♡MATATAH CE♡
♡♡♡♡♡♡
57
©Rabiatu sk msh
®NWA
Labari....Ilileee
www.babymsh.blogspot.com
Tun bayan tafiyar Najib sai Saude taji gidanma yafi mata daɗi a haka, Hajia na ɗan aikata gidan Husna harsun saba sosae, hankalinta yanzu kwance har mantawa take da wani Najib, tunanin Yasseer ma kullum k'ok'arin yakiceshi take.
Ranar friday sati uku da tafiyar Najib, da aiki suka tashi gidan kamar za'ayi wani manyan bak'i, kuma taa lura Momie na cikin farin ciki fiye da kullum, sai dai bata tambayeta dalili ba don bata faɗa mata ba,
Sai bayan saukowar masallaci suka kammala, a gajiye Saude ta fito daga kitchen ɗin batama jira an gyara wurin da ita ba, tafiya kawai take bata kallon gabanta sai dai ta jiyo sallamar mutum, idanunta akan hanyar shigowarshi, harta buɗe baki zata amsa mishi sallamar ta tuna maganarshi daya faɗa mata.
"Idan har zuciyan mutanene a jikinki, karki k'ara nunamun fuskarki!!!" maganar taa shigeta sosae, kafin ya shigo ta lallaɓa ta koma can jikin bango ta laɓe bayan ta amsa sallamar can cikin mak'oshinta, tana hangenshi ya shigo ya wuce, ya k'arayi mata kyau sosae, anma kamar yaa ɗanyi rama.
Saida ta tabbatar ya shige ɗakin Momie, sannan ta fito tabar wurin, ɗakinta ta shige, bata k'ara marmarin fitowa ba.
Tun shigarshi gidan yaketa hangen inda zaiga Saude anma bai ganta ba, shiyasa ma kai tsaye ya wuce ɗakin Momie yasan zai sameta a can, anma bai ganta ba, Momie ita kaɗai ke maganar ta anma tunanin ta inda Saude zata fito yake. Dubara tazo mishi na tambayan Momie,
"Nifa tun zuwana banga Hafsat ba ko tana wurin Mamanta?"
"A'ah tana wurin lesson ne" shiru yayi donshi ba amsar da yaso ta bashi ba kenan,
"Aina ɗauka tana wurin Mamanta"
"A'ah" kawai Momie tace mishi, baiso hakanba, sai kuma yaga wannan kamar dama ne dazai fara yima Momie tuni akan hakk'in Saude.
"Momie itafa Sauden yaushene zata fara zuwa makarantar?"
"Haba Saude fa, ai ita yanzu tayi girma da zuwa makaranta, nasan bazata so ma tana shiga aji da k'annanta ba"
"A'ah Momie, shi karatu ai baida babba babu yaro, idan har tanaso ko inane zata iya, in kuma bataso sai mu k'yale andai fita hakk'inta"
"Hakane, anma tunda gaka kazo saika nema mata makarantar daya dace"
"tohm shikenan Momie, tana ina?" ya samu dai ya tambayeta.
"k'ila tana ɗakinta ko, gajiyar aiki nasan tana hutawane, tun asuba bata zauna ba" wani irin daɗine yazo mishi,
"Momie Saude ita tayi girki?"
"Kusan ita tayi fa, don yanzu Talatun ma ita ke tayata" fara'arshi saita k'aru yau zaici girkin Saude, har k'agara yayi su tafi dinning cin abinci, anma kuma shiru babu Saude, kuma yaji Momie batayi maganarta ba, sai yanda Momie zatayi maganarta yake anma bata kula ba.
Haka duk ranshi ba daɗi ya yini a ɗakin Momie, sallah kawai ke fitar dashi don karma ya fita Saude ta shigo bainan, har dai Momie da taga dare ya kusa bai fita ba tace "yau kuma bazaka fita ba?"
"A'ah Momie, yau ranarki ce babu inda zanje nan zamuyi ta fira" aikam taji daɗi sosae da maganarshi, ta ɗauka daga sallahn isha'i ma zai wuce ya kwanta, sai gashi har 10:30, yana jiran Saude tazo mata saida safe.
"Naga alaman yau anan zaka kwana, kaga ni tashi barci nake ji"
"Momie yau kuma korata ake?"
"Ya zanyi na kori Babana, barci nakeji gobe ka dawo muyi firan"
"Tohm mu kwana lafia" ya tashi ya tafi yanajin haushin barcin wurinnan na Momie yau, duk da haka a falo ya zauna yana hangen hanyar da zata fito yana kallon dole.
Saude da taga haka saita fasa fitowarma, ta koma ɗaki ta kwanta ko kaɗan bataji daɗin rashinma Momie saida safe ba, barcin k'arya ta ringayi duk sanda ta aika kiranta da rana don batason fita, saida dare ya raba tsakiya sannan ya hak'ura ya kwanta.
Washe gari da asuba taje gaisheta tana gama sallah tasan bai dawo masallaci ba, da yake yaa daɗe baiyi barci ba, sai bai farka da wuri ba sanda ya tashi harsun gama break fast, ta koma ɗaki, yinin ranar ma wasan ɓuya suka ringayi, kota fito bata bari su haɗu.
Ranar asabar kenan haka har dare basu haɗu ba, gashi lahadi yakeson komawa, kusanma haushin kanshi ya fara ji, kenan maganar Ahmad gaskiyane yana son Saude? Shiyasama duk ya damu ya ganta, miye ma a jikin Sauden da zaiso ya gani? Tunaninta ya matsa mishi har baison zama shi kaɗai, tashi yayi yabar ɗakin Momie yama fasa son ganinta.
Lokacin ita kuma Hafsat na wurinta ta matsa sai dai ita zata rakata ta kwanta, ta rik'o hannunta suka fito, tana ganinshi ta juya tun kafin ya gansu anma ta makara saida Hafsat ta mishi magana tanata so ta k'wace hannunta taje wurinshi.
Tsura mata ido yayi duk da yaji daɗin ganinta a zuciyarshi, amma saiya kauda kai, ta saki hannun Hafsat kawai, ta juya tabar wurin, yabi bayanta da kallo harta shige.
Hafsat ce ta kamo hannunshi, sannan ya maida hankalinshi kanta.
"Uncle ina sweets ɗina?"
"Sorry Hafsat kinga yau ban fita ba, gobe zamuje in siyo miki"
Ta washe baki, "gobe zaka fita dani yawo ko?"
"eeh mana"
Harda tsallenta "Yauwah gashi babu ckul"
Ya ɗaga mata gira "Hakane fa, tohh kije ki kwanta da wuri"
"tohm uncle Good night"
"bye karki manta da addu'ah" tun daga nan ta fara kware baki tanayi donma yaji bata manta ba, murmushi kawai yayi, shi yanzu harya daina mamakin surutun Hafsat, shekarunta biyu anma labari kam kamar mai sauke hadda, wayau ne da ita sosae shiyasa tun wuri aka kaita prep.
Yau bai fito ba, break fast ma sai dai yayi ma Momie waya aka kai mishi, na rana ma shiru bai fito ba, Momie ta aika aka mata kiran Saude,
"Shiru bakici abinci ba, yayanki ma bai fito ba duk yau"
"Naci a kitchen Momie"
"Bana hana ba Saude? Ɗauki na Yayanki kikai mishi"
"tohh Momie?"
Bata iya musa mata, anma da akwai yanda zatayi bazata je ba, cikin sanyin jiki ta harhaɗa mishi, ta kwasa ta tafi gabanta na faɗuwa har ta shiga.
Yana kwance abubuwa sun mishi yawa, duk zuciyarshi cunkushe take, haushin kanshi kawai yakeji, tunanin Saude, Soyayyarta, da kuma son ganinta sun rikita mar k'walwa, ya ɗauke wayanshi ya kira Ahmad.
"Masoya! Ananan da Saude an manta damu"
"wace Saude? Bazan iya ba Ahmad, gaba ɗaya na fara tsanar kaina, ita zuciyar daman haka take? Bazatayi shawara dani ba akan wacce ya kamata taso ba sai Saude"
Ahmad na mishi magana Saude ta shiga ɗakin, a falo ta aje mishi saman centre table, sai kuma taga kamar bazai san an kawo ba, ta tafi ta faɗa mishi, ta jiyoshi yana magana.
"Haba Ahmad baka ganta ba, bak'yauyah ce ta k'arshe, ko ɗaurin zane bata ita ba ballantana ɗan kwali, sai afkin wanka anma babu wayewa, ni wallahi haushinma ganinta a haka nake" dafe k'irjinta tayi tuni hawaye suka wanke mata fuska,
"bak'yauyen mutum fa Ahmad duk yanda zaka mishi yananan dai da duhun k'yauyenshi, duk inda zai shiga kuwa...." abunda ta iya saurara kenan, da gudu ta tafi zata bar ɗakin, wurin sauri k'afarta harta zame ta faɗi, ba k'aramin zafi taji ba haka ta daure da sauri tabar wurin.
K'arar faɗuwar mutum da yaji ne ya fito dashi, anma baiga kowa ba sai dai girkin da aka aje mishi, bayanta yabi anma harya fito baiga kowa ba, Momie ya gani da shirin fita ta fito,
"Sai yanzu ka fito?"
"eeh, fita zakuyi ne?"
"eeh anma bazan daɗe ba, Saude takai maka abinci ko"
Ya samu amsar tambayarshi kenan itace ta shiga ɗakinshi, "eeh Momie" rage tsawonshi yayi inda Hafsat take,
"Ba magana don za'aje anguwa?"
"A'ah akwai"
"tohh ina mamanki?"
"tana ɗakinta"
"muje ki rakani" yanda Momie bazata ji ba yayi maganar, ya kama hannunta.
"Momie muna zuwa plz"
"owk ta sameni a mota" tayi gaba su kuma suka tafi.
Hafsat taa rigashi shiga ɗakin da Saude take, da murnarta donta faɗa mata tare suke da Najib sai kuma taga tana kuka.
"Mama kuka kike?"
Ta share hawayenta tana k'ak'aro murmushi, "waya faɗa miki kuka nake?"
"nina gani da kaina Momie, kuma kin hana kukan rigima"
Kuka ne ta k'ara fashewa dashi, a k'alla ta samu damar da zata faɗi damuwarta ko zata samu sauk'in zuciyarta, duk da tasan Hafsat bazata fahimci komi ba,
"ba kukan rigima nake ba Hafsat, inayi ne don in rage bak'in cikin zuciyatah, miye don an haifeni a k'yauye? Ni bani da kyau ne? Ko kuma wani mugun abunne k'yauyenci? Mutane da yawa sun gujeni silarshi, harda babanki Hafsat, nasan shima dalilinshi kenan na barina, Uncle ɗinki Najib ma abinda ya sanyashi tsangwama ta kenan, Momie kaɗai ke sona Hafsat, kawuna ma ya tsaneni saboda maraicina, babu fa wanda na ɗaurama kaina, ko kinsan inda k'yauyencinnan yake a jikina in cireshi in huta?"
Kamar tasan me tace, ta girgiza mata kai, murmushi tayi, "Naji daɗi da baki tashi a k'yauye ba Hafsat....."
Muryar Momie suka jiyo tana k'wala ma Hafsat kira, harta tafi da gudu kuma ta dawo, hannu ta saka ta share mata hawaye, sannan ta koma ta gudu.
Murmushi tayi tabi Hafsat da kallo, kawai sai taga mutum tsaye a bakin k'ofa ya harɗe hannuwanshi biyu yana kallonta, jikinta na kyarma ta tashi tayi hanyar fita don taa rasa inda zata shige a ɗakin, ya k'ara mamammake k'ofar yanda babu wurin fita, ta kasa haɗa ido dashi a hankali tace,
"Kayi hak'uri"
"Dame fa?" ya tambayeta cikin wani irin salo.
"Na saka kaa k'ara ganina"
Ita har yanzu bata manta da wannan maganar ba kenan? Ya shareta kawai.
"menene damuwarki?" ta ɗan ware idanunta duk da bata ɗago fuskarta ba,
"ba komi" ta juya da sauri zata koma, saboda hawayen dake k'ok'arin zubo mata.
"meyasa kike kuka?"
Muryarta na rawa alaman kuka yaci k'arfinta tace "kaina kemun ciwo" ta bashi amsa duk taa matsu yabar ɗakin.
Tohh meya shigo dashi shida yace baison k'ara ganinta? Ko kuma wani wulak'ancinne zai k'ara mata.
"Sanya mayafinki kizo muje" ya katse mata tunani, ta k'asan ido take son kallonshi donta tabbatar koda ita yake magana,
"Dake nake, ki sameni a waje" ya fita kawai ya barta, sannan ta sauke ajiyar zuciyah, ta k'arema ɗakin kallo babu wata sai ita dashi, anma tana gudun ta fita ya mata faɗa ko bada ita yake ba, ko kuma tak'i zuwa tayi laifi.
Saida ya gaji da jira ya dawo don kanshi, yace taje su tafi, ta tashi ta bishi zuciyarta na mugun bugawa, harta shiga motan, tunani kawai take a ranta ina zai kaita?.
©Rabiatu sk msh
0 comments:
Post a Comment