idonah kacemin in amince da auren deen?
Rabiatu sk msh
[12:53, 3/20/2016] Rerbee'art: 🌿MARYAM KO MARYAMA🌿
❣soyayyar whatsapp❣
@OHW
146-150
Deen ne ya dafe qirjinshi kamar wanda ake tsira ma wani Abu, sauke ajiyar zuciah tayi a ranta tace "lallai wannan mutumin zaiyi kyau da Acting, dk da sosae ya bata tausayi kuma soyayyarshi ta dawo mata sabuwa fill Yace "ina sonki Maryama, ke kanki kinsan hkan tun kafin in ganki insan ynda kke, shin bzaki duba grman wannan soyayyar ba ki amince da aurenah? Maryam tace "idan har bzaki amince da auren deen ba zan dauka baki yafemin bne Maryama akwai daukar da kkamun a zuciah! Soyayyar deen ce data shgeni lokaci daya ta sanyani aikata hakan, don Allah ki yafemin Maryama! Momie tace "muma bzamu taba yafe miki ba indai Maryama bata amince da auren deen ba! Cikin tashin hankali Maryama ta kalli momie, tace "mun gama yanke maganarmu suka tashi zasu tafi, Maryama tace "don Allah momie karkuyi fushi da maryam na amince zan auri deen, nan da nan fuskar kowah ta koma cikin farin ciki
Tace "anma da sharadin bzai saki Maryam ba, kuma bzai taba nuna bnbnci a tsakaninmu ba! Maryam tayimin halaccin da bzan mnta a rayuwatah ba, batasan asalinah b batasan inda na fito ba ta daukeni na zaunah a gdansu harna qare karatunah, rabuwatah da deen harda kuskurenah, nan take ta basu labarin qarairayin data dinga shryawah! Tace "nayi hkane sbd rayuwar makarnta kowah yafiso yayi hulda da dan mai kudi, kuma bn dauka alaqarmu zatayi nisan hka ba, anma ku yafemun don Allah! Maryam tayi hkane don tanason deen, ko kadan bnji haushi a raiba ba don Allah momie ku yafe matah
Momien deen tace "gsky naayi sa'a da samun suruka mai kyakkyawar zuciah kamar maryama, Allah yai miki Albarka ya baku zamn lpy! Momien Maryam tace "kin gani ba? Dk abnda kkaima maryama anma ita take nema miki yafiya? Kiyi qoqarin koyan halayya mai kyau wurinta, Allah yai miki albarka Maryama, daddyn deen dana Maryam ma Albarkar suka sanyama Maryama, Ahmad kuwa tuni ya fice yana hawaye! Shikam deen baice komi ba sai farin cikin da yake kamar ranar aka daura musu aure da Maryama!!
Kasancewar dare yayi su duka sukai sallama suka tafi akabar Maryam da deen, Maryama kuma Momie suka tafi da ita gdansu Maryam a can zata kwana!!
Rabiatu sk msh
[12:53, 3/20/2016] Rerbee'art: 🌿MARYAM KO MARYAMA🌿
❣soyayyar whatsapp❣
@OHW
151-155
washe gari iyayen Maryama sukazo harda gwaggo, bayan sun huta a gdansu Maryam, Momie tayi musu bayani cikin fahimta suma sun nunah amincewarsu, kuma saida suka tilasta mahaifan Maryam suka yafe mata!!
An hadu aka tsaida ranar Auren Maryama da deen 1week (Allah sarki Maryam ko 2weeks batayi da aure ba za'a mata kishia *tears* lol) daddyn Maryam ne yace shizai dauki hidimar duka, don bikinma so yayi su mama su zauna katsina ayishi, anma baba yace qara dai su koma can kaduna ayi saboda danginsu basu san da bikin ba!!
Maryam da deen kuwah tun ranar basu qara haduwah ba, shrye shryen bikinshi da Maryama kawai yake don Maryam ta fita ranshi damn ko kadan bai tabajin sonta ba, ita dinma bata shga harkarshi saboda tsanarta da take hangowa a idonshi, taa wani koma kalar tausayi!!
Tun kafin ranar bikin tazo ake shagulgula sosae ansha shagali, anma nidai babu wanda na halarta saboda jin haushin Maryama bata auri Ahmad ba don sosae naaso auren Maryama da Ahmad!!
Ranar da aka daura aure aka kawo Amarya qaton gdansu mai shegen kyau ita da Maryam da deen dinta, a lullube aka kaita dakinta da aka tsara mata, Maryam kasa fitowah tayi tana daki
Kowah yaa watse Maryama na kwance tana tunanin wai yau itace da auren deen abnda ta dade tana mafarki, kuma wai gida daya da Maryam a matsayin kishia, tohm wane irin zama zasuyi?? Ita ko a littafi ko a film bata tabajin wannan Al'amari ba, ita da an barta da Ahmad kawai zata aura suyi zamnsu ta qyale Maryam da deen, wata zuciar ce ta gargadeta da tunanin wani tunda ynzu taa zama matar deen
Tana cikin tunanin ya bude qofar ya shgo, kanta a qasa ta lullube da mayafi ya ajiye ledar hannunshi gefe ya qarasa inda take cikin farin ciki ya yaye gyale ta rumtse idonta yayi murmushi yace "yau taa kasance ranar farin ciki a gareni, ranar da bzan mnta da ita ba, ji nake kamar nafi kowah sa'a da samun macen datafi kowacce mace kyau, wadda take fahimtata a kyawawan watannin da mukai muna soyayyar whatsapp, wadda zata kula dani, i'm fortunate da samunki kusa dani, ita dai batace komi ba sai sadda kai da tayi a qasa Yanata surutunshi batace komi ba sai farin cikin da take yau gata ga deen a matsayin mijintah!
Tashi yayi yana cewa naa mnta pa bn siya baki ba, ya dawo ya zauna suna gogar juna ya kamo kyawawan yatsunta ya zira mata zobe ta waro ido tace "deen tana murmushi ya daga matah gira yace "cewah zakiyi deen ina sonka! Ta noqe kafada tace "naqi, yace aikam saikin fada yana qara matsawa inda take, tace "bzance bpa! Yace "aikam yau saina sanyaki cewa kina sonah! Tace "hka kace ko? Ta matsa ta fara mishi cakulkulo yana daria ya kamota ta zulle ta tashi ta nufi falo tana gudu su duka suna daria cikin farin ciki, sai data gaji don kanta ta tsaya tana kallon deen cikin ido tace "ina sonka sosae Masoyi! Kamotah yayi sosae ya rungume kamar wani zai qwace mishi, tana lafe a jikinshi tace muje mu gano Maryam tunda nazo bn jiyo motsinta ba, shru yayi donshi tsakaninshi da Allah yama mnta yana da wata mata!
Dagowah tayi taja hannunshi tace "muje masoyi! Taja hannunshi suka tafi dakin Maryam, tana zaune ta jingina da gado da Alama tunani take hawaye wasu na korar wasu!!
Rabiatu sk msh

Related Posts:

  • ABDUL WAHAB 24ABDUL WAHAB 24 ©Rabiatu sk msh           ®NWA Ranar d'aurin aure, sadeey ta daure ta shirya tunda safe saboda yanda fatima ke fushi da ita ta'ki zuwa bikinta, taa riga ma… Read More
  • ABDUL WAHAB 27ABDUL WAHAB    27 ©Rabiatu sk msh           ®NWA                 Shi kuwa … Read More
  • ABDUL WAHAB 25ABDUL WAHAB 25 ©Rabiatu sk msh           ®NWA Da'kyar ta share hawayenta, ni'kab dinta ta ciro ta maida, kanta na 'kara tsananta mata ciwo kamar zai rabe biyu Haka ta fit… Read More
  • ABDUL WAHAB 27ABDUL WAHAB    27 ©Rabiatu sk msh           ®NWA                 Shi kuwa … Read More
  • ABDUL WAHAB 26ABDUL WAHAB 26 ©Rabiatu sk msh           ®NWA A firgice ta farka, tana fad'in innalillahi wa inna ilaihir raji'un, du'kar da kanta tayi yaa daina mata ciwo, fara tariyo d… Read More

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts