New Post

Sunday, 23 October 2016

MAKASHINKA 37-38

```MAKASHINKA...```
         37-38

©Rabiatu sk msh

Da sauri kaka ta ɗebo ruwa a buta ta nufota dashi tana mata sannu, suma duk tsayawa sukayi suna mata sannu.

Shamsuddeen da sauri yayi ƙoƙarin kareta "Kema kaka saida na faɗa miki bazata iya cin abinci mai nauyi ba, kwana biyu zazzaɓin cizon sauro tayi" huraira tace "suma gidan ƴan gayu har akwai sauro kenan? Sannan kaka ta saki baki da duk taa damu taa ɓata ma ƴar mutane ciki ta kalli huraira tace "rufema mutane baki," sannan ta kalli shamsuddeen tace "Shikenan ay sai a dama mata fura, tunda dai bazata zo ta tafi da yunwa ba," dafe kanshi yayi, ko gurɓataccen ruwan unguwar tasu ma saiya ƙara ɓata ma sadeey ciki.

Hanne da bazata wuce shekara 14 ba tace "bari in ɗauko mata dawo a dama mata, ɗazu dije ta bada aka daka mata (mahaifiyarta)," kaka tace "Yauwah yi sauri kice ta baki ki kawomin, bari Malam yazo ya siyo nono" Shamsuddeen yace "bari in siyo kaka" don idan ya tafi karya dawo har sai zasu tafi ko yaje gari ya siyo mata ta roba, anma kaka sai tace "A'ah ka bari malam ya fika iya siyen mai kyau" yace "Shikenan tohm kaka nina tafi wurin hafeez".

Malam Ya siyo nono kindurmo mai kyau na dama furar suna zaune tsakar gida wurin inuwar bedi suna fira, Yace "ga yalo nanma idan zataci" sadeey sai kallonsu take gasu dai cikin garin jigawa, anma rayuwarsu kaf irinta ƴan ƙauye.

Har malam yaa kusan shiga ɗaki kaka tace "tohh malam ga yalon ko zaka ci" Yace "A'ah ita na siyo mawa" ta fara dama furarta suna labari sai surutu suke ma sadeey sai dai ta bisu da murmushi.

Saude tace "kaka zanyi magana anma kar kice komi," tace "yi maganarki ina jinki" taci gaba da dama furarta, saude tace "kaka don Allah ki ajiye damun furar yanda zaki jini" ta ajiye ludayin tana kallon ta, tace "Anma dai bakuwar shamsuddeen ba'a ƙasarnan take ba ko? Kalli fatarta mai kyau kamar bata mutane ba" duk suka kwashe da dariya harda sadeey, kaka bata ce mata komi ba taci gaba da dama furarta.

Ganin suna mata daria tace "kaka ba kice komi ba" kaka tace "kunji ni da mace, kefa kikace kar ince komi yanzu kuma kice ince wani abu?" Dariya suka ƙarayi ta yanzu har tayi yawa, malam ya fito zai fita yana dai dai wurinsu kaka tace

"Malam ga yalon fa," Yace "naace miki bani ci," ba tace komi ba harya kai ƙofar sannan ta kara cewa "malam a kawo maka yalon? Da ƙarfi yace "naace miki bani ci" ƙasa ƙasa suka fara daria kaka tace a hankali cikin ƙuluwar tayi mishi tayi yaƙi ci "babu haƙoran ci dai" har ya fita sunata daria kaka bata san yaaji ba sai gashi ya dawo har inda take dama furan yazo.

Kama hannun kaka yayi zai ciza ta fara ƙoƙarin ƙwacewa tana cewa karka cijeni, duk sun tsaya suna kallo, sai da ya cijeta ko ya sakar mata hannu yace "wai kiji in akwai haƙoran" haule da saude suka tafa sannan suka kwashe da daria, sadeey ma sai daria take.

Wani irin farin ciki takeji sai binsu take da kallo yanda suke wasa da daria, rayuwarsu gwanin sha'awah mai cike da sauƙin kai da burgewa.

Sai yanzu tayi magana "nikam kaka ya sunan unguwar nan? Karaf hurera tace "ba unguwa bace, ƙauyene ya haɗe da gari, anma dai har yanzu kamar ba cikin gari muke ba"

Kaka tace "tohh sarkin surutu, ke aka tambaya? Tace "tohm ay nima nasan amsar kaka, kullum harira cewa take wai gwamnati taƙi gyara mana hanyarmu, anƙi gyara mana magudanan ruwa, babu banbanci har yanzu tsakaninmu da ƴan ƙauye"

Saude tace "ke da akace za'a yima aure ma dakin cika shekara 15? Nan hurera ta ɓata rai tace "Shiyasa duk naa tsani shekara sha biyar" haule tace "ki daina cewa kin tsani shekara sha biyar idanfa kika mutu kafinnan?" ta zaro ido da taji zancen mutuwa tace "Anma ay inason shekara ashirin" dariya suka dinga yi mata wai tsoran mutuwa take.

Har kaka ta gama dama furarta suna firarsu cikin nishaɗi sai burge sadeey suke, sannan ta Miƙa mata furar da shamsuddeen ya aiko mata da pure water ta dama mata a sabon kwanon shan ruwanta

Sadaukarwa ga Sadeey S Adam, Fatan Alkhairi a gareki a duk inda kike.

©Rabiatu sk msh

Related Posts:

  • MAKASHINKA 63-64```MAKASHINKA...```           63-64 ©Rabiatu sk msh Damuwah ta ƙara yima sadeey yawa, kwana ukku ta ina zata samu hujjojin da kotu zata gamsu baida laifi? Ya Anwar ta kir… Read More
  • MAKASHINKA 61-62```MAKASHINKA...```           61-62 Washe gari... Aka mik'a shamsuddeen a gaban kotu, *A KOTU* An cika a kotun kowa yana jiran yaji ya wannan shari'ar zata kasance, Bayan alkali y… Read More
  • MARYAM KO MARYAMA 21-40[10:39, 3/10/2016] Rerbee'art: 🌿MARYAM KO MARYAMA🌿 ❣Soyayyar whatsapp❣ @OHW 21-30 Tana bude datar messages da yawa suka shgo mata, anma naashi ta fara dubawa, da wayarta glaxy s5 wadda Abokinta A… Read More
  • MAKASHINKA 65-66```MAKASHINKA...```           65-66 ©Rabiatu sk msh ƘARSHE Sadeey Sai zagaye ɗakin take cikin fargaba, a zuciyarta kuma addu'ar samun nasara kawai take, kasa haƙ… Read More
  • MARYAM KO MARYAMA 1-20[10:36, 3/9/2016] Rerbee'art: 🌿MARYAM KO MARYAMA🌿 ❣Soyayyar whatsapp❣ @OHW 1-10 Kishingide take saman lumtsumemiyar kujerarta 2seater da remote a hannunta! Masu aiki nata yi mata hidima, daya dga… Read More

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts