♡MATATAH CE♡
♡♡♡♡♡♡
36-40
©Rabiatu sk msh
®NWA
Labari....Ilileee
www.babymsh.blogspot.com
Duk ya ruɗe ya rasa yanda zaiyi da ita, sai girgiza jikinta yake yana cewa "tashi Saude, na daina fa" ita kam kukanma ya daina zuwa,
Sai can ya tuna da ruwan zafi fa ake shiga a wanke jiki, da sauri ya tafi ya duba babu ko wanda babu sanyi sosai, haka ya ɗaura ruwa cikin darennan, ya haɗa sannan ya ɗauketa ya shiga kewayen da ita, bayan ya gasa mata ko ina, har wankan soso ya mata ya wanketa tass, sannan ya taimaka mata tayi wankan tsarki, ya fito da ita ya kwantar da ita saman katifa, tana kwanciya sai barci,
Washe gari cikin nishaɗi ya farka, sai yau ma yake jinshi kamar Angon, sai wani annuri yake fita a fuskarshi, bai tasheta daga barcin da take ba, shiya haɗa mata break fast, da duk abunda zata buk'ata ya ajiye mata, yakai hannu ya shafi fuskarta, zazzaɓi harya sauko mata, gashi baison ya tasheta, ya ajje mata magani inda zata gani sanda zai fita, har yakai k'ofa yana waiwayenta, taa k'ara yi mishi kyau sosae, don dolene kawai zaije wurin aikinnan, anma idan sonshi ne ya zauna kawai yayi jiyyarta.
Tana jin yaa fita ta buɗa idonta, daman taa daɗe da farkawa kunyarshi ce ta hanata buɗa ido, ga yunwa tanaji anma bazata iya cin abinci ba, maganin daya aje mata ta gani, ta ɗauka tasha, sannan tayi kwanciyarta.
Duk da babu inda ke mata daɗi a jikinta, haka ta tashi da taga rana tayi, ta ɗaura mishi girki, tun kafin ta gama ta fara jin k'arfin jikinta, sai dai zafinda bata daina ji ba, tana gamawa sai gashi, yau da wuri yazo, tana gyara inda tayi girki, baima kula da ita ba saida ta amsa sallamarshi.
Ya juya yana kallonta abun mamakin Saude bai k'arewa, sai kallonta yake yace "Saude maiya fito dake kuma?" da sauri ta bar abunda take, a inda take ta durk'usa tana kallon k'asa,
"Sannu da dawowa"
"Yauwah ya gida" a can ciki ta amsa, duk ta takura da kallon da yake mata,
"Bana hana yawan aikinnan ba Saude? Keda bakijin daɗi ai kamata yayi ki kwanta ki huta"
"Ai naji sauk'i"
"Ban yarda ba, ki ajje aikinnan muje ki huta" tace "tohh" ta mik'e tana sauri ta k'arasa aikin, zuwa yayi ya kamo hannunta ta mik'e tsaya, yana rik'e da ita har cikin ɗakin, sai k'asa take dakai, kamar k'asa ta buɗe ta shige kawai, wani irin kunyarshi takeji,
Saida ya Zaunar da ita, sannan ya buɗe laidar daya shigo da ita, fresh milk ne da naman balango mai zafi sai k'amshi yake,
"Ki zauna kici, naga bakiyi break fast ba, zan tashi in watsa ruwa kinji"
"tohh abincin fa?"
"a ina aka samu?"
"Girkawa nayi,"
Rasa me mezaice mata yayi, "yanzu dai a k'oshe nake, k'ila anjima" ta gyaɗa kai, yana fita ta fara cin namanta, saida taci sosae har taji ba wuri, sannan ta kora da fresh milk ɗinta.
Ba laifi Saude ta samu kulawa daga wurin Yasseer a ranar, duk da bai wani san yanda zai tarairayeta ba, yana zaune gida, anma sai yawan yi mishi waya ake, duk dai maganar tafiyarshi ce,
Tun cikin dare yake haɗa kayanshi, ita dai har tayi barci bai kwanta ba, duk ta shiga damuwa, batason ya tafi ya barta, ita da tanada damar hanashi ma bazata bari yayi tafiyar ba, sai dai kawai k'ok'arin dannewa da take,
Da asuba bayan tayi Sallah ta kwanta, tana jiyoshi ya dawo daga masallaci toilet ya shiga yayo wanka sannan ya shigo ɗakin, tana jinshi yana shiri, saida ya gama ya fara tashinta, ta buɗe ido kamar mai barci,
"Yi hak'uri naa tasheki, yanzu zan wucene"
Batasan sanda tace "tun yanzu?"
Tsadajjen murmushinshi ya sakar mata, "Tohh ai garinmu ne da nisa, shiyasa zan tafi yanzu k'ila in isa kafin magrib"
"Tohh Allah ya yarda"
"Ameen"
Ta mik'e zata ɗaukar mishi jakar kayanshi ta rakashi, ya kama mata suka fito har soro, har lokacin gari da sauran duhunshi,
Suna tsaye sai wasa take da yatsun hannunta, ya sunkuyo dai dai fuskarta, ta lumshe ido, "Yadai?"
Idanunta a rufe tace "ni bansan mezan baka bane, idan ka tafi ka ringa tunawa dani"
"Saude kenan, tafiyar kwana biyun? Ai abinda kika bani ma ya isa har k'arshen rayuwatah bazan manta dake ba" da sauri ta juya jikin bangon tana ɓoye fuskarta,
"tohm baka faɗamun sunan garinku ba"
Cikin wasa yace, "tsoro kikeji kar in gudu in barki?"
"A'ah inason sani kawai" ta faɗa tana dariya,
Har yanzu cikin zolaya yake mata magana "A k'asar katsina nake"
"Uhmn nasan ai ba jaharmu ɗaya ba"
"Hakane fa, garinmu yana can hanyar wani gari, idan anje kusa da wani gari, anma dai muna kusa da babban birnin tarayya, garinmu babban birni ne,"
Shiru tayi dai duk bata fahimci maganarshi ba, ita tunda take banda k'auyensu babu inda ta taɓa zuwa, ko k'auyukan mak'wabtansu bata sani ba.
Wayanshi ce tayo ringing, ya katse kiran sannan yace "lokaci nata wucewa, karna rasa mota, ko zaki rakani gari saiki dawo?"
"A'ah za'aita yimun surutun na fara fita ai, Allah ya kaika lafiya ya maido dakai lafiya"
"Ameen saina dawo" ya juya ya tafi, har yayi nisa tana mishi addu'a, sai k'ok'arin shanye kukanta take, tana daina ganinshi kau ta duk'e wurin ta fara kukan da babu mai rarrashinta.
BIRNI
Da marece sosae Yasser ya isa garin nasu, kai tsaye gidansu ya wuce, babban gidane, mai kyau da tsari, duk yanda kyanshi yazo muku a rai, ya wuce nan, idan kaa shiga bazaka taɓa tunawa a k'asarnan kake ba
Daman zaman jiranshi suke, sosae suke nuna farin ciki da zuwanshi, sai da ya nutsu ya zauna sannan suka k'ara gaisawa da momiensa,
Husna data kasa sakin jikkarshi duk ta rirrik'e tace "Yaya tsarabanah fa?"
Momie tace, "In banda abunki Asma'u wanne tsaraba ne a k'auye?"
"nidai inaso momie, ai shine yamun alk'awari"
"indai tsaraba ne gaki gashinan, inda abunda zaki iya ci"
"zanci indai bazai ɓatamun ciki ba"
"kin daiji dashi" yace mata
Kiran wayarshi da akayine ya sakashi mik'ewa,
"Bara in shiga in shiga ciki momie, idan Daddy ya shigo a kirani plz" yana kallon husna ya k'arasa maganar,
Dariya take rik'ewa da yayi hanyar ɗakinshi, "tohh yaya, abincinka nananma, yaa daɗe yana jiranka"
"Yauwah k'anwar"
Yana tafiya ya ɗauka kiran, muryarta ta sauka a cikin kunnanshi,
"Hakanan jikina ya bani yau Masoyina ya dawo"
Yasseer ya saki murmushi kamar tana ganinshi, "Kin canka dai dai, yanzunnan ban daɗe da dawowa ba"
"Aina sani, kuma shine baka faɗamun ba?"
"Yi hak'uri Masoyiyah, nayi laifi"
"Zan hak'ura anma sai kaazo na ganka"
"Insha Allah gobe zaki ganni"
"Ban yarda ba, nidai yau zan ganka"
"Kinsan na shawo gajia fa, gashi dare yayi, goben idan nazo har saikin gaji dani"
"nidai A'ah, wata uku fa ban saka ka a idanuna ba"
"tunda kinyi hak'urin wata uku, ki k'aramin en awanninnan mana, nima fa naso in ganki"
Suna cikin maganar ya isa ɗakinshi, duhu yaa fara ta ko ina yakai hannu zai kunna fitila, sai kawai ya jiyo an rungumoshi ta baya, zai juyo ta saka hannu ta rufe mishi fuska.
©Rabiatu sk msh
0 comments:
Post a Comment