ABDUL WAHAB 18
©Rabiatu sk msh
®NWA
Yana rufe bakinshi sadeey ta fara bud'e idanunta a hankali, kallon sama ta farayi a hankali ta fara kallon kowa a d'akin da sauri ta tashi zaune duk sun zuba mata idanu. Lokacin hajia taa dawo
Ita ta fara mata magana tace "sannu sadeey," tace "yauwah hajia, tana murmushin kauda damuwa, ko kallon inda Abdul yake batayi ba ta fara 'ko'korin miqewa da sauri fatyma ta ri'keta, ita ta taimaka mata suka koma d'akinsu don har lokacin ji take d'akin na juya mata.
Hajia batayi mata maganar ba sai da dare da bata fito cin abinci ba tana d'aki tana fama da kukan zuci, komi na duniya ya canja mata, soyayyar Abdul naa 'kara azalzalarta can zuciyarta.
Batasan shigowarta ba, sai dai taji an dafata, firgigit ta dawo daga tunanin da takeyi, ta tashi zaune da sauri ganin hajia ta shigo, hajia ta dafata tace "ki fad'amin gaskia sadeey, kada ki 'boyemun komi, miye dalilin daya sanyaki shock? Girgiza kai tayi tama rasa me zatace can kuma tace "ina shigowa d'akin yaya bansan yaabar kallo kunne ba, sai dai naji ana film din ban tsoro, na tsorata zan juya da gudu carpet ya zameni.
Hajia ta jinjina kai cikin tausayawa tace "kin tabbata gaskiya kika fadamun? Sadeey ta d'aga kai, hajia tace "Tohm shknan Allah ya kyauta ya kiyaye gaba, sadeey tace "Ameeyn".
Tun daga ranar sadeey ta fara janye jikinta daga Abdul, duk taayi sanyi magana ma bata cika yiba sai dai ta bada amsa dakai, cikin wata d'aya ta rame, fatyma naa matu'kar tausaya mata don ita kad'ai tasan damuwarta, don Abdul ma daina kulata yayi, daman abnda yafiso kenan.
Ita kad'ai ta zauna tana tunani, zaman gidansu Abdul duk yaa isheta bata da wani sukuni, tabbas ZAFIN SO baida magani, taa yarda bazata taba samun Abdul ba tunda ko kad'an yanzu bai bata kulawa.
Tashi tayi ta fara tattara kayanta, babu abinda ta bari nata, fatyma ta shigo tana kallonta cikin mamaki tace "matar yayanmu wannan kayan pa? Tana murmushi tace "bakisan maisu bane? Tace "kamar naki dai na gani, ina zuwa haka? Sadeey tace "inda na fito, kinga muje ki rakani d'akin hajia. Fatyma bata musa mata ba ta bita suka tafi, don taa matsu taji abnda sadeeyn zatace.
Hajiya naa waya suka shiga, sai data gama ta d'ago kanta tana kallon sadeey tace "harkin gama shryawa? Sadeey ta d'aga mata kai kanta na 'kasa, tace "shikenan sadeey, yanzu maminki ta kirani ta fad'amin kunyi waya kince yau zaki koma gida, yanzu idanma wani abun muka miki ni bazaki sameni ki fadamin ba? Dani da maminki duk dayane, idanma son ganinsu kike a gari daya pa kuke sadeey, ki fad'amun gaskiya idan wani abu ake miki da bakiso don na lura da canjawarki kwanannan.
Girgiza kai tayi tana hawaye, tace "Wlhy ba abunda kukamin hajia, nipa bawai zan koma gida bane, kawai zanjene bazan dade ba zan dawo. Hakanan hajia ta amsa anma a zuciyarta bata gamsu da abnda sadeey ta fada ba, duk da tasan bata da wani zurfin ciki, abnda ke ranta kawai take fad'a.
Dedicated to Mr. Smiles😃
❤❤Rabiatu sk msh❤❤
0 comments:
Post a Comment