ABDUL WAHAB 7
©Rabiatu SK msh
®NWA
Da sauri Abdul ya kashe wayarsa, duk ya tsure cikin duhu yake ma khady alamar ta taimaka mishi, tayi sauri ta danna wayarta tayi kamar ita aka kira,sadeey tace "A'a naji kamar k'arar wayar yayanah, "da sauri Khady ta juya, sannan ta girgiza kai, tace " no bakowa wayata ce tayi k'ara, "sannan sadeey, tace "ok. "ta juya ta tafi, tana tafiya Abdul yayi wata irin ajiyar zuciya, khady ta kwashe da dariya, tace " Ashe duk abinka kai matsoracine, tunda har kana tsoron mata. " Abdul ido kawai ya kora mata yana kallonta, kaasa ce nata komi kawai yayi, "Ashe dai yarinyarnan kyakkyawa ce? Gaskia taa iya murmushi, abinda yake fad'a a zuciyarsa kenan, itama daina dariyar kawai tayi ta tsaya tana kallonshi....
Cikin wata irin murya yayi magana Wanda shi kansa baisan yana da irin murya bah, yace "meyasa ki kayi karya dan ki kareni, ke kyakkyawa ce, karya baza tayi maki kyau bah. " itama cikin siririyar murya ta mai da masa amsa, Wanda saida yaji maganarta har cikin kwakwalwarsa har zuwa cikin zuciyarsa, da sauri ya lumshe idanuwansa, sannan ya bud'e a ahankali, tace " kaima baza kayi kyau da mai tsoron yan mata bah, da ina maka kallon jarumin namiji " gyaran muryar da akayi ne yadawo dasu hankalinsu, da sauyi suka juya Raheem ne da fatyma tsaye suna dariya, fatyma ta fara magana, tace " uhmm yau dai naa kama yayana yana soyayyah, "raheem yayi murmushi, yace "ai na gayawa abokina but yayi man gar'dama gashi yanzu. " Abdul ya d'aure fuska yana kallon fatyma yace "lallai yarinyarnan wasa nake dake? Ni ba soyayyah muke ba, ko soyayyah muke?
Rasa amsar da zata bashi tayi sai Raheem ne yace "ay ba iya soyayyar kake ba, don hka bzaka gane ba, anma ku duka kuna son junanku! Juyawa yayi yana kallon khadija ya sadda kanta a 'kasa, kafin yayi magana sadeey ta qaraso wurin ita da qawayenta. Inda abdul yake ta qarasa ta tsaya!
Ta dubeshi ta harde hannu a qirji tace "ina ka tafi yayana inata nemanka? Qawayenah duk sun qagara su ganka, kasan kuwa wahalan da nasha kafin in ganka?
Duk yaa rasa amsar dazai bata ma, tayi murmushi kawai ta kalli qawayenta tace "yau dai ga yayanah da naketa baku labari koma shine wanda zai aureni insha Allah, d'an uwanah ne, auren zumunci za'a mana, ya kukaga dacewarmu?. " da sauri khady takai dubanta ga Abdul......
*Dedicated* to Mr smiles😃
❤❤Rabiatu SK msh❤❤
0 comments:
Post a Comment