New Post

Thursday, 30 March 2017

MATATAH CE 63

♡MATATAH CE♡
   ♡♡♡♡♡♡
             63

©Rabiatu sk msh
      ®NWA
                   
      Labari        
               Ililee...  

www.babymsh.blogspot.com

   Saude na zaune gefen Momie bayan ta aika kiranta, saiga Najib ya shigo yana fad'a mata su Yasseer sun sauka yanzu zaije ya d'aukoshi, tsayar dashi tayi.
   "da yanzu zan tura Saude gidan Husna da driver, anma tunda zaka fita saika wuce da ita, anma ka hanzarta tana jira"
    "Gidan Husna kuma? Me zatayi?" ya tambaya Momie cikin mamaki.
   "Wai aikin azumi ta fara, taa kasa k'arasawa kaasan yanzu tayi nauyi (cikinta ya tsufa) shine zataje ta dinga tayata"
   "kuma sai Saudat d'inne zata tayata dole?"
   "kasanta dai batason er aiki, shiyasa ta nema taimakon k'anwarta, sauri fa zakayi taa cemun girkinta nakan wuta" ya k'ara b'ata rai duk baiso ba, "yaushene zata dawo?"
    "idan ta haihu mana, nikam Daddy bansanka da haka ba"
   "ai dole in damu Momie, tunda zatayi nesa dani"

  Kunya ya bama Saude ta mik'e, "bara inje in had'a kayan dazan tafi dasu,
Momie ta tsayar da ita, "Daddy zai kai miki daga baya, ki d'auko mayafinki dai"
    "tohh" ta tashi ta tafi, ba don yaso ba ya hak'ura ta koma gidan Husna.
  A hanya suna tafiya duk sunyi shiru, ta d'an karkad'a mishi yatsunta biyu ya jiyo.
    "wai bazakace komai ba?"
  "Nama rasa mezance Masoyiya, tunaninah kawai yanda zanyi rayuwa koda na rabin awa ne baki a kusa dani"
       "kana magana kamar wacce zata bar garin ko zata maka nisa, nasan ai duk inda nake zaka kasance tare dani"
   "Hakane fa, don yanzu zama gidan Husna ya kamamu" dariya tayi, ta bud'a baki zatayi magana dai dai lokacin sun isa gidan, ya shiga da motan yayi parking harta bud'e zata fita ya kalleta.
    "Sai sauri kike ki barni ko" da sauri ta d'aura hannunta saman leb'enta.
    "babu wannan kalmar tsakanina dakai, ni taka ce, bazan tab'a barinka ba"
   Murmushi yayi "nima duk da wasa nake miki, anma saida harshena yayi nauyin fad'a"
   "Yayanmu fa yana jiranka a airpot, kayi sauri plz"
   "Aww! Nifa ina tare dake mantawa da komai nake, saina dawo" tana murmushi take d'aga mishi hannu harya fice sannan ta shiga gidan.

  Tayi sallama sannan ta shiga gidan, Husna na zaune falo ta baje da gani ta tara gajia, ta amsa sallamar Saude.
    "Sannu Aunty Husna"
  "Yauwah Aunty Saudat" ta fad'a tana tsokanarta.
   "yau dai zan saka Matar yaya aiki"
   "Aunty Husna zolaya ko? Yanzu dai dame zan fara? Lokaci ya kusa"
    "komai yananan kitchen na fara na kasa k'arasawa"
   "Tohh Aunty bara inje" tana tafiya hanyar kitchen d'in Husna ta mata magana da d'an k'arfi yanda zataji.
   "Yaya Yasseer ya dawo kuwa?" saida gabanta ya buga yanda takeji kullum aka ambaci sunanshi.
     "A'ah yanzu dai yaa tafi ya d'aukoshi"
  "Wlhy naso aje tarbansu dani, anma dai duk jikina ba dad'i nakeji"
       "Ayyah! Aikam yaronnan yazo duniya fad'a zanyi dashi tunda yana takura Auntyna"
   "tohh bara Abbanshi yazo in fad'a mishi" tana dariya ta k'arasa shiga kitchen d'in, "ba ruwana fa wasa nake" itama Husna dariyan take. Ta shige kitchen ta fara aiki, ba wani mai yawa bane, kafin a kira Sallah taa kammala komai, ta wuce d'akin da Husna ta nuna mata ta zauna.

   Kamar ba abunda ya faru, Momie ta tarbi su Yasseer hannu biyu sai nan-nan take dasu, Rabi'ah sai wannan shisshigema Momie take ita mai suruku, sunje bud'a bakima a kusa da ita ta zauna sai fira take mata kamar ba surukarta ba ko er kunyarnan babu. Shidai Yasseer sai d'ari-d'ari yake don yasan ya b'ata ma Momie rai da yawa, sai da ta koma d'akinta yaje ya sameta jikinshi a sanyaye, ya d'uka saman gwiwoyinshi kamar zaiyi kuka.
     "Na sani ni mai laifi ne, kuyi hak'uri Momie hakan bazata sake faruwa ba, don Allah karkiyi fushi da d'anki"
   "Kaga alaman ina Fushi dakai? Damuwata na rashin zuwanka gidane daman, tunda na ganka kuma sai hankalina ya kwanta, ai babu wata uwa dake fushi da d'anta" rarrafawa yayi kusa da ita cikin farin ciki ya kwantar da kanshi saman cinyarta, "Hakan bazata k'ara faruwa ba insha Allah, nagode Momie"  murmushi tayi tana shafar kanshi kamar k'aramin yaro. Magana takeson mishi akan jikokinta da bataga alamansu ba, anma taa rasa ta inda zata fara mishi.
   Rabi'ah ce ta shigo d'akin,
      "Momie ya zaki barshi kamar k'aramun yaro? Kaifa nake jira hniee"
   "Ki barni inji d'umin mahaifiyatah mana, yaushe rabon da in ganta?"
   "Oh! Tohm ai bakai kad'ai keda ita ba, nima Momien tawace" ta k'arasa shigowa d'akin itama zata kwanta cinyar Momie tana musu dariya tace "Maza dai ku k'arasa er tsohuwar tun kafin jikokina suzo", cak Rabi'ah ta tsaya duk ta b'ata rai, ta d'auka wayarta dake gefen Gadon Momie.
    "Yanzu zan wuce gida Momie, sai Allah ya kaimu"
  Baki bud'e Momie ta bita da Kallo, "Allah ya kaimu" Yasseer ya mik'e da sauri, "Bara inje in kaita Momie" sai kuma ya lura da yanayin da take ciki.
    "nima haka nake fama da ita Momie duk sanda na mata maganar haihuwa" kad'a kai kawai Momie tayi, har suka tafi.

  A tsakiyar falo suka had'u da Najib ya sab'a Hafsat a kafad'arshi,
    "broda sai ina?" ya juyo muryar Yasseer ya tsaya sannan ya juyo, "Gidan Husna zanje"
   "Daa kuwa aron Motarka nakeso zankai Rabi'ah gida"
       "tohh ai sai in d'auka wata" yana zaro mishi mukullan a aljihu, ya saka hannu ya shafi fuskar Hafsat.
   "Ina kuma ka samu kyakkyawar babynnan?" da sauri ta fizge fuskarta daga hannun Yasseer,
    Murmushi yayi da wasa Najib yace "Tawah ce".
   "aifa da shekarun da nayi bananan sunkai shekarunta a duniya, tohm bazanyi tantama ba don kuwa komai naka ta d'auko" inji Yasseer
   Najib yace "haka aketa cewa yanayinmu d'aya, shiyasa nakeji da d'iyar Momien nan, Hafsat bazaki gaida Uncle ba?"
   Zumb'ura baki tayi ta kauda fuska gefe kamar ta sanshi, "Sunan Momie kuma kuke kiranta dashi ko sayawa bakuyi?"
   "ai Momie ta hana a b'oye sunan"
   "Mai kyau da ita, Inama kuka samota?" Najib ya bud'a baki zai bashi amsa suka jiyo muryan Rabi'ah, "Hniee kaifa nake jira" ya juya zai tafi kuma ya dawo ya mik'a mata hannu.
   "Hafsat zaki rakani?" mak'ale kafad'a tayi,  Najib yace "anma dai nayi Mamaki, Hafsat bata tab'a yima wani haka ba, akwaita da sakin jiki da Mutane"
   "aini bak'one a gareta, zamu saba ko Hafsat? Hakanan ina son yarinyar sosae"
      "ai haka take da saurin shiga rai" ya juya ya tafi. Shima wasu mukullan ya d'auko sannan suka fito, cikin irin fushinta na yara ta cema Najib, "ka fad'a mishi karya k'ara tab'ani"
  Cikin mamaki yace "Sabodame Hafsat?" shiru ta mishi, har sukaje gidan yanata tambayarta tak'i ta amsa, ya k'yaleta kawai sannan ta saki jikinta. Can ta wuce cikin gidan wurinsu Husna da yake ta saba dasu sosae, har so suke tazo musu yini, Masoyan biyu kuma suna can waje ta musu shimfid'a suna fira.

   Sai da dare yayi sosai basuma sani ba, har Hafsat tayi barci, sannan sukai sallama zai tafi ya ciro sabuwar waya a kwalinta ya mik'a mata, ta amsa tana murna ta bud'a, Iphone7 ce komai irin tashi, sai murna take.
   "ni banmasan ta inda zan fara nuna maka farin cikina ba, babu abinda zan biyaka dashi da soyayyar da kake nunamin"
       "ai kin riga da kin gamamin komai tunda kika mallakamun soyayyarki, kici gaba damun Addu'ah karna rasaki Saudat"
   "bazaka rasani ba, ka kwantar da hankalinka Saudat takace"
   "zai kwanta dai, anma sai sanda kika k'arasa zama tawa d'in" murmushi tayi, "ka d'aukama na zama" ta ciro wayan daga kwalinta, a kunne take da simcard d'inta,
     "Allah yasa dai ka faramun saving numberka, don ita zan fara sakawa"
   "Abunda na fara yi kenan ranki shi dad'e"
   "gaskia nagode sosai dear" harararta yayi cikin wasa, ta rufe bakinta da hannu, "Sorry na daina, wallahi dad'ine har yamun yawa"
    "Kin rik'eni da yawa, so kike Momie tace nayi dare gobe ta hanani fitowa?"
  Yanda yayi maganar saida ta bata dariya sosae "Momie bazata hanaka ba" ta gano Camera a wayanta.
     "first selfie?" ta kanne mishi ido, ta matsa inda yake ya duk'o zasu d'auka hotan, ya d'aura yatsanshi d'aya saman yatsanta mai d'aukan hotan, sannan suka d'auka a tare su duka suna dariya.
 
  Sunyi kyau su dukansu, nan take ta mayar dashi wallpaper, "Haka zaiyi zamanshi" shima a wallpaper d'inshi ya maidashi, sunyi kyau sosae, ba don sunso ba sukai bankwana, sai da ta daina ganinshi, ita kuma ta shige gida tana nunama Husna wayanta.
    Yana mik'a Hafsat wurin mai kula da ita, kai tsaye d'akinshi ya wuce don yasan Momie tayi barci yanzu, Yasseer harya kwanta, da yake daman d'akin nasu ne su biyu
     "Big bruz harka dawo?"
   "Kasan kuwa lokaci yanzu?"
       "anma dai tashi zakayi ka bani labari, yau babu barci"
   Girgiza kai Yasseer yayi, "So nake in kwanta da wuri, gobe da safe akwai inda nakeson zuwa"
      "Haba bruz daga dawowanka? Ina zakaje kuma?"
   "K'yauyen da Naje Bautan K'asa, akwai abinda na barone mai matuk'ar mahimmanci da nakeso inje in duba, abun yana raina bazan iya k'ara lokaci banje ganinshi ba"
    "Tohh ka bari ka k'ara hutawa zuwa jibi sai muje tare, anma yanzu ga azumi ga gajia"
   "jibi daren Sallah kenan mu dawo ranar sallah? Ba komai fa kasha zamanka, namafiso inje ni kad'ai, kai dai kamun addu'ah Allah ya bani sa'ar abinda zanje nema"
     "Ameen d'an uwah, Momie dai taa barka ko?" cikin wasa yace "ai aikin lallashin ta barni zuwa nayi tun dawowatah daga gidansu Rabiah" dariya sukayi,
     "Yaka baro Saudat d'in?" Yasseer ya tambayeshi
  "ya akai kasan wurinta naje?"
  "Momie ta fad'amun mana, ko wacce mai sa'ah ce ta iya samun zuciyar little bruz har haka?"
   "Saika ganta zakasan nima mai sa'ahne sosae dana sameta"
   "kana sonta da yawa gaskia"
   "sosai kuwa bruz, ina sonta fiye da rayuwatah"
   "gaskia naso ganin wannan Saudat d'in taka, da alama Momie ma tana ji da ita, anma ai zanje ganin Husna"
    "yanzu ma bara in nuna maka hotunanta"
    "karfa in ganta tafi kyau a hoto akan zahiri"
   Dariya yayi "Saudat ganinta ai yafi jinta"
   Folder da yake ajje hotunanta ya shiga, sannan ya mik'a mishi wayar bayan ya gano mishi hotunanta.

©Rabiatu sk msh

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts