♡MATATAH CE♡
♡♡♡♡♡♡
70
©Rabiatu sk msh
®NWA
Labari....Ilileee
www.babymsh.blogspot.com
Da Yasseer yayi Sallah yaso ya koma barci abun ya gagara, wani irin azababben ciwon kai ya saukar mishi ko motsin kirki dak'yar yake da kan, gaba ɗaya ji yake kaman duniyar ne duka yake ɗauka.
Hayaniyarsu da yake jiyowa a falonne ya k'ara hargitsashi, daganan yana jiyo dariyar Najib da Saudat, a hankali yake fita zuwa falon ya ɗaura hannuwanshi duka biyun yaa dafe, yana tafiya dak'yar.
Sun baje I.V tana gani, ba k'aramun kyau sukai ba da gani an kashe kuɗi da yawa, ko meya haɗosu? Cikin wasan ta tilla mishi filon kujera, ya tare da hannuwanshi biyu bai sameshi ba yana mata gwalo ta k'ara jefa mishi wani sai saman k'afan Yasseer.
Su duka suka ɗaga ido suna kallonshi, da gani yanajin azabar ciwon kan lokaci ɗaya har ya faɗa, Najib ya mik'e a ruɗe yaje inda yake.
"lafiyanka bruhh? Meke damunka?"
Yak'e kawai ya mishi yace "ba komai" ya raɓa gefenshi zai bar musu ɗakin, Saude ta gaisheshi, hakanan ya tsinci kanshi da sakar mata fuska.
"lafiya lau Saudat ya kika tashi?"
"Alhmdlh" sai kuma ya fita yanajin haushin zuciyarshi da rigimar da take shirin kunno mishi, me yasa zuciyarshi zata mishi haka? Da gani basai an faɗa ba Saudat da Najib masoyane da suke matuk'ar son junansu, tayayama zaiyi nasara?
Yana fita Najib ya zauna jikinshi a sanyaye, damuwa ce bayyane a fuskarshi, "gaskia bruhh yana da damuwa, kuma nasan zurfin cikinshi bazai taɓa bari ya faɗamun ba, koma menene tunda kika ganshi haka yana matuk'ar damunshi da yawa, shi mutum ne da bai ajje damuwa a ranshi"
Itama sosai ta tausayama halin da Yasseer yake, "Allah sarki, Allah yasa dai ba wani matsala bane"
"Ameen"
Ɗakin Momie ya shiga, tana duba zannuwan gadon data saima Saude, da ganin yanayinshi ta maida hankalinta kanshi, zaman dirshan yayi a saman carpet ya jinginar da kanshi a bango,
Momie duk hankalinta ya tashi ta koma inda yake "Baka lafiya ne?" ya girgiza kai kuma ya ɗaga.
"meke damunka?" wasu siraran hawayene suka gangaro mishi, cikin muryan tausayi yace "nima ban sani ba Momie"
"bazai yiwu ba, dole zakasan dalilin damuwarka, sai dai in yauma bazaka faɗamun ba"
Tohh ciki waccema zai faɗa mata? Labarin Saude Matar daya aura a k'auye ya gudu ya barta da har yanzu soyayyarta da tunaninta suka hana zuciyarshi sukuni, har yanzu dana sanin abunda ya aikata yake? Ko kuma matsalar Rabi'ah ta kullum take damun k'wak'walwarshi? Bata rageshi da komai ba, duk wani soyayyar miji da mata tana nuna mishi, matsalanshi ɗaya da ita rashin son haihuwa, kuma Allah ya yishi da son yara, shima yanason yaga k'wanshi a duniya, ko kuma babban matsalan da shi kanshi kunyar kanshi yakeji, wai yanason matar da k'aninshi zai aura!
"ban sani ba Momie, anma inajin kaman duniya gaba ɗaya ta juyamun baya"
"meyasa kace haka?"
"ba komai Momie, anma ina neman Alfarma a wurinku"
"ka faɗi koma menene"
"Don Allah Momie a taimakamun a ɗaga ranar ɗaurin aurennan"
"saboda me?"
"yayi shiru ya kasa bata amsa"
"Karka damu, insha Allah kafin lokacin kaa warware, ka yawaita addu'a akan damuwarka, shi Allah maji rok'on bawansa ne, akwai wata addu'ah a cikin husnul muslim: Allaahumma 'innee 'abduka, ibnu 'abdika, ibnu 'amatika, naasiyatee biyadika, maadhin fiyya hukmuka, 'adlun fiyya qadhaa'uka, 'as'aluka bikulli ismin huwa laka, sammayta bihi nafsaka, 'aw 'anzaltahu fee kitaabika, 'aw 'allamtahu 'ahadan min khalqika, 'awista'tharta bihi fee 'ilmil-ghaybi 'indaka, 'an taj'alal-Qur'aana rabee'a qalbee, wa noora sadree, wa jalaa'a huznee, wa thahaaba hammee ."
"fassarar addu'ar shine: Ya Allah! Ni bawanka ne, kuma ɗan bawanka, kuma ɗan baiwarka. Goshina a hannunka yake, hukuncinka zartacce ne a kai na, kuma k'addararka gareni mai adalci ce. Ina rok'onka da kowane suna naka, wana ka ambaci kanka dashi, ko ka saukar dashi a cikin littafinka, ko ka sanar dashi ga wani daga cikin halittarka, koka keɓance kanka da saninsa a cikin ilmin fake da ke wurinka, da ka sanya Al-Qur'ani ya zama kaka ga zuciyata, da haske a k'irjina, da kwaranyewa ga bak'in cikina, da kuma mai tafiyar da damuwata."
"insha Allah zaka samu sauk'i a zuciyarka, bansan meke damunka ba, anma duk ɗan adam daka gani Allah yana jarrabarshi, kuma imanin mutum baya cika saiya yarda da k'addara mai kyau da marar kyau, komai kaga ya faru dakai k'addarane, idanma matsala tsakaninka da Rabi'ah ne kayi k'ok'arin gyarawa tun wuri, kada ka taɓa raunana zuciyar mace, kada kace zaka juya mata baya don matsalar dake tare da ita na rashin haihuwa"
"kodai matsalan data ɗaurawa kanta?" ya faɗa a zuciyarshi, baison ya faɗama Momie tsakaninshi da Rabi'ah ne, don bazaiso ya haɗasu ta dinga ganin bak'in taba, anma dai duk yanda zaiyi da Rabi'ah batajin lallami ko shawara,
"Na gode Momie" ya furta yana zubar da hawaye, saiga Hafsat ta shigo da gudu Najib ya biyota, baisan sanda ya mik'a hannunta tazo wurinshi ba, ta zulle ko kallanshi batayi ba ta faɗa kan Momie.
"Guje-gujenne ko Hafsa? Bana hana ba?"
Tana shesshek'ar gudu sai dariyarta take "Momie Daddy ne ya biyoni"
"shine kika rugo haka ko ɗayan Daddynki bazaki gaisar ba?"
"ni Daddy na ɗaya mai sona, ban haɗashi da kowa ba Momie"
"Wannan ma babanki ne, ki gaisheshi nace" ta kalleshi tana tura baki, hakanan yarinya da ita gaba ɗaya haushinshi takeji, sai kuma ta ganshi yana hawaye sosai ya bata tausayi.
Ta tafi inda yake, ta saka k'asan rigarta tana share mishi hawaye, ya ɗago yana kallonta, murmushi ta mishi, "Mamana taa hana kukan rigima, idan ta ganka kana kuka Momie zata faɗa mawa kuma Daddyna bazai kaika shan ice cream ba"
Murmushi yayi yarinyar sai k'ara burgeshi take, inama ace tashi ce? Lallai iyayenta ba k'aramin Sa'a sukai da samunta ba.
"na daina kuka, anma saikin yarda mun shirya bazaki k'ara guduna ba"
Ta mak'ale kafaɗa "nina daina shiri da kowa, best frnd na ɗaya"
"wanene?"
"Daddy na"
Najib ne ya shigo ɗakin yana nemanta, ganin Yasseer zaune gaban Momie harya juya zaiyi baya, Yasseer ya mik'e yabar ɗakin duk kalanshi ya canja.
Momie ta kalleshi, "yayanka ya faɗa maka damuwarshi?"
"A'ah Momie, kin sanshi dai da zurfin ciki"
"tohm Allah ya kyauta"
"Ameen"
"Ina Saudat ɗin?"
"ta wuce ɗaki tasha maganin ciwon cikinta"
"ni wannan ciwon ciki da tak'i yarda aje asibiti"
"ai tace da tasha magani yake tafiya"
"Allah ya bata lafiya"
"Ameen"
Hidimar biki kawai ake, ranar laraba za'a fara shagulgulan, don ita Saude in yanda takeso nema baza'ayi komai ba, tunda safe take jiran Najib shiru bai fito ba, tana ta mishi waya bai ɗauka ba, ta wuce ɗakinsu a falo ta tsaya tana k'wala mishi kira, taji shiru dai saita shiga ɗakin don bataga alaman Yasseer na ciki ba.
Najib ne kwance shi kaɗai, ganinshi da shirin fita ne ya tabbatar mata ba barci yake ba.
"Masoyi kaifa nake jira" ya mata shiru kawai,
"in tafiyatah bazaka kaini ba?" saima ya k'ara gyara kwanciya.
Ta ɗan saka hannu tana buga filon da yake kwance, yanaso yayi dariya ya rufe fuskarshi da filo,
"daman nasan ba barci kake ba" tayi dariyar mugunta, a ranta tace yanzu zaka tashi.
Ta ɗauko wayanta ta fara mishi video, "idan kana barcinma kafi kyau, tunda bazaka kaini ba bara in maka video, wow! Kaaga yanda kayi kyau kuwa?" duk ta kashe mishi ido da flasher ya kasa rufe idon da daɗi.
"wai da gaske videon kike?"
"ina ruwan mai barci da abunda nake?" ya diro daga saman gado.
"in gani inda gaske ne"
"nak'i fa" ta tashi ya biyota da gudu, suka fara zagaye ɗakin taa hanashi ya gani.
Suna cikin zagaye ɗakin ya samu dak'yar ya kamota ya rik'e, ɗaga wayan yayi, "kinga irin videon da zaki ɗauka nan"
Ta fara k'ok'arin zamewa, shikam hankalinshi kwance yanata mata dariya dak'yar ta k'wace, da gudu tabar ɗakin, yace, "Matsoraciya kawai"
Da yake ba kallon gabanta take ba, tana fita sai dai taji ta faɗa ma mutum, kwance saman k'irjinshi, wani iri takeji a jikinta, gaba ɗaya ma ta kasa ɗagowa, ko ban faɗa ba kunsan ko waye.
Tafe yake shima gaba ɗaya komai nashi ya canja, ko tafiya yake tunani ne kawai. Zuciyarshi, ga tarin damuwa data mishi yawa.
©Rabiatu sk msh
0 comments:
Post a Comment