New Post

Sunday, 16 October 2016

ABDUL WAHAB 21

ABDUL WAHAB 21

©Rabiatu sk msh
           ®NWA

Kuka ne yaci 'karfin khadija, duk taa tada mishi hankali a rud'e yake cewa ki fad'amin mna, da'kyar ta iya bud'a baki tace "kayi ha'kuri Abdul aurena dakai bazai taba yiwuwa ba!

A rikice yace "me kike shirin fad'amin khadija? Idanma wasa kike ki daina plz wannan ba wasa bane, tace "ba wasa nake maka ba Abdul, ni kaina banda wani burin daya wuce zama matarka, soyayyatah taka ce, duk wani tsarin rayuwatah dakai na yishi, anma a yau komai ya rushemin sanadiyyar umarnin mahaifana, bazan iya bujire musus ba, sunyimin komi a duniyarnan, bazan iya 'kin kar'bar za'binsu ba, kayi ha'kuri ka fiddani a zuciyarka, Don Allah ka yafemun, kada ka zargeni da yaudararka.

Kasa furta komi yayi, da'kyar ya iya sauke wayar a kunnenshi, kamar ba namiji ba, Abdul ne na gani ya fara shesshe'kar kuka, tabbas wannan wata jarabawa ce ta ubangiji, ko kuma nace sakayya, yau d'innan gashi ya d'and'ani zafin da sadeey taji ba'aje ko ina ba cikin 'yan awannan, rabuwarshi da khadija akwai wata ishara da Allah yakeso ya nuna mishi.

Dafe 'kirjinshi yayi da hannu dai dai inda zuciyar take, saboda wani irin bugu da take mishi, 'kirjinshi naa mishi nauyi, mi'kewa yayi da'kyar ya 'karasa wurin fridge, robar ruwan swan ya d'auko mai sani 'karara, anan ya 'budeta ya fara kwankwad'a, sannan ya ciro yana kwarara ma kanshi, Abn nashi tsoro ya fara bani, ga tausayinshi da nakeji da sauri na fito na nufi gidansu sadeey.

Da gudu ta shiga babban falo tana 'kwala ma mami kira, hangota tayi tana safkowa daga upstairs ta ruga ta fad'a jikinta tana gunjin kuka, itama mami taaso tayi hawayen dauriya kawai take ta fara shafa kan sadeey tana rarrashinta.

Mami tace "kiyi ha'kuri sadeey don kin rasa abdul......, da sauri ta d'ago tana kallon maminta tace "Abinda yafi 'konamin zuciyah kenan mami, bazan iya cewa naa rasashi ba, don na tabbata zuciyatah bazata ta'ba rabuwa dashi ba, ina son yayanmu Mami, anma nafison inga farin cikinshi.

Mami ta shafi kanta tace "Allah ya yaye miki damuwarki dear, anma yana 'konamin zuciya ganinki cikin damuwah.

Share hawayenta tayi tace "karki damu mami, insha Allahu, daga yau farin ciki kawai zaki dinga gani a fuskata kamar yanda kika saba, duk da bazan iya mantawa dashi ba, naa mi'ki Alkawarin daina yawan tunaninshi, 'kara rungumeta tayi sannan ta juya ta nufi d'akinta.

Mami ta bita da kallo, hawayen datake kokawar maidawa ne saida suka zubo mata, tabi bayan sadeey da kallo, "tabbas babu wanda ya kaita fahimtar halinda 'yar tata take ciki, saboda bata da wata abokiyar shawara data wuceta, babu abnda take 'boye mata, tasan irin yanda sadeey keson Abdul.

Dedicated to Mr. Smiles😃

❤❤Rabiatu sk msh❤❤

Related Posts:

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts