New Post

Sunday, 5 March 2017

MATATAH CE 51

♡MATATAH CE♡
   ♡♡♡♡♡♡
             51

©Rabiatu sk msh
      ®NWA
                   
            Labari....Ilileee

www.babymsh.blogspot.com

  Cikin tashin hankali Saude ta tashi ta fara waigen ɗakin bata ga Yasseer ba, a ruɗe ta tafi k'ofar toilet ko yana ciki anma bata jiyoshi ba, kamar kaɗangaruwa ta ringa bin bango harta lek'a ciki bainan, tsananin tashin hankali batasanma sanda ta fita daga gidanba, tafiya mai nisa tana nemanshi har wurin masallaci duk da ba'a shiga ba, haka ta daure ta dawo gida,
      Sai lokacinma ta duba duk kayan Yasseer bai bar komi ba, katifarnan kawai ya bar mata da kayan amfani, tana ɗaga filo sai gaa mak'udan kuɗi nan yaa bar mata, sai lokacin ta ida yarda lallai Yasseer yaa barta, wani irin kuka ne yazo mata na tausayin kanta.
  Ta saka hannu tana shafa cikin jikinta cikin muryar kuka tace "Shikenan mahaifinka yaa tafi ya barmu, ya tafiyanshi, ya gudu ya barni dakai kaɗai" ta k'ara fashewa da wani kuka,
    "Lallai sai yau na k'ara yarda ni marainiyah ce, kayi kuskure Yasseer, kayi kuskure daka shigo rayuwatah ka cutar da wannan raunanniyar zuciyar tawa, kaa riga kaa gama da zuciyatah, tunda ka koyar dani yanda zan soka, kuma ka gudu ba tare daka nunan hanyar dazan daina ba" kuka yaci k'arfinta, tana dukan bango tana kuka, komai na duniyar gaba ɗaya yaa daina mata daɗi.

    Gari naa fara haske ta zari mahafi sai gidan Kawu Ado, shi ɗinne dai komai zai mata bata da inda zata kai kukanta daya wuce can, idanunta duk sun kumbura, duk da rufe fuskar da take en k'auyen sai binta suke da kallo. Harta isa gidan da sallamarta ta shiga, sunyi shimfiɗa tsakar gida suna cin ɗumame, duk suka saki baki suna kallonta.
  Tun kafin tayi magana Gwaggo bilki ta mata tsawa "Yau kuma da wacce tsiyar kikazo mana? Halan kinyi bak'in halin da mijin naki ya fasa tafiya dake?"
  Munanan tambayoyin da suka dira kunnanta kenan daga bakin Gwaggo, anma da yake hankalinta a tashe yake saita k'ara fashewa da wani sabon kukan, "Guduwa yayi, yaa gudu yaa barni"
    "Tohm yanzu waya aika kiranki anan da kikazo kina faɗa mana? Ko sakinki yayi?"
   "A'ah Gwaggo bai sakeni ba,  don Allah ku taimakeni"
   Sai yanzu baba Ado yayi Magana "Taimakon k'aniyarki? Lallai duk shekararnan ba'a rainamun hankali ba irin haka, mu ga yaranki ko, mu ringa zagaye gari gari muna nemo mikishi ko ya kikeso ayi? Yaron da bamu taɓa ganin kowa nashi ba bamusan daga inda ya fito ba, koko so kike ki dawo mana nan da zama?"
   Yayi shiru yana mata wani irin kallo, "Tohh ko ɗaya bazai yiwu ba, shi kanshi bazai iya da bak'in halinki bane shiyasa ya gudu ya barki, don haka tunda muma mun samu kinyi nesa damu ki kiyaye ni, aradu na k'ara ganin ko sawunki ne hanyar gidannan sai naayi bala'in saɓa miki"
  Gwaggo tace "k'warai kuwa malam, don kokai kaa yarda ta zauna ni bazan k'ara zama da ita ba, mijinta ma yaa gujeta ballantana mu"
   Wani irin kuka ta fashe dashi tana rok'arsu, "Don Allah Kawu ka taimakeni, kai kaɗai ka rage gatana, bani da kowa a duniya sai kai"
   "ni ɗinma fiddani a lissafinki, indai ni kike kallo a matsayin gatanki tohh bakki dashi, don haka ki tashi ki ficemun nace"
   Kuka taci gaba dayi tana rok'arshi anma yayi biris da ita, da yaga bata da niyyar tafiya ma icce ya ɗauko ya rakata har waje a guje, ya tsaya yana ci gaba da masifa, tsabar kuka Saude har sik'ewa take, dak'yar ta iya kai kanta gida.

   Lallai babu mai laifi a cikin rayuwar data tsinci kanta kamar kawu Ado, yana sane da cewa basu san asalin Yasseer ba, basusan kowa nashi ba suka bashi aurenta don tsanar da suka mata, da sun samu wani wanda yake garin komai talaucinshi komai nakasunshi yafi mata wannan auren k'addarar da suka ɗora mata, maganar Yasseer ce ta ringa dawowa mata kullum ta tambayeshi garin da yake,
   "Kina tsoran kar in gudu in barki ne?" sai yanzu ne ya tabbatar mata da abunda yake nufi, duk da yarda dashi da tayi bata taɓa sakawa taa kawo hakan a ranta ba.

Bayan wata bakwai...
Rayuwar Saude har tafi ta daa muni, tana gida ita kaɗai sai abunda ke cikinta, ko waje batason lek'awa don da an ganta ne za'a fara mata wak'a irin tasu ta k'auye, ana sakar mata habaici, har yara gulmanta suke idan zata wuce, mijinta yaa gudu yaa barta, ita kam kullum cikin saka ran dawowar Yasseer take, don shine yasan inda take, tana saka ran duk daɗewa zai nemeta.
   Wata rana tana zaune ita kaɗai tayi tagumi cikin watan haihuwarta, cikinta ne ya fara murɗawa, nak'uda tazo mata gadan-gadan, gashi babu kowa gidan sai ita kaɗai, daman babu mai zuwa inda take, ta dinga ihu tana neman agaji, tayi matuk'ar galabaita,
   Cikin sa'a saiga k'awarta Hanne zata wuce ta shiga gidan, daman ita kaɗaice koda tana gidansu Gwaggo takejin tausayinta, ba ɓata lokaci ta tafi tazo da unguwar zoma, lokacin harta fara fita hayyacinta, ita ta taimaka mata harta haifo k'atuwar yarinyarta jajir kamar babanta. Farine kawai ta ɗauko na Babanta anma komai nata na mamantane, kamarsu ɗaya da Saude kamar tayi khaki.
   Unguwar zoma da Hinde ne suka taimaka mata suka gyarata da jaririyar tata, zata tafi ta ɗauko kuɗin sallama ta bada ta tafi tana ta godia, Hinde ita ta samo maiyi ma Saude wanka da erta, idanta samu lokaci tana zagayota, da en tsirarun en k'auyen masu zuwa su bama idonsu abinci, su gwaggo dai ko lek'e har akayi suna.
   Cikin kuɗin da Yasseer ya bar mata ne, ta saima yarinyar kayan sakawa,  tasa aka yanka ma yarinyar ragon suna, taaci suna Hafsat, saboda yanda takeson sunan, kuma babu dai wanda zai zaɓa ma er tata suna bayan ita.

   Kwanci tashi babu wuya wurin Allah, Hafsat ta fara girma, taayi wayau ita ta zama abokiyar firar Saude, ita take ɗebe mata kewar mahaifinta, ko wasanta take da Saude tayi shiru tana tunani zata rarrafo ta tafi inda take, tana ɗaukarta tayi ta wangale baki.
   Zara dai bata barin dame, hafsat nada kusan shekara biyu komai ya fara fin k'arfin Saude, duk kuɗin dake hannunta sun k'are tunda daman ba juyasu take ba, harta fara siyarda kayan amfanin gidan, rayuwar hafsa take tausayamawa, batason ta tashi cikin k'uncin rayuwa ta saba da babu da yunwa, idanma ta zauna a haka ai saidai yunwa tayi ajalinsu tunda babu mai taimaka mata, sannan kuma wacce amsa ma zata bama hafsat idan taa girma ta tashi tambayarta waye mahaifinta? Taa rasa sana'ar da zatayi, gashi k'auyen ba kowane ke bada aikatau ba, kowa baison fidda kuɗi.

   Wata matar dake ɗaukar en aiki takai birni taje ta samu ta faɗa mata buk'atarta nason ta samar mata gidan aiki inda za'a dinga biyanta koda abincin da zataci ne,
  Baba haja ta nisa tace "Anya Saude zaki iya kuwa? Nifa banan kusa nake kai en aiki ba, can birnin Abuja nake zuwa"
   "koma a inane zan iya zuwa wallahi baba Haja, wake gareni a k'auyen da bazan iya tafiya ba? Ai yin nesan ma shine zaifimun Alkhairi"
   "tohh Allah yasa hakan, daman akwai wata Amaryah ce don ko haihuwa batayi ba, tace in samo mata er aiki, Allah yasa ta amsheki don basu cikason en aiki yara ba"
   "Ameen baba, ni indai zata amince wallahi aikinta ko yakai girman me zan iya mata"
   "Tohh ai shikenan, sai kije ki fara shirye-shirye idanna tashi tafiya zan nemeki"
  Tayi ma baba Haja Godia sosae sannan ta tashi ta tafi.

   Tana shirin tafiya tana tunanin yanda Yasseer ya mata, saida ta gama shiri ya tafi ya barta, ita yanzu tama fidda rai da dawowarshi, don indai bai manta da ita ba tsawon lokacinnan yaa isa ya nemeta.
   Ko sati biyu ba'ayi ba, baba Haja ta aiko mata tafiya taa tashi, en kayanta da suka rage daman duk taa sayar, ta tattara en kuɗinta suka tafi, bayan taje tayima mai gidan hayar da suke godia, don daman cewa yayi kuɗin da Yasseer ya biyashi ko zata shekara biyar a ciki bazasu k'are ba, ta bar mishi dai ta tafi.
    Wa yaga Saude a Abuja, ita da ko k'auyensu bata taɓa bari ba, nima dai naa tafi in shirya don dani za'aje Abujar nan

©Rabiatu sk msh

Related Posts:

  • MAKASHINKA 29-30```MAKASHINKA...```           29-30 ©Rabiatu sk msh     A hanyarsu ta komawa gida, sadeey tayi shiru tana sauraren Shamsuddeen yana ƙara mata nasiha, ba … Read More
  • MAKASHINKA 27-28```MAKASHINKA...```           27-28 ©Rabiatu sk msh Zuwan yayanta ya hana shamsuddeen ya fara koya mata, duk inda zataje da yayanta take zuwa kullum suna tare, har ya gama wee… Read More
  • MAKASHINKA 25-26```MAKASHINKA...```          25-26 ©Rabiatu sk msh Shamsuddeen zaune ya haɗe fuska wuri ɗaya, ranshi a ɓace yake kallon hafeez dake ta dariyarshi hankalinshi kwance … Read More
  • MAKASHINKA 21-22```MAKASHINKA...```            21-22 ©Rabiatu sk msh _Washe gari_ Da wuri sadeey tayi shirinta natafiya makaranta domin ta san yau babu driver, Daddy ma haka tundda wuri… Read More
  • MAKASHINKA 23-24```MAKASHINKA...```            23-24 ©Rabiatu sk msh Ana tashi ckul, ta hangoshi yana jiranta, anma ta shareshi sai data ɓata mishi lokaci sosae, duk en makarantar a… Read More

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts