♡MATATAH CE♡
♡♡♡♡♡♡
53
©Rabiatu sk msh
®NWA
Labari....Ilileee
www.babymsh.blogspot.com
Wani k'ayataccen ɗaki aka shiga da Saude, ɗaki ɗayane anma babba sosae, akwai kujeru masu kyau da babban Gado saiti, komai na ɗakin a tsare kalan skye blue, ba k'aramin k'ayatuwa yayi ba, a ciki harda toilet shima babu abunda babu a ciki kamar ansan da zuwan Saude,
Wuri ta samu ta zauna gefen gadon saman lumtsumemiyar katifarta, wai wannan k'ayataccen ɗakin duk nata ne, duk kayan dake cikin ɗakinnan na mutum ɗaya ne, lallai en gayu sunji daɗinsu,
Mai aikince ta dawo mata da abinci sannan ta faɗa mata tanaso tayi sallah, ta rakata toilet ta nuna mata yanda zatayi, ananma duk tasha k'auyanci, dak'yar ta gama kalle-kallenta tayi alwala ta fito.
Tunda tayi sallah ta kwanta barci ya ɗauketa, ko juyi batayi saman luntsumemiyar katifar, sai da asuba aka k'wank'wasa mata k'ofa, dak'yar ta tashi tayi sallah saboda barcin dake idonta, tana idarwa ta kwanta saman carpet ɗin taci gaba da barcin.
Sanda ta farka ta fito har Baba Haja ta tafi, bataji daɗi ba taso suyi bankwana ta mata godiya sosae, er aikin Hajiya ce ta rakata har ɗakin da hajiyar take tace tun ɗazu take nemanta, da Sallama ta shiga ɗakin, ta amsa mata duk da tana kan waya ne, ta ɗan tsaya bata shiga ba.
"shigo mana Saude, ina waya da ɗan uwanki ne"
Allah sarki hajia har yaranta sun zama en uwan Saude, saman cinyarta ta iske Hafsat tana ta wasanta, tana ganinta ta k'ara washe baki tana mik'a mata hannu, anma kunya ta hanata ɗaukarta ta nema wuri k'asa ta zauna tana jiran Hajia ta gama magana.
Cikin nishaɗi take wayar cike da soyayyar ɗa da uwa,
"Yanzu haka kaa gantanan hannuna, sai kallonta nake tana ɗebemun kewarka da kana yaro" bataji mai akace ba ɗayan ɓangaren sai dai hajiyar ta k'ara magana,
"nifa ba kama kuke ba, ita ai kyakkyawah ce kamar mahaifiyarta" dariya ta k'arayi bayan taa gama magana.
"kana dashi, anma dai takwarah ta taa fika kyau"
Tana dariya ta gama wayan "Hmm shak'iyin yaro kawai"
Saude tayi murmushi, "Ina kwana hajia"
"lafiya lau Saude ya kika tashi? ya bak'unta?"
"Alhmdlh"
"gaskia kinsha gajia, har Baba Haja ta tafi kinata barci, nina hana a tasheki gara a barki ki huta"
"uhum" kawai tace,
"Daddy ne muke waya inata bashi labarin Hafsat, yarinya mai saurin sabo, wai harya k'agu weekend yayi yazo yaga childhood image ɗinshi"
"Allah ya dawo dashi lafiya"
"Ameen, ya dawo yaga k'anwar dana mishi" murmushi dai kawai Saude take, taso ta tambaya Hajia sunanshi na gaskia, anma kunya ta hanata, da alama Hajia tanaji dashi sosae.
"kinyi wanka?" ta katse mata zancen zucin da take, girgiza kai tayi
"karin kumallo/kalaci fa?"
"A'ah"
"Har yanzu? Aikam mun tashi ɓatawa, banison bak'untarnan Saude kije kitchen talatu ta haɗa miki abunda zakici, idan kinyi wanka ki buɗa ma'ajiyar kayan sawa akwai na yayarki nanan kafin tayi aure, k'ila suyi miki kafin in fita ayi miki wasu"
"tohh Hajia nagode"
"kuma dai? Idan zakimun Godia duk abunda zan miki a rana dubu nawa zakimun? Kamar mahaifiyarki nake babu godia tsakaninmu, don haka ki ringa kirana da Momie kamar sauran Yayunki"
"Tohh momie Na..." sannan kuma tayi shiru ganin Momie ta ɗago tana kallonta, ta sakar mata murmushi sannan ta fita wurin talatu, cikin sa'a a falo ta ganta, daman tana tunanin inda zata gano kitchen ɗin.
Zaman Saude cikin gidan tana daɗa samun kwanciyar hankali, duk da babu inda take fita kuma shigarta da komai nata na k'auye nanan, sai dai jikinta dake k'ara murmurewa yana kyau ta ɗanyi k'iba jikinta ya fara kyau alaman hutu, kullum Momie zata kirata su zauna tana mata fira, tana k'ara janta a jiki, tsakaninta da Hafsat kuma sai kallo ko idan Momie taa fita ta ɗauketa, koda yaushe tana hannun Momie sai barci take bada ta wurin mai kula da ita, kayan yara masu na mata data gani zata zoma Hafsat dasu, ta washe sosai daman Gata kyakkyawa, kamar ba'a k'yauye aka haifeta ba, ta k'ara zama abun sha'awa ga kowa. Soyayya sosae take nuna musu kamar ita ta haifa Saude.
Kwananta biyar da zuwa gidan ko tsakar gida bata taɓa fita ba, aka fara shirye-shiryen dawowan yaron Momie, kullum sai momie tayima Saude firan Daddy, shima har gajia yake da labarinta da momie ke bashi, yamafi son firar Hafsat har waya suke tayi ta yi mishi gwarancinta.
Daren Ranar dazai dawo basu kwanta da wuri ba, soye-soye aka dinga mishi kamar ba mutum ɗaya ne zaizo ba, yanda Saude ta dage tana aiki duk da daman kullum bata zama, yasa momie take ta faman ce mata taje ta huta, anma bata tafi ba har aka gama.
Washe garin ranar dazai dawo friday, tunda safe suka farka aka fara girke-girke, momie sai faman kiranshi take tun safe, kaɗan-kaɗan taa cema Saude, ko mantawa take da tayi mata maganar?
"Kinga k'azamin yaronnan yak'i ya dinga barin mukullanshi a mishi gyaran ɗaki, kullum yafison zama cikin k'azanta"
Sai dai kawai tayi murmushi "ai haka ɗakin mazan yake Momie"
"Haba k'azamai dai, koda Husna nanan sun dinga faɗa kenan idan taa mishi gyara bai sani ba, wai tana zubda mishi takardu masu amfani"
"Allah sarki, ai basu cikason hakan ba"
"Hhm bakisan k'azantar Yayannan naki bane, saiya buɗa ɗakin nashi zakiga jibji" dariya tayi sosae, momie ma ta tashi tana dariyar jibjin da tace.
Har marece ana jiranshi baizo ba, momie sai kiranshi take a kashe sai marece sosai ta sameshi.
"wai meya tsaida kai har yanzu baka dawo ba?" ta ɗanyi shiru tana saurarenshi.
"A'ah kasan banson tafiyar darennan, kayi zamanka kai aikinka wani satin kaazo"
"A'ah nace, duka yaushe ka tafi? Ka zauna ka gama duk abunda kake fa"
"Yauwah tohh zan kashe saimun sake maganar" ta sauke wayar fuskarta da alamar rashin jin daɗi.
"kin ganshi ashe aiki ya tsaidashi, wannan satin bazai samu zuwa ba"
"Allah sarki, ai kamar gobene"
"Hakane Allah ya kaimu"
"Ameeen"
Da dare momie ta kirashi tana k'ara tambayarshi aikin, duk yaa lura bataji daɗin rashin zuwanshi ba, Momie taa damu dashi sosae, sai dai yaci gaba da kwantar mata da hankali da firar da zata sakata daria irinna ɗa da mahaifiya harta ware, sannan sukai sallama, lokacin Saude ta shigo mata saida safe, tana kan cewa ya rik'e wayan su gaisa da k'anwarshi harya kashe, ta mata bankwana ta koma ɗakinta.
Washe gari da wuri Momie ta fita, har Hafsat ta saka aka shirya mata ita ta tafi da ita Saude na can tana barci, sai k'arfe 10 ta farka da wata matsananciyar yunwa, ta sauko daga Gadon sannan ta jawo zani ta ɗaurin k'irji dashi saman doguwar rigar barcin jikinta, ta tsira ɗan kwalinta irin style ɗin da suke a k'auye shigarsu dai ta en k'auye, kai tsaye kitchen ta nufa.
Talatu ce kaɗai a kitchen ɗin ta fara aikin rana, ta gaisheta cikin girmamawa, sannan tace "Momie fa?"
"sun fita ita da takwararta"
"Yau safko sukayi kenan"
"aikam da wuri ta fita"
Suna ɗan taɓa firarta tana haɗa break fast, doya da k'wai sai ruwan tea ta ɗauka ta fito tana cema talatu bara tayi break fast ta dawo.
"ai naga alama barcinnan bai isheki ba, yunwah ce kawai ta tasheki"
"wallahi fa, ai hakanan dai zan barshi" ta faɗa tana murza ido da hannun data rik'e tean, bayan taa cika baki da doya. Dai-dai lokacin tana wucewa ta k'ofar da zata shigo da mutum falon.
Ji tayi ta kaima mutum karo, gaba ɗaya tean dake hannunta ya kwarare mishi a jiki, da sauri tayi k'asa dakai ba tare dasun haɗa ido ba, jikinta ya fara kyarma ganin yanda ta mishi a jiki tama kasa bashi hak'uri.
©Rabiatu sk msh
0 comments:
Post a Comment