New Post

Thursday, 30 March 2017

MATATAH CE 67

♡MATATAH CE♡
   ♡♡♡♡♡♡
             67

©Rabiatu sk msh
      ®NWA
                   
            Labari....Ilileee

www.babymsh.blogspot.com

    Kafinsu tashi barci, an gama haɗa musu break fast, daman da Momie zasu tafi sunsha rok'onsu su dawo nan su karya kumallo, sai gashi sun dawo tunda wuri, sabuwar tabarma aka shimfiɗama Momie ta zauna sannan aka jere mata kayan break fast kala-kala.
   Koko da k'osai, fura, ɗan wake, shinkafa da wake, alala,  sabon tuwo, da shayi ruwan bunu (marar madara), Momie dai sai godiya take, "wannan kalaci duk mu kaɗai? Ai daa baku wahalar da kanku da yawa haka ba"
   Gwaggo tace "haba Hajia, ai babu komi, so muke kici ki k'oshi,"
   Ɗan waken kawai taci, don Momie akwai son ɗan wake, ta kora da ruwan koko ko kaɗan bata nuna musu k'yamata ba, zama tayi taci kamar yanda zataci a gidanta, Saude ta ɗauka na Najib ta tafi kai mishi yana cikin mota ya kasa shiga.

Ta ajje mishi, suna gama gaisawa ta tashi zata tafi, ya rik'o hannunta
   "wannan kayan break fast ɗin duk ni dawa?"
       "kai da cikinka mana"
    "wasa kike, sai dai ni dake"
        "nawa yana ciki fa yanzu zanje inyi"
    "A'ah wannan ya ishemu" ta mak'ale kafaɗa, "shikenan kwashesu ki koma dasu"
   "rigima ko?"
  Ya kashe mata ido, "mijinki na sonki kusa dashi ne"
   Jiranshi dai tayi harya gama, don a waje suka shimfiɗa tabarma, duk da ba mutane anma saita kasaci, shima Fura kawai yasha, qila itama don a gabanta ne, don gaba ɗaya tsantsamin kwanukan yake da ruwan garin, yana sha yanajin tashin zuciya dak'yar dai yasha da yawa.

  Tana maida kwanukan, ta kwashi tsarabar Hanne k'awarta ta fito, tare da Najib suka jera suka tafi shima yanaso yaga k'auyen. Nan su Gwaggo suka shiga rabon tsaraba suma, don daɗi bakunansu har kusa da kunne, wai yau sune suke fantamawa haka duk sanadin Saude da suka tsana.
   Suna tafiya tana mishi bayanin k'auyen, duk inda sukayi ana nuna su 'ga Saude can tazo da bak'on ɗan birni, Saude ce tazo daga birni taa waye, Saudece ta zama er gayu' kowah dai da abunda yake faɗa.
    "mutanen garinku fa ke kaɗai suke kallo"
    "A'ah ai kaine bak'o a wurinsu"
   Dai dai gidan da suka zauna ita da Yasseer ta tsaya tana kallo, bazata taɓa mantawa da gidan ba, abubuwa da yawa a gidan da bazata iya mantawa dasu ba.
   A gidanne aka fara ajjeta a matsayin amarya, a gidanne ta zama cikakkiyar mace, a gidanne ta samu farin cikin da bazata taɓa mantawa ba, a a gidanne ta samu bak'in cikin da har yanzu yakenan mak'ale a ranta, a gidan ta samu cikin Hafsat kuma anan ta haifeta, bazata taɓa mantawa da gidannan ba.
    Zagayowa yayi saitin fuskarta, ya ɗan kaɗa mata yatsunshi guda biyu, firgigit ta dawo daga dogon tunanin data tafi, "sau nawa zan faɗa miki banson ganin wannan fuskar a tare dake?"
   Murmushi tayi, "idan hakan ya maka mu tafi ko?"
   "Yayi anma saikin faɗamun nan inane?"
   Hawayen data daɗe tana maidawa ne suka fara kwararo mata, girgiza mata kai yayi, yasa hannu yana share mata hawayen, kama hannunta yayi sukabar wurin,
    "ga gidan Hanne can"
       "tohm ki fito inanan ina jiranki, kuma bance kiyi sauri ba don kawai kin barni anan, zan jiraki ko yaushene"
  Murmushi tayi ta ansa ledar hannunshi. Hanne najin sallamarta da gudu ta fito ta tarbeta, har suna kusan faɗuwa.
    "sai yanzu zakizo tun jiya ake kawomun labarin Saude tazo garinnan"
  "kuma shine bakizo kin ganni ba? Wai jirama tukunna ya akai kika ganeni"
  "inafa na ganeki, yanda aketa kwatantamin kene dai"
  "wai kinga yanda kika koma kuwa? Lallai birni taa ansheki, wallahi Hajjaju komai naki ya canja fa" sai shafa jikin Saude take yanda yayi laushi tana ta surutu.
    "kemafa kin canja k'awatah, don dai bazan mantaki bane anma dak'yar na ganeki, kin zama wata babbar mace, haba duk ina gayun naki kike nema ki tsofe da wuri?"
   "Hmm Saude kenan" ta lura tana cikin matsala, kuma ita bamaison jin sirrin mata da miji bane, bazata manta taimakon da Hanne tayi mata ba, ta kawo tsarabarta ta bata, da kuɗi masu ɗan yawa tace tayi jari, godia sosai take mata har suka fito k'ofar gida.

  Wurare da yawa sukaje da Najib a k'auyen, daga k'arshe suka wuce rafi.
    "Gaskia yanayin garinnan naku da daɗi yake, bana gajia da shak'ar sanyayyar iskarnan"
    "saimu barka anan kayita zamanka ai"
   "bazan damu bafa, indai tare dake ne"
   "daman ai kawu yace indai zai baka aurena tohm sai dai mu zauna anan"
   "ke! A ina? Anma dai da wasa kike ko?"
  Babu alamun wasa a fuskanta tace "Da gaske nake mana"
   "abincin k'auyennan? In kwana cikin k'auye? Kawu ya taimakamun mana"
   Dariya tayi sosae, "Matsoraci, daman nasan duk faɗi ne kawai"
     "ba haka ba, nafison na ajeki inda zakiji daɗi ne"
   "daɗin baki ko?" ta faɗa tana dariya, sai dai taji tayi tuntuɓe har saida ta faɗa jikin Najib, da sauri ya rik'ota, ta dafe k'irjinta dake faɗuwa sannan ta tashi a jikinshi.
     Duk'awa yayi wurin k'afar tata, "Sannu, baki daiji ciwo ba ko?"
   "A'ah, bara dai a ɗauke dutsin saboda kar wani ya k'ara faɗuwa"
  Ta duk'a zata ɗauke, ya riga ya zauna wurin, kamar dutsin daya taɓa mata ciwo a k'afa sanda ta faɗo daga bishiya, da sauri ta ɗaga kanta sama, bishiyar mangwaronnan ce wacce ta faɗo daga samanta lokacin da zata ɗeboma su Kabiruwa.
    Juyawa tayi tana kallon Najib, ta k'ura mishi ido sosae ji take kamar Yasseer ne take gani, bazata manta da haɗuwarsu ta farko ba, duk abubuwan da suka faru jikin bishiyarne suke dawo mata a ranta.
    Gatanan Zaune lokacin da ake mata Kamu, tuna rik'on da Yasseer ya mata a lokacin tayi, saida duk tsikar jikinta ta tashi, gabanta ya faɗi taja wani ajiyar zuciya, maganarshi ce ta dawo mata a kunne kamar lokacin yake mata ita, lokacin data mishi godiyar taimakon daya mata.
    "ni nake da godia, da kika bani dama harna taimakeki, kuma na samu lada"
   Najib ne ya hure mata ido, "kamar dai yau kika fara ganina" lumshe ido tayi, kamar dai Yasseer a haɗuwarsu ta farko.
   Tana murmushi mai ɗauke da damuwa ta kalla bishiyar, "wannan ne dalilin haɗuwatah da mijina na farko, ananne na ganshi, kayi hak'uri anma bazan iya tsaida tunaninshi ba duk sanda nazo wurinnan"
    "Shi kike tunani, anma ni kike gani domin nine a gabanki yanzu, bazan hanaki tunawa dashi ba, don nasan idan kika sake dawowa, nida shine zakina tunawa"
    Ɗaga mishi kai tayi, "Allah yaji k'anshi, yakai haske a kabarinshi"
   "Ameen ta amsa tana murmushi"

  Sai kusan Azahar suka koma gidan, Momie na jiransu har tayi shirin tafiya, yanayinta kawai suka gani gaba ɗaya hanjin cikinsu suka kaɗa, bama kamar Saude da gabanta ya fara faɗuwa, shikenan kawu ya gama tona mata asiri.
    Najib ne ke mata magana a ruɗe, "Meke faruwa Momie? Don Allah karkicemun zan rasa Saudat" ganin yanda duk suka tada hankalinsu, Momie ta kasa rik'e dariyarta, sannan suka sauke ajiyar zuciya.
   "mun gama magana, kawunka ya yarda zai baka auren Saude, da munje kawunanka zasu zo a saka rana, saura ka bani goran Albishir" kafin Momie ta rufe baki ya zaro komai na aljihunshi ya aje a gabanta, saida ya jiyo dariyarsu Kawu ne, ya fita daga gidan a kunyace, donshi baimasan suna wurin ba.
   A ranar sukai bankwana suka koma, duk kuɗinta da Najib ke bata harma da wanda Momie ke bata, bata kashewa ta damk'ama Kawu yayi gyaran gida, har mota ya bisu yana godia, harda en k'wallansu shida Gwaggo.
   Gaba ɗaya kuɗi sun rufe mishi ido, yama manta da wani auren Saude da Yasseer, don daman shi baida wani matsala da aurenta.

   ©Rabiatu sk msh

Related Posts:

  • A YINI ƊAYA 1-2[11:20pm, 19/09/2016] Amrah💓Pinky💓durling😘: 💀 *A YINI 'DAYA* 💀     💀💀           💀💀  … Read More
  • A YINI ƊAYA 5-6[11:54pm, 19/09/2016] Amrah💓Pinky💓durling😘: 💀 *A YINI 'DAYA* 💀    👹💀            💀👹  … Read More
  • A YINI ƊAYA 5-6[11:54pm, 19/09/2016] Amrah💓Pinky💓durling😘: 💀 *A YINI 'DAYA* 💀    👹💀            💀👹  … Read More
  • A YINI ƊAYA 3-4[11:35pm, 19/09/2016] Amrah💓Pinky💓durling😘: 💀 *A YINI 'DAYA* 💀    👹💀            💀👹  … Read More
  • A YINI ƊAYA 1-2[11:20pm, 19/09/2016] Amrah💓Pinky💓durling😘: 💀 *A YINI 'DAYA* 💀     💀💀           💀💀  … Read More

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts