```MAKASHINKA...```
63-64
©Rabiatu sk msh
Damuwah ta ƙara yima sadeey yawa, kwana ukku ta ina zata samu hujjojin da kotu zata gamsu baida laifi? Ya Anwar ta kira ta mishi bayanin Matsalarta sosae ya gamsu da bayaninta, Shima tsanar iyayenshi ya fara yi, kuma ya mata alƙawarin taimaka mata kowanne hali.
Shiya taimaka mata ya nemo mata lawyern dazai kare Shamsuddeen.
Har ana kwana gobe kwana ukun zai cika sun kasa samun wata hujja akan Abba ya kashe iyayen Sadeey, Kuma abinda yafi ɗaure musu kai da Shamsuddeen ya tabbatar musu da baida alaƙa da abinda ya samu momie, tohh wa keda Alhakin hakan?
Tana zaune taa zuba ma momie ido taayi tagumi, duk taa rame idan tana tuna halin da shamsuddeen yake ciki na wahala, gashi yau momie kwananta uku a asibiti har tau bata farfaɗo ba, ita kaɗaice zata iya bada Shaida akan abinda ya faru gashi rashin lafiya ko motsi batayi sai yanda akai da ita.
Wucewar Anwar ta hango daman tana son magana dashi, Ta ajiye wayarta kusa da momie ta tashi ta bishi bada saninta ba ta danne inda zatayi video screen short ɗin wayar, duk maganar da za'ayi zata fito ta fita.
Inda ta hango Anwar ta duba bainan, duk ta duba wuraren bata ganshi ba ta haƙura ta koma, Abin mamaki ta hango daya matuƙar firgitata.
Momie ce Zaune daram Kamar ba abinda ya taɓa damunta, suna ƙyalƙyalar dariyarsu ta mugunta ita da Abba, Maganganu suke cikin nishaɗi daga inda take bazata iya jiyo Abinda suke cewa ba, laɓewa tayi yanda bazasu hangota ba duk mamaki ya cika mata zuciyah, tohh me hakan ke nufi?
Wayarta ta nema ta kirawo yaya Anwar ta manta taa baro ta, cikin sa'a kuwa sai gashi yaa tafo bai lura da ita ba zai wuce ta jawoshi, Yace "Yadai Ƙanwata?" nuna mishi abinda idanunta suka ganar mata tayi, Shima yaa kaɗu da ganinsu, mamaki yaa hanasu su duka magana.
Dubara yayi ya zaro wayarshi ya musu hoto a haka, yace "Tabbas akwai wani ɓoyayyen Al'amari dan gane da wannan abin, dole ne inje in sanar da lawyern mu" tace "kayi sauri Ya Anwar, don wannan ba ƙaramar shaida bace" Yace "karki nuna musu kinsan komai ƙanwata, ki kula sosae nasara tana tare damu insha Allah" ta ɗaga mishi kai kawai.
Har yaa tafi cikin hanzari ta ƙwala mishi kira ya tsaya tace "Ya Anwar ngde sosae" Yace "karki damu ƙanwata, nasan zafin da kikeji a zuciyarki, duk da iyayenah ne, ni kaina naa tsanesu akan wannan halayyar" bata ce komi ba ya juya ya tafi.
Tana juyowa ta hango har Abban ya tafi, ta dai-daita kanta, sannan ta tafi ta koma ɗakin, Momie ta kwanta kamar yanda ta barta, kamar ba ita bace ta gama labari da daria harda shewa ba.
Wayarta ta duba charging ya kusan ƙarewa, ta kasheta kawai gaba ɗaya saboda bata taho da charger ba, ta ajiyeta kawai tana ci gaba da yima Shamsuddeen Addu'a a zuciyarta.
Washe gari Zaman kotu...
Anwar kawai yaje da Abba, sadeey kam zaman kotun ma ƙara mata damuwah yake, kuma tana saka ran da yardar Allah yau sune da nasara.
Duk wani hujja da Lawyern Shamsuddeen ya kawo kotu bata gamsu dashi ba, br ishaq ya dage sosae wurin ganin an hukunta shamsuddeen.
Ganin lawyern Shamsuddeen baida wani gamsasshiyar hujja ya saka Alƙari ya gamsu da cewa shamsuddeen shine ya kashe iyayen Sadeey, don hotan momie da Abba ma lawyern cewa yayi computer ne kawai ta haɗa.
Alƙari ya fara jawabin yanke ma Shamsuddeen hukunci....
Sadaukarwa Ga Sadeey S Adam
©Rabiatu Sk msh
0 comments:
Post a Comment