♡MATATAH CE♡
♡♡♡♡♡♡
54
©Rabiatu sk msh
®NWA
Labari....Ilileee
www.babymsh.blogspot.com
Ko kallon inda take duk'e baiyi ba, ya wuce ta kawai ya shiga falon, wata hanyar yabi daban, saida taji yaa wuce sannan ta ɗago tana kallonshi bata ga fuskarshi ba, anma a jiki ma ba k'aramin haɗuwa yayi ba, shigarshi kanta ta dabance, ga k'amshin turaren daya bar mata nan mai daɗin k'amshi.
Sauke ajiyar zuciyah tayi bayan yaa shige, take tambayar kanta shi kuma wannan daga ina? Anma ganin yanda ya shiga gidan kai tsaye ya sanyata gano shine yaron Momie da suke sanya ran dawowarshi jiya. Yasseer ta tuna, da ko dak'ik'a ɗaya bata taɓayi ba tare da tunaninshi ba, hakanan wani lokacin sai dai ta shige ɗaki tayi ta kuka har sai k'uncin ranta yaɗan rage, don wani lokacin kuka ma yana maganin damuwa.
Break fast ɗinma kitchen ta koma dashi tayi, hakanan sukuku ta ringa taya Talatu girkin, har Momie suka dawo bata sani ba tana can suna aiki, sai dai ta aiko ma Talatu kalolin Abincin da za'ama Daddy,
Talatu tace "ashe dai Daddy yaa dawo? Yanzu girkin gidannan zai k'aru"
"cin abinci ne dashi sosae kenan?" Saude ta tambayeta,
"A'a zaki sha mamakin kalolin abincikan da za'a haɗa mishi, anma sai yaga dama zaiyi cokali biyar"
Sadeey tace "tohhh"
"sosai fa, kuma duk ma'aikatannan gidannan idan yazo ni kaɗai nake girki yaci, donshi bai son abincin en aiki"
"Allah sarki, wasu ai k'azantane basu so"
"kamar kin sani kuwa shima haka yake, don ɗan gayune na gaske, ubangidana akwai tsafta, anma idan kika shiga ɗakinshi...."
Tun kafin talatu ta k'arasa Saude ta kwashe da dariya tuna abunda momie tace jiya,
"tunma kafin kiga ɗakin nashi kin fara dariya kenan" ta faɗa taa ɗauka ita take ma dariya, talatu akwai labari koba komai firar da take mata tana rage mata wani tunanin,
"kinga yanzu tayani zakiyi mu ɗaura girkin nashi, rana nayi gashi kuma wannan ban kusa gamawa ba"
"tohh" tace sannan ta tashi ta fara k'ok'arin ɗaurawa, da yake tana koyo a wurin talatu kusan duk girkinma ita tayishi, har suka gama suka jerashi a dinning.
Ɗakin Momie ta shiga, tayi mata sannu da dawowa, harta mik'e zata tafi, Momie da fara'arta tace "Yayanki yaa dawo fa, yanzunnan ya fita dakun gaisa" shiru tayi data tuna abunda ta mishi saida taji tashin hankali, jiki ba k'wari tace, "Barka momie ya iso lafiya"
"Yauwah Saude, kije kiyi wankan kun gama girki ko?"
"eeh an ajje komai Momie"
"yauwah tohh idan kinyi wankan kimun magana"
"tohm momie"
Bayan ta fito daga wankan, mai kawai ta shafa ta saka kayanta, milk atamfa ce mai kwalliyan ja a jiki, ɗinkin riga da zani yayi kyau sosae, tayi ɗaurin k'irji da zanin can sama ta tattareshi, ta cukuikuye ɗan kwalin ta ɗaureshi tsakiyar kai, ta fito daga ɗakin ta fara biyawa ɗakin Momie, tare suka fito bayan taa kira Daddy a waya.
Da sauri Saude ta jama Momie kujera ta zauna, ta zuba mata abinci ta duba bata ɗauko miya ba,
"Momie ban ɗauki miyanki ba bara inzo"
Tace "tohh" tana k'ara kiran Daddy a waya ko meya tsaidashi? Da sauri ta ɗauko miyan tana sauri ta kawo ma Momie wurin shiga dinning ɗin sukaci karo shima yana sauri momie tayi kiranshi, kamar ɗazu dai gaba ɗaya ta juye mar miyar a jikin fararen kayanshi. Da sauri ta ɗaura hannu akai a razane.
Wannan karon ta k'ure hak'urinshi da rashin maganarshi, wata irin tsawa ya daka mata "ke jahilan wacce gari ce da bakya kallon gabanki tsabar k'auyanci"
Duk taa tsure hawayene ke bin fuskanta, "Kayi hak'uri"
"Dallah rufamun bakinki, hak'urin banza, wannan ma ai tsabar raini ne, kinga ɗazun ban miki ba kawai kuda kunfison mutum yana ɗaga muku murya"
"kinyi shiru malama saina faɗa miki ki gyara ɓarnar da kikayi?" da sauri duk ta ruɗe ta kamo rigarshi ta fara k'ok'arin gogewa duk wurin ya k'ara damewa, wani tsawar ya k'ara mata,
"ke! Miye haka?" duk ta tsorata taja baya, tama rasa me zatayi, Momie daga can tana jiyo su, cikin faɗa-faɗa tace "Haba Daddy banfason zafin rannan, tunda taa baka hak'uri kaje ka cire kayan mana" ya buɗa baki zaiyi ma momie magana kuma ya fasa, a zafafe yabar wurin bayan ya sakar ma Saude wani dogon tsoki, baiko kalla inda take ba.
Wata miyar taje ta kawo ma Momie, sannan ta gyara wurin duk jikinta a sanyaye, muryarshi nata yawo a k'walwanta, sosae take ratsa mata dukka sassan jikinta, ko kaɗan bataji daɗin abunda tayi ma ɗan lelen Momie ba.
Momie ta kirata bayan ta gama gyara wurin,
"Kinga zauna kici abincinki, ki manta da wannan Yayan naki Zafin rai ne dashi, kina hak'uri da faɗanshi kinji"
"babu komai fa Momie aini na mishi laifi"
"Yauwah tohh zuba abincinki kici" ta zuba kaɗan, tana zama taa gama zubawa sai gashi ya dawo da wasu kayan da alama wankama ya canja.
Bayan yaa zauna Momie tace Saude ta zuba mishi abincin, Momie tace "Me zakaci?" baiko ɗago kai ba ya bata amsa sannan yaci gaba da danna wayarshi, lallai mutuminnan miskili ne, ko magana bai cikason yi ba.
Data gama zuba mishin ma ya daɗe sannan ya ɗauka ya fara ci, yana ci yana danne-dannenshi a waya, sai dai yakai cokali yaji babu komi yaa cinye plate ɗaya, Momie na lura dashi tace "Da alama girkinnan dai yayi maka daɗi" cikin zolaya
"Gaskia ne Momie, talatu bata taɓa girki mai daɗin na yau ba"
"Daman ya za'ayi Talatu tayi girki mai daɗi haka? K'anwarka ce tayi maka"
"K'anwatah kuma?"
"eeh mana, idonka ya rufe da faɗa ko gaisawa bakuyi ba,"
Ranshi ne ya ɓaci, waida wannan cikakkiyar bak'auyarce Sauden da Momie ke bashi labari? Duk da baiga fuskarta ba, shigarta ya nuna ko hasken birni bata saba gani ba. Ajje cokalin kawai yayi ya mik'e zai bar wurin.
"Koma ka zauna nace" inji momie, yaɗan tsaya anma bai tafi ba, ta k'ara cewa "Idan ba so kake raina ya ɓaci ba" da sauri ya koma ya zauna don baison ɓacin ranta.
"Saude baki gaishe da yayan naki ba" a hankali tace "ina wuni"
"Lafiya" ya amsa a tak'aice kaman dole,
"Ya hanya an dawo lafiya?" tsoki ya saki kawai, sai da Momie ta mishi wani kallo sannan ya amsa, har lokacin hankalinshi nakan waya.
"Banson halinnan Daddy k'anwarka ce, ka ɗauketa kamar Husna, banson k'ara ganin wani banbanci"
"naji Momie"
"Yauwah Babanah, Saude tashi ki k'ara mishi abincinnan", don dai abincin ya mishi daɗi, anma kamar yace karta zuba duk da ya k'oshi sai yace "farfesun en cikin kawai" daman shi kaɗai ne baici ba, sai lokacin ta ɗaga kai ta kalleshi.
A tare shima ya ɗaga ido yana kallonta, wani irin faɗuwar gaba taji, da batasan dalilinshi ba, tama kasa ɗauke ido daga kallonshi duk taa zuba mishi manyan idanunta, duk yanda ake cewa suna yanayi da Hafsat bata ɗauka yakai haka ba, har yanayin kallonsu ɗaya, shima kallonta yake ko k'iftawa baiyi, bak'auyah ce, anma ba irin k'auyawan daya saba gani ba, kallonta kawai yake yana k'are mata kallo,
Ya rigata ɗauke ido, gaba ɗaya rikitashi take da manyan idanunta, "ke kallonma k'auyanci kike mishi?" da sauri ta sauke idanunta tana zuba mishi girkin, Momie tayi dariya kawai lokacin taa gama nata launch ɗin.
Ta mik'e zata tafi yace "Momie wai yaa maganar kiwon da nace miki zan fara?"
Tana dariyarta ciki-ciki tace "Kiwon en ciki?" aikam sun bama Saude dariya, shima dariyar yayi, "Nifa Momie ba santi nake ba"
"ai bance ba, daɗin girkin Saude ne kawai kakeji" ta tafi tana dariya, ta barshi daga shi sai Saude a wurin, waya taji an kira shi, abinda kawai taji yace "Eeh Najib ne"
A hankali ta sake maimaita sunan nashi "NAJIBULLAHI" suna mai daɗi.
©Rabiatu sk msh
0 comments:
Post a Comment