♡MATATAH CE♡
♡♡♡♡♡♡
71
©Rabiatu sk msh
®NWA
Labari....Ilileee
🙋🏻kuyi hak'uri dani Masoyah, naga k'orafinku, kuma naji daɗi da gyaran da kukamun, kunsan dai ɗan adam ajizine, babu wanda yafi k'arfin kuskure, gaba ɗaya na manta na saka Saude bata gane Yasseer, wasu na cewa ya kamata ta ganeshi tunda ita a ɗan birninshi ta sanshi, maganar gaskia daman Saude bata ganeshi ba, ita da tazo Abuja ma taa canja ballantana shi daya bar k'asar, ga matarshi Rabi'ah dake kula dashi😉 kuma idan baku manta ba Saude ma tana yarinya a lokacin daya tafi ya barta, Nagode sosai da tunatarwar da kukamun, wallahi naji daɗi sosae, don Allah ko a gaba kuka k'aracin karo da wani gyaran ina maraba dashi, Nagode sosai Masoyah, Allah yabar k'auna, LYSM😍
www.babymsh.blogspot.com
Gabantane ya shiga faɗuwa, har wani kyarma take k'afafunta suka kasa ɗaukanta, tana shirin faɗuwa ya tafi zai rik'ota, ta kauce kawai ta juya zata tafi.
Zata ita manta kamanninshi, zata iya manta sautin muryanshi, da duk wani abu nashi anma bazata iya manta ɗumin jikinshi ba, bazata iya manta yanayin da takeji a duk sanda jikinta da nashi suka haɗu ba.
Tana shirin tafiya ya rik'o hannunta, ta juyo suka haɗa ido, zuciyarta ce ke cewa A'ah Saudat, don yana da yanayin mijinki da kuma sunanshi ba lallai ne ya zama Yasseer ɗinki ba, kima fiddarai da sake ganinshi a rayuwanki.
Bata taɓa tsayawa ta k'are mishi kallo ba, Yayan Najib farine sosai, yafi Najib tsayi da cikar jiki, ga wani irin k'warjini da yake tare dashi, duk da ko ranshi a ɓace yake ka kalleshi kamar yana murmushi, saɓanin Najib da ko murmushin tsadane dashi, yafi Najib sakin jiki da fira da mutane. Kyakkyawane na k'arshe harta kasa gane shida Najib wanne yafi.
Ji yake kamar ya fito fili ya faɗa mata abun dake zuciyarshi, anma ya kasa koda buɗe bakinshi, idon yana kallonta ganinta yake kamar Saudenshi sai dai ya kasa yarda da zuciyarshi, mezai kawo Saude Abuja kuma gidansu? Kawai dai wata soyayyar ce Allah ya k'addaroma zuciyarshi, a hankali ya saki hannunta, kamar wacce take jira da gudu tabar ɗakin.
Fitar da basuyi ba kenan. Ranar bata samu halartar partyn da Abokan Najib suka haɗa mishi ba, don gaba ɗaya ji takeyi babu abinda zata iyayi, saima ta fake da ciwon cikinta.
Washe gari Momie tayi Mother's day, har ranar Saude bata fitowa ko k'ofan ɗakinta, wani tunanin Yasseer ne yake dawo mata sabo, ta rasa gane tsanarshi ne, haushinshi, ko kuma soyayyarsa, ga wani salon da Yayan Najib kezo mata dashi.
Kowanne ɓangarori anata hidiman biki, su gwaggo ma ana k'yauye anata shagali sai ranar ɗaurin aure zasuzo, Najib ma duk ya damu na daina ganin Saude sai dai suyi waya, anma inya tuna ta kusan zama tashi ma gaba ɗaya sai hankalinshi ya kwanta.
Ranar ɗaurin aure.
Tunda safe da sak'on Najib ta farka.
"Yau burina zai cika na samunki, na tabbatar babu sauran wani garkuwa yanzu tsakanina dake, ke tawace, ni naki ne, ina sonki Masoyiyah"
Murmushi tayi bata maida mishi ba saita kirashi, don a halin yanzu tafiso ta saurari muryarshi fiye da komai, "Masoyi an kusa zama Ango"
"nama zama dai, waɗannan awoyinma duk zasu shuɗene bayan sun sadani da farin cikina"
"Me kakeyi yanzu?"
"tafiya nake"
"Ango daman yana yawo?"
"tohh yana iya tunda kina guduna?"
"hhm" knockn k'ofanta taji anayi, ta sauka tana saka hijabi.
"ana miki knockn fa"
"Gashi zan buɗe"
Tana buɗewa sukai ido huɗu dashi, suka sakar ma juna murmushi, "Yadai?"
"Amaryatah nazo gani" ta tsaya jikin k'ofan bata bashi hanya ba sai so yake ya shiga.
"ko ba'a maraba dani in koma?"
"bak'in naka ka baro ka fito?"
"eeh mana tunda ina son ganinki"
Ya wuce ta ya zauna ɗaya daga cikin kujerun ɗakin.
Dai dai lokacin Yasseer na can ɗakinsu ya rasa meke mishi daɗi, tunanin ta yanda zai dakatar da auren kawai yake, ga wani sabuwar rigimar da Rabi'ah ta ɓullo da ita, ciki ne da ita taa rantse mishi bazata haife ba, ita bata shirya haihuwa yanzu ba, dukiyarshi ma gaba ɗaya ya mata alk'awari akan ta haife mishi ɗanshi anma tak'i jin lallashi, ga damuwan zai rasa Saudat kuma.
Meya kamata yayi? Yana kwance shi kaɗai yasan azabar da yakeji a jikinshi, yaje juyawa yaci karo da wayar Najib ɗayar daya bari, harya maida zai ajje ya hango hotanshi da Saude mak'ale a wallpaper, su duka suna dariya, wani irin daɗi yaji yana kallonta a hotan, gaba ɗaya kewanta yakeji, tunawa yayi da hotunanta da Najib ya taɓa cewa zai nuna mishi, ya shiga dubasu ba wahala sai gashi ya gansu, ya shiga yana dubawa babu wanda baiyi kyau ba, harya jawo wayanshi zai fara turawa yaci karo da wanda Najib yayi mata a tana er k'auye, wani irin zabura yayi ya tashi zaune.
Zazzafan zazzaɓine a jikinshi, anma ji yayi lokaci ɗaya kamar an yaye mishi shi, "Saude? Lallai kuwa biri yayi kama da mutum, babu tantama wannan ce Saudenshi" wata zuciyar tace 'anma mezai kawo Saude anan? Wannan sunanta Saudat kuma matar da k'aninshi zai aura! Mezai kai Saude yin aure saman aure? Anma kuma ai ance daga k'auye tazo, gani yayi kamar yana ɓatama ma kanshi lokaci, ya diro da niyyar zuwa ya tambaya Momie, don ta bashi tabbacin abinda zuciyarshi take zargi.
Cikin farin ciki yake tafiya kamar wanda akama bushara da gidan Aljannah, anan ya wuce abokan Najib en ɗaurin aure, ya wuce can cikin gida, duk taron matan da kema momie hidima da bak'in dake zuwa idonshi rufe ya shiga yana tambayar Momie, dak'yar ya ganota, ya jawo hannunta cikin zumuɗi, "Momie kizo kiji don Allah"
"Meye zanji? Kai har yau kamar k'aramun yaro, bakaga abunda nake ba?"
"plz Momie maganar nada muhimmanci ne, don Allah kizo kiji"
"Ya zanyi da bak'in dake zuwa? Kasan en ɗaurin aurema duk yanzu zasuzo, kaje ka shirya mana"
Rik'o hannunta yayi duk ya shagwaɓe kaman shine Autan "kizo kiji Momie bazaki daɗe ba"
Can ya jata ɗakin da babu kowa ciki, "ki zauna kiji don Allah Momie" ta ɗanji daɗi da taga ya fara sakewa, k'ila damuwar tashice ya tashi faɗa mata, ta zauna tana saurarenshi anma duk hankalinta ya tafi ga hidimarta data baro.
"Momie don Allah ki faɗamun ina aka samo matarnan da Najib zai aura?"
"lafiyanka kuwa? Wai menene matsalanka da aurennan?"
"zan faɗa miki Momie, wallahi zan faɗa miki ko menene damuwatah, anma ki fara faɗamun Momie" tayi shiru tana ɗan tunani,
"Don Allah Momie ki faɗamun" ganin yanda yaketa gamata da Allah ya sanyata fara bashi labarin Saude kamar yanda baba Haja ta faɗa mata, komai bata rage ba harda cewa mijinta ya rasu da kuma er da tazo da ita.
Cikin farin ciki yake tambayarta shekaran Hafsat nawa sanda sukazo? Ta faɗa mishi harma da sunanta na daa Saude, kamar ya fasa ihu don daɗi yadai daure yace "Momie ya sunan mijin nata?"
"Yasseer" ai baisan sanda ya k'ank'ame Momie ba yana murna, ya saketa ya duk'a har k'asa yayi sujjada, "Alhamdulillahi" kawai bakinshi ke furtawa, tsananin murna ma ya hanashi cewa komi sai dai yaci gaba da zagaye ɗakin.
Kallonshi kawai Momie keyi kaman wani zautacce, saida ya gama murnarshi take kallonshi baki buɗe, ya dawo kusa da k'afafun Momie ya zauna, "Momie ta tabbata dai Saude MATATAH CE, wallahi MATATAH CE dana biya sadaki aka ɗaura mana aure"
Sai yanzu ta ida tsorata da Al'amarinshi, gaba ɗaya kamar k'walwarshi ta taɓu take kallonshi, tausayinshi takeji, kodai damuwar tashi ce ta fara rikita shi?
"Matar k'aninka fa ce da za'a ɗaura musu aure yanzu ba daɗewa kake ik'irarin cewa matar kace, ba tun yanzu na gane take-taken ka ba, tun wuri ka fita idona karma ka ɗaga maganar nan wani yaji, wannan ai hanyar da zaka haddasa rigima ne tsakaninka da ɗan uwanka"
"wallahi Momie da gaske nake, Saudat MATATAH CE, nine mijinta Yasseer, na kasa faɗa muku ne don bansan yanda zaku ɗauka maganar ba, anma k'auyensu ne nayi bautan k'asa kuma a can aka bani aurenta"
"k'arya kake mijinta ya rasu, ka rabani da shirmennan naka ka bani hanya in wuce, sai dai in daman akwai wani abun a ranka"
Kamar yayi hawaye yake rok'on Momie, "Don Allah Momie karki yanke hukunci a rashin sani, wannan auren wallahi gaba ɗaya bai halarta ba, nine mijinta kuma gani a raye, ki yarda dani aurene za'a ɗaura saman aure"
Ita dai Momie ko maganganunshi bata fahimta, gaba ɗaya a tsorace take dashi, kallon marar lafiya take mishi, "Momie ki kirata ki tambayeta, zata faɗa miki gaskia da bakinta, idan harta musa na yarda ba Matatah bace"
"kana cikin hankalinka kuwa? Tun wuri ka dawo da tunaninka, Matar k'anenka ce fa, idan har taji maganar nanma ai girmanka zai faɗi a idanunta, na faɗa maka ka daina maganar nan ko?" ta wuceshi zata tafi.
Ya buɗa baki yanda zata jiyoshi, "Momie kinamun kallon mahaukaci ko" wallahi gaskiyatah nake faɗa, don Allah ki saurareni Momie, ina cikin hankalina" tsayawa tayi.
"ki aika aka kira miki ita, idanta k'aryata abunda na faɗa na yarda da duk wani hukunci da zaku yankemun"
Jikinta duk yayi sanyi da maganganunshi, ta dawo ta zauna, yananan zaune ta buga waya, sannan ya sauke ajiyar zuciyah.
Najib na ɗakin Saudat Abokan wasanshi sun sanyasu gaba suna tsokanarshi, yama kasa hak'urin akai mishi ita zaizo ya mata zaune ko shirin ɗaurin auren bazai tafi yayi ba, shine ma mai k'ok'arin maida musu, don dagashi har ita babu mai yawan magana cikinsu, kiran Momie ne ya fiddasu wurin ya tafi ya rakata. Tsayawa tayi kafin su shiga ɗakin.
"ka jirani karka biyoni kaji me Momiena zata cemun"
"kina da sirrin daya fini ne? Ai duk wani sirrinki nawa ne, don haka daga yanzu duk inda kika sanya k'afarki ina tare dake, bazan taɓa barinki ba"
"Gaskia na more miji dake matuk'ar k'aunatah, kaine sirrina Ya Najib, idanna zama matarka dukkan wani burina ya gama cika"
Maganan Momie sukaji, "Saudat ce anan?"
Da sauri ta shiga, "eeh Momie gani", "keda waye?" sai gashi shima ya shiga.
Sai lokacin suka kula da Yasseer da yayi zaman dirshan a gaban Momie, gaba ɗaya itama yanayinta ya canja, tayi niyyar korar Najib don bai kamata ayi maganar gabanshi ba, sai kuma taga ai shima ɗan uwane,
Cikin hikima don kar Saude tayi saurin gano yanayin da suke ciki tace "kince mijinki ya rasu ko?" Saude ta ɗaga kai ita mai gaskiyarnan,
Momie ta nuna Yasseer, sannan take kallon Saude cikin ido "wannan fa kin sanshi? Ki faɗamun miye tsakaninki dashi" k'walalo ido tayi tana kallon Yasseer, gaba ɗaya hankalinta ya tashi, cikin sark'ewar murya tace "Ya Yasseer, anan gidan na sanshi"
Najib yace " Meke faruwane Momie? Wacce irin magana ce wannan?"
Hannu ta ɗaga mishi alamun dakatarwa, "ki faɗamun gaskia" ta ɗaga kai tana kallon Yasseer, ita tsakaninta da Allah a farko gaskia ta faɗa, toh me Momie ke nufi?
Yasseer ne ya katse mata tunani, sai dai ta ganshi kawai a gabanta,
"ki faɗi gaskia Saude, ki faɗa musu ke MATATAH CE, nine Yasseer mijinki, nasan laifin dana miki fiye da mutuwa saiki ɗaura mun, ki faɗa musu gaskiya, ki faɗa musu mijinki ba mutuwa yayi ba"
Najib ne ya tureshi daga gabanta cikin hucin zuciyah yace "wannan wane irin abune kakeyi bruhh? Karma ka soma, Saudat MATATAH CE, kuma munan bamusan da wani maganar aurenka ba"
Momie ce ta mishi tsawa, yayi shiru anma sai huci yake.
"Saude kiyi magana don Allah, karki bari ku aikata HARAMTACCEN ZAMA, nine Yasseer naki wanda naje bautan k'asa k'auyenku aka bani aurenki, wallahi nasha wahala nemanki, don Allah ki buɗa baki ki faɗa musu gaskia, kada laifin dana miki ya kaiki aikata zunubi, ni mai laifine, ki hukuntani da duk hukuncin da zaisa kiji sauk'i a zuciyarki, anma karki aikata saɓon ubangiji, karki bari a ɗaura aurennan, don har yanzu ke MATATAH CE!"
"Ya isa haka" momie ta dakatar dashi, sannan ta kalla Saude, "ki faɗamun tsakaninki da Allah mijinki yana raye, Yasseer ɗana shine mijinki?"
©Rabiatu sk msh
0 comments:
Post a Comment