ABDUL WAHAB 4
©Rabiatu sk msh
®NWA
A dinning ya iske fatyma qanwarshi tana break fast, yaja kujera ya zauna sannan ta gaisheshi ta tashi tana zuzzuba mishi abinci.
Hankalinshi duk bai tare dashi sai data gama zuzzuba mishi tanata mishi magana yaayi shru, ta'boshi tayi da hannu yayi firgigit ya dawo tunaninshi, qura mishi ido tayi tana murmushi tace "ya sunanta yayanmu? Yace "wacece? Tace "wadda kake tunani mana, don yanayinka yayi kama da wanda ya fad'a ma soyayya!
Yace "soyayyah? Ni kuma? Haba da wannan yarinyar? Yama za'ayi naso wannan masifaffiyar yarinyar? Dariya sosae fatyma keyi tace "kacemin dai tunaninta kakeyi! Haba gaskiyah ce bakaso anma koda bn ganta ba taa gama burge yayanah tunda harya fara sonta!
Yace "kinga qanwatah nipa bazan ta'bason wata ba, zama da sadeey ta fara koya miki surutu ko? Dai dai lokacin sadeey ta kusan zuwa tun daga nesa ta 'bata rai kamar mai shrin kuka tace "nice ma nake da surutun?
Duk pa mezance don na damu dakai ne, Maganganunah basu wuce, ka tashi lafiya? Kaayi mafarkinah yau? Kanamayin tunani nah? Me zakaci na girka maka? Yau dawa dawa ya kallarmin kai? Wow! Wannan kwalliyar taka tayi kyau, in tayaka fira? Anma dai aikin yau bai baka wahala ba ko? Wane irin kaya......."?
Dafe kanshi kawai yayi yana saurarenta, fatyma ma ido ta zaro jin da tayi bata da alamar tsayawa ne ya sanyata cewa "ya isa haka aku, da wannan surutun naki ay saiki sanya kan yayanah ya qara girmah! Tace "wannan ne surutu? Mamanah tace idan bani kula dashi wata zata ita 'kwacemunshi, ta du'ko saitin fuskarshi har yana jiyo numfashinta tace "yayanmu ay dai bani damunka ko?
Miqewa yayi kawai ya d'auka brief case dinshi ya shiga gaisheda hajiyarsu, daya fito har wurin motah suka rakashi sadeey na qara tuna mishi da birthday partyn da zai kaisu don duk taa qagara anjima tayi.
***
Yana driving yana kallon titi kozai sake ganin khady, tuna yanda ya shaqotah yayi tana ta huci cikin 'bacin rai kamar zata dakeshi, dariya yayi a fili yace "rigimammiyah kawai, sai kuma ya d'aure fuska yana qoqarin daina tunaninta!
Harya tashi daga office tunaninta kawai yake sai sanda ya fahimtane yake fara qoqarin dainawa!
Yana shiga gida a falo ya iske raheem da fatyma suna labari sai dariya take shima raheem din dariya yake, yana shigowa suka hangoshi kamar masu ciwon daria suka qara kwashewa da dariyan fatyma hrda hawayen raheem naa riqe da ciki
Fuska ya musu ya nemi wuri ya zauna yace "malam lafiya daga gani zaku dinga daria? Bai bashi amsa ba saima yaci gaba da dariyarshi
My facebook page: Rabiatu sk novels
Dedicated to Mr. Smiles😃
❤❤Rabiatu sk msh❤❤
0 comments:
Post a Comment