New Post

Thursday, 30 March 2017

MATATAH CE 58

♡MATATAH CE♡
   ♡♡♡♡♡♡
             58

©Rabiatu sk msh
      ®NWA
                   
            Labari....Ilileee

www.babymsh.blogspot.com

  Tafiya kawai suke babu wanda kema wani magana, duk a takure take, shikam ko a jikinshi kamar baisan tana a motan ba.
    Dai dai wurin wani babban wuri taga yayi parking da batasan ko ina bane, ya fita ya barta a motan, bai daɗe ba saiga wata kyakkyawar budurwa ta fito wurin tana ta karairaya tasha Makeup harya mata yawa.
   Tana daga ciki suke maganarsu har suka gama, sai dai ya buɗe mata yace ta fito, kallonsu dai kawai take, budurwan ta kalleshi tana wani lumshe ido.
   "zan maka waya idan an gama, don zai ɗauka lokaci gaskia"
  "ba komai, idan an gama inanan ina jira"
   "owk, muje ko Saude?" ta kalleta tana murmushi, maida kallonta tayi kan Najib duk a tsorace take, ya ɗaga mata kai, sannan ta juya ta bita.
     
      Hannunta ta sak'ala cikin nata, suka shiga wurin tana binta a baya sai da taga mata da yawa wurin hankalinta ya kwanta, wasu ana musu kitso, wasu gyaran gashi, wasu Make up, wasu gyaran fuska, kowa dai da abunda ake mata.
       Wurin mai gyaran jiki takai ta, wani ɗaki ana ma wata an kusan gama,
     "Aunty Nainah sannu da zuwa, keda kanki kuma?"
  Bata tsaya bata amsa ba tace "ko waye a layi, dakin gama wanda kikema ga sistatah, ki mata gyaran jiki mai kyau so nake idanna dawo bazan ganeta ba"
   "tohm shikenan Aunty an gama" Saude tana zaune kamar tayi tsalle don murna, duk ta matsu a gama itama ai mata, sai bin mutanen wurin take da kallo tana murmushi.

   Gyaran jiki, fata, k'afa, fuska, gashi, baki, wuya komai lungu da sak'o na jikinta babu wanda ba'a gyara ba, wata haɗaɗɗiyar doguwar rigane red colour, Aunty Nainah ta kawo mata, ta shiga ta saka, sannan aka mata Makeup, ita da kanta ta naɗa mata gyalen rigar, sannan taja hannunta,
    "Zo muje" tabi bayanta har gaban Mirror, tsayawa kawai tayi baki buɗe tana kallon kanta, wai itace nan a haka? Kamar wata jinsin larabawa masu masifan kyaunnan, ita kanta saida tayi k'ok'ari wurin gane kanta, Maganar da Yasseer ke faɗa mata kullum itace ta faɗo mata a rai.
     "Saude ke mai kyau ce" jin maganarshi kawai take a matsayin yabo, ko kuma yana faɗi don ya sakata farin ciki, inama ace yau yana tare da ita yaga yanda Saudenshi ta koma? Tsananta tunaninshi da tayi ne kawai hawaye suka fara zuba a idanunta.
  Aunty Nainah ce ta dafa kafaɗarta "Yadai Saude?" share hawayenta tayi duk da bata iya ɓoye damuwan dake fuskarta ba,
    "Ba komai Aunty, Na gode miki sosai"
   "Bani badai, Najib shiya biyamu kuɗaɗe da yawa donmu muki gyarannan, bansan yanda kuke dashi ba, anma Allah yasa yana da muhimmanci a gurinki kamar yanda kike wurinshi"
   Maganarta taa ɗaure mata kai, harma ta rasa me zata ce mata, hannunta ta sake rik'ewa.
   "Muje yana jiranki tun ɗazu" suka tafi har kusa da wurin ta rakata, sannan ta mata bankwana don tafiso ta k'arasa ita kaɗai.

   Shi kaɗai harya gaji da jira, anma bai nuna alaman k'osawa ba, ta daɗe a tsaye, bai buɗe ba hankalinshi ma sam bai kanta, ta saka hannu taɗan k'wank'wasa k'ofan, sauke glass ɗin yayi kaɗan, ya kalleta yana sauraren k'arin bayani.
   "Daman an gama ne" tace tana wasa da yatsun hannunta, ya taɓe baki donshi tsakaninshi da Allah bai ganeta ba.
    "an gama me?"
        "Aunty Nainah ce ta rakoni" sannan ya ɗaga kanshi yana kallonta sosai, donshi ko kallan mata bai cika yi ba, sai kuma ya ware ido bakinshi ɗauke da murmushi.
    "Saude??" ta saka hannu biyu ta rufe fuskanta tana daria, "Naam" ai saiya buɗe mota ya fito, hannu ya saka ya janye mata hannun data rufe fuska dashi, yana k'arema kyakkyawar fuskarta kallo.
   "I cant believe dis Saude kece kika koma haka?" dariya kawai take, ya ɗaura hannunshi saman kafaɗarta.
   "Kinyi kyau, kinyi kyau Saude, ke mai kyauce"
  Gabanta ne yayi mummunar faɗuwa, duk fara'ar da take ta kauce saboda k'ara tuna mata Yasseer da yayi, ta kalli kafaɗarta inda ya ɗaura hannunshi, ya ɗauka abunda ya ɓata mata rai kenan da saurinshi ya janye.
    "Meya faru kuma?"
      "ba komai" ta k'ak'aro murmushi, yace "Selfie?" yana ɗaga mata gira cikin wani irin salo mai burgewa.
  Batasan me yake nufi ba, sai dai ya janyo waya, kusa da ita ya tsaya anma bai taɓata ba, ya dinga musu pics masu kyau, sannan itama ya mata, mutane sai kallansu suke ba k'aramin burgewa sukai ba,

  Daganan wani k'aton boutique ya kaita, ya dinga jidar mata dogayen riguna masu kyau da masu wando, harda kayan barci duk wanda ya burgeshi ɗauka yake ya zuba kawai, kamar mai shirin buɗe kanti, kuɗi masu yawa taga ya zaro ya mik'a.
   Basu gama ba har dare yana yawo da ita, wuraren shak'atawa ya dinga kaita, sunsha yawo sosai, wani iri takejin ranar daban da sauran ranakun da tayi a baya, duk da ba wani magana suke a tsakaninsu ba, shi miskili ita kuma sarkin kunya, saima ta maida fuskarta gefe tana shak'ar sanyayyar iska da yake glass ɗin a sauke yake, wani irin farin ciki na k'ara shigarta, ga wani kiɗa mai taushi dake tashi.
   Kaɗan kaɗan zata waiwaya ta kalleshi, tanason mishi magana anma kunyarshi taa hana, hankalinshi gaba ɗaya yanakan tuk'i, shima wani irin nishaɗi yake ciki, wak'ar koredo bello ne yake bi a bakinshi kamar shine ya rairata, yana lura da duk wani motsinta.
    "Ina zamuje?" ta tambayeshi cikin fargaba, batasanma yaji ba saida ya bata amsa,
   "Gida, ko akwai inda kikeson zuwa?"
  Ta k'ara k'asa da kanta tana wasa da hannunta, kallonta yake anma tak'i magana.
   "kinyi shiru, karki goge zanen lallen mana"
  Da sauri ta ɓoye hannunta tana dariya, "Daman..." kuma sai tayi shiru.
    "ehen..."
       "Zamuje gidan Aunty Husna?"
   "Me zakiyo?"
       "ba komai"
Ya duk'o da kanshi yana kallon fuskarta,
    "zaki nuna mata kwalliyar ne?" ta girgiza kai duk ta takure jikin k'ofa, shi kuma ya wani shige mata.
   "eeh mana kedai faɗamun" wani irin zaro ido tayi tana nuna mishi gabanshi,
     "Gabanka yaya Najib" da sauri ya koma kan tuk'unshi baiga komai ba, ya kalleta sai dariya take mishi.
   Ya ɓata rai "kekoh" itama duk saita marairaice fuska ta ɗauka haushi yaji.
      "yi hak'uri"
   Sai sannan shima ya fara dariya sosae, "kinfi kyau a haka" kallonshi kawai take.
 
   Mutum mai faɗa da birkitaccen hali idan baka fahimceshi ba, anma mai sauk'in kai da son mutane, ga wanda suka zauna dashi, ya iya zama da mutane sosae ba tare da yaa ɓata musu ba, matsalanshi kawai kar a mishi katsalandan.
   Sanda suka isa gidan har Momie ta dawo tana shirin kwanciya, suka shiga ɗakin da kaya niki-niki, ba k'aramin daɗi taji ganin Saude a haka ba, ta dinga saka musu albarka, ita da kanta ta dinga mishi godia, ta mishi addu'ah sosae.
  Shiya ɗaukarma Saude kayan har ɗakinta, tana tsaye jikin madubi don bata gajia da kallon kanta, sai murmushi take ita kaɗai, daga bayanta ya tsaya tana kallonshi ta cikin madubin, sai kuma taji kunya da sauri ta rufe idanunta.
   Saitin kunnanta yake mata magana "bansan me nake tunani ba Saude, anma yau ranace ta musanman a gareni, naji daɗin kasancewarki cikin farin ciki" yasan bazatayi magana ba, yana gama faɗa ya fita sannan ta buɗe idanunta,
    "Nagode sosai ta sabuwar rayuwarnan daka bani Yaya Najib" ta faɗa kamar yanajinta, bayan taji fitarshi

©Rabiatu sk msh

Related Posts:

  • MATATAH CE 36-40♡MATATAH CE♡    ♡♡♡♡♡♡            36-40 ©Rabiatu sk msh       ®NWA   &nb… Read More
  • MATATAH CE 26-30♡MATATAH CE♡    ♡♡♡♡♡♡           26-30 ©Rabiatu sk msh       ®NWA    &nb… Read More
  • MATATAH CE 31-35♡MATATAH CE♡    ♡♡♡♡♡♡            31-35 ©Rabiatu sk msh       ®NWA   &nb… Read More
  • MATATAH CE 36-40♡MATATAH CE♡    ♡♡♡♡♡♡            36-40 ©Rabiatu sk msh       ®NWA   &nb… Read More
  • MATATAH CE 41-45♡MATATAH CE♡    ♡♡♡♡♡♡            41-45 ©Rabiatu sk msh       ®NWA   &nb… Read More

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts