New Post

Sunday, 12 March 2017

MATATAH CE 55

♡MATATAH CE♡
   ♡♡♡♡♡♡
             55

©Rabiatu sk msh
      ®NWA
                   
            Labari....Ilileee

www.babymsh.blogspot.com

    Tunda ya fara magana a waya ta zuba mishi manyan idanunta tana kallonshi ko k'iftawa batayi, maganarshi cikin nutsuwa hankali kwance yake fitar da ita ɗaya bayan ɗaya, yana cikin magana ya ɗago yaga shi take kallo, wani  banzan kallo ya watsa mata, batasan ma yanayi ba, saida ya gama wayan har zai mata magana ya fasa, sai dai yaja dogon tsoki, aikam da sauri ta dawo hankalinta, bata tsaya ganin kallon da yake watsa mata ba tabar wurin.
   Abinda ta lura ga Najib (Daddy) baison yawan magana, kuma bai cikason a shiga harkarshi ba, ita kaɗai ke zancen zuci harta isa amsa kiran Momie.
   Bayan ta duk'a har k'asa tace "Gani Momie"
    "Yauwah ki shirya yanzu Daddy zai ajjeki gidan Husna, yanzu taimun waya batajin daɗi kiɗan rage mata ayyukan gidan"
   "tohh Momie" ta tashi zata tafi Momie ta fara magana, "itama dai Husna, tak'i yarda a ɗaukar mata er aiki, yanzu aida taa samu maiyi mata gyaran gidan" Saude ta fita ta barta tana faɗa, daman Momie tana bata labarin Husna itace er Autar ta tana bima Najib (Daddy) shine na biyu, sai kuma babban yayansu yana Moscow shida Matarshi, yaranta uku daman.

    Kayan jikinta mayafi kawai ta ɗaura akai, sannan ta dawo ta faɗama Momie taa shirya, ba k'aramin ɓata rai yayi ba da Momie tace ya kaita gidan Husna kawai don bazai iya mata musu bane, wani irin kallo yakai mata sannan ya kalli zanin data ɗage can sama (alaman ta saukeshi) donshi yafi aika sak'o da kallo bai cikason magana ba, bata gane mai yake nufi ba, sai tayi saurin kauda kai.
    "A haka zaki fita da wannan zanin?" ɗaga kai tayi bata fahimceshi ba,
   "da Allah saukeshi nace" da sauri ta saukeshi, anma still dai saman ciki, kaɗa kai kawai yayi ya wuce gaba ta bishi, yau ne fitarta ta farko harabar, sai kalle kalle take daman an fiddo mishi da mota a wanke sai k'yalli take, ya buɗe ya shiga ya barta tsaye, taa rasa inda zata shiga, batasanma yanda zata buɗe ba,
   Tsoki ya k'ara ja saboda yanda take ɓata mishi lokaci, daga ciki ya buɗe mata, da sauri ta tafi ta shiga, ta zauna kamar mai koyon zama, wani sak'on ya k'ara aika mata da kallo, anma duk bata gane ba, sai ta k'ara gyara zama ta rirrik'e kujerar data zauna a gaba,
     "Motar ma nizan rufe miki?"
   "yi hak'uri" sannan ta saka motar ta jawo motar a hankali ta rufe kamar tana tsoran karta ɓalle,
    "bata rufu ba" yace da ita, ta k'ara sanya hannu ta jawota, girgiza kai yayi sai magana take sakashi, "matsanan" ta kwanta sosae jikin kujerar, yakai hannu zai rufe duk da haka saida ya taɓa jikinta, da sauri ya ɗauke hannunshi saboda wani yanayi daya ziyarceshi,
Itama wani abune ya ratsa mata har tsakiyar kanta, ba shine na farko da ba, anma bata taɓajin yanayin da taji yanzu ba, kodan an kwana biyu ba Yasseer😉.

    Gidan da suka fara zuwa da baba Haja nemar mata aiki taga an buɗe mishi ya shiga da motan, gani yayi sai kokawar buɗewa take, ya shareta kawai ya fita ya barta, a ranshi yace 'sai dai ki kwana a ciki ni ba ɗan buɗe miki k'ofa bane' kamar tayi kuka haka ta dinga kiciniyar buɗewa duk ta haɗa zufa ko ina a rufe, sai mai ban ruwan fulawane ya buɗe mata ta fito tana maida numfashi, ta mishi godia sannan ta shiga gidan, da yake tasan hanya.
     Zaune ta iskeshi suna fira da dariya kamar ba shi ba, Husna ta kalleta tanaso ta tuna, ta nunata da hannu "kece Saude?" da sauri ta ɗaga kai,
    "Allah sarki, kamar kece kukazo da baba Haja darennan ko?"
    "eeh nice"
  "Anma dai naji daɗin kasancewarki gaban Momie, kiyi hak'uri da wannan ranar kinji"
   "ba komai fa"
      "Yauwah" sannan suka gaisa, ta mik'e sukaje tana nuna mata abubuwan da zatayi, share-share ne kawai da goge-goge, tana fita taci gaba da aiki, shima tun shigarsu ya tashi yabar gidan.

    Sai dare ta gama mata dukkan ayyukanta, ta haɗo mata mayuka masu kyau na gyaran jiki dana kai, da turaruka masu k'amshi ta bata, Saude ta amsa tana ta mata godia.
     "haba banson godiyarnan Saude, ai mun zama ɗaya"
   "Tohh Aunty Allah ya saka da Alkhairi"
   "Ameen" sai kuma ta kalleta,
   "Saude kenan, gaki a birni anma har yanzu k'yauye tak'i barinki"
        "Ban gane ba Aunty husna"
   "gani nayi har yanzu shigarki nanan ta k'yauye, baki ganin yanda en matan birni keyi? Ki canja shigarnan kinji" ɗaga mata kai tayi har lokacin bata dai fahimtan ba, driver aka saka ya kaita har gida.
    A harabar gidan ta iske motan da suka fita da ita tare da Najib, an bubbuɗeta da alamar wanketa akayi, ta zagayeta ta wuce cikin gidan kai tsaye ɗakin momie ta shiga, muryarta ta jiyo da alama faɗa take,
   "Yanzu saboda kaa ɗauka k'anwarka a mota ne kake wanketa Daddy?"
   "nifa momie wallahi da gaske ta ɓatamun mota, ni kunyama nayita ji kar wanda ya sanni a ganni da ita cikin motah"
   "Hinyehh! Ai da cemun kayi bazakaje da ita ba kawai, sai insan yanzu kaa daina jin maganata"
   "kiyi hak'uri Momie"
Saida ta share hawayenta sannan tayi sallama cikin ɗakin momie duk yanayinta ya canja, tunda take bata taɓajin zafin kasancewarta er k'auye ba irin yau.
   Momie ta nemo fara'a tanajin sallamar Saude "Sannunki da dawowa"
    "yauwah momie Sannu da gida" ta zube mata kayan da Husna ta bata a gado,
   "Gashi ta bani, tace a gaishe dake"
  "Ina amsawa, an gode ma Auntynki Husna, naa gani ki adana"
  "tohh" ta tashi zata tafi, Momie duk bata yarda da yanayinta ba tace "kodai wani abu ta miki naga yanayinki yaa canja?"
    "A'ah Momie, Aunty tana da kirki sosae, er gajia ce kawai"
  Momie ta sauke ajiyar zuciya data tabbatar Saude bataji maganar su ba, tace "Sannu kinji, kije ki kwanta da wuri"
  Tace "tohm Momie"
Idanunta k'asa k'asa ta kalla inda Najib yake, yana rungume da Hafsat tayi barci a jikinshi.

  Washe gari saboda gajia taa daɗe bata tashi ba, sanda ta tashi Talatu harta kusan gama ayyukanta, ta kama mata dai suka k'arasa, duk sai taji ba daɗi kuma ta zauna bata aiki, ta shiga ɗakin Momie ta mata gyaran kaya, ta k'ara gyara ɗakin.
  Ɗakinta ta koma duk batason zaman hakanan, da marece kafin su fara girkin dare ta tashi ta fara zagaya gidan, hanyar ɗakin Najib tabi  hakanan taji tanaso taje taga inda ɗakin yake, cikin Sanɗa ta k'arasa cikin Sa'a kuwa a buɗe yake, ta dinga lek'en falon ba k'aramin kyau yayi ba, komai a tsare sai dai kuma ko ina yayi datti, bataga alamunshi a falonba, hakan ya bata k'warin gwiwar shiga bedroom ɗin shima ta labule ta lek'a anma bataga alamunshi ba, shima duk yayi kaca-kaca kamar ba mutum ke zama a ciki ba, saida ta tabbatar bai cikin gidan sannan ta gyara shirinta ta fara aiki, gyaran ɗakin ta shigayi ko ina take kakkaɓewa tana kauda kayayyaki.
   Cikin lokaci kaɗan ta gama gyaran ɗakin, ko ina yayi fes yayi kyau fiye da daa, har zanin gadon ta cire ta canja mishi wani, toilet ɗinshi ma ta wanke mar duk da baiyi wani datti ba, ta saka turaren wuta mai k'amshi ta turare ko ina. Ita kaɗai ta tsaya tana kallon ɗakin, ita ma kanta yaa burgeta sosai, yanzu momie zata daina damuwa da dattin ɗakin Najib, ta faɗa a zuciyarta.
  A hanzarce ta gama ta fito, a hanyar da zata fiddata gaba ɗaya bangaren nashi ta haɗu dashi yana niyyar shiga, a ruɗe ta k'ara sauri tabar wurin, binta yayi da kallo kamar ya mata magana kuma ya fasa, ya wuce ɗakinshi.

©Rabiatu sk msh

Related Posts:

  • HAKKIN KISA 21-25☠HAK'K'IN KISA☠       👽👽👽👽            21-25 ©Rabiatu sk msh       ®NWA … Read More
  • HAKKIN KISA 1-5☠HAK'K'IN KISA☠       👽👽👽👽               1-5 ©Rabiatu sk msh     &… Read More
  • HAKKIN KISA 6-10☠HAK'K'IN KISA☠       👽👽👽👽               6-10 ©Rabiatu sk msh     … Read More
  • HAKKIN KISA 11-15☠HAK'K'IN KISA☠       👽👽👽👽               11-15 ©Rabiatu sk msh     … Read More
  • HAKKIN KISA 16-20☠HAK'K'IN KISA☠       👽👽👽👽             16-20 ©Rabiatu sk msh       … Read More

4 comments:

  1. Enter your comment...jinjina gareki

    ReplyDelete
  2. "I like this post,And I guess that they having fun to read this post,they shall take a good site to make a information,thanks for sharing it to me.
    Read more here:
    kim kardashian sex tape
    porn sex video hd
    mia khalifa sex video
    sunny leone sexy movie"

    ReplyDelete
  3. To boost your appetite and reduce the hunger craving there are tons of supplements available
    today but among them one source works great that is named as Pro Keto X, which leads to burn
    stubborn fat presence from the body and gives a slim and stylish waistline
    Keto Pro X

    ReplyDelete
  4. Why worry with the weight loss factors when there is one of the best weight loss supplement
    available in the market that is named as teal farms keto and works to remove bad cholesterol
    and boost the metabolic rate of the bodyto deliver controlled weight gain and burn unwanted
    calories naturally Teal Farms Keto

    ReplyDelete

Popular Posts