♡MATATAH CE♡
♡♡♡♡♡♡
65
©Rabiatu sk msh
®NWA
Labari....Ilileee
www.babymsh.blogspot.com
Saudat ta gama jere ma Rabi'ah kayan ciye-ciye, Husna sai sannu take mata, sai gata ta dawo daga rakiyan Yasseer.
"Sannunku da zuwa Aunty Rabi'ah" kallonta ta ɗanyi.
"Saudat ko?" ta ɗaga mata kai tana murmushi, "Sannunki kinsha aiki, ya gajia?"
"ai ba wani aiki bane"
Taje zata kama Husna dake k'ok'arin tashi dak'yar, "Sannu Aunty"
"Yauwah Aunty Saudat"
Rabi'ah tace "waih! Sannu kinji, gaskia kina k'ok'ari"
"ai saima yazo kanki zaki sani" inji Husna.
"ni? Allah ya rufamun asiri, wahalan ɗaukan ciki, haihuwa ga raino mutum ya tsofe tunda wuri"
"Miye abun rufin Asiri? Kardai kicemun har yanzu kina da wannan Ra'ayin naki tun muna ckul, wollah garama ki canja kin sanmu dangin miji dai"
"akwai hanyar samun yara da yawa ko ban haihu ba, yanzu dai a barni in gama cin amarcina dan Allah ki dainamun maganarnan kina kadamun gaba"
"Baki ma da hankali wallahi, wannan ba tunani mai kyau bane, inma bazaki haifa mana ba zamu auro mai haifa mana"
Filon kujera ta ɗauka ta jefa mata, "bakinki ya faɗama mak'iyanki, kinsan Allah ko wata naji anyi ma kishia zuciyatah tafasa take" Husna daria kawai take mata, ta k'ara ɗaure fuska, "Allah wannan ba abun dariya bane" bata saurareta ba, dariyarta kawai taci gaba dayi, yanda takeyi dariya take bata sosae.
Da yake Saude da Najib suna waje, Rabiah da ɗan rage murya, "wai da gaske wannan ce Saudat ɗin Najib?"
"itace mana"
"daga ina ya samota?"
"ɗiyar Momie ce, daga k'auye tazo"
"lallai kice kyawawan en matah na k'auye, na birni kwalliya da wayewa zasu nuna musu kawai"
"eeh mana, Yayanmu ma a can zamu samo mishi ta biyu"
"Allah idan bazaki dainamun maganarnan ba yanzu zanbar miki gidanki"
Ta rufe baki tana dariya, "yi hak'uri matar babban yaya, na daina"
"karma ki daina ɗin"
A gidan Husna Rabi'ah ta yini har dare, sai fira suke da Saudat kamar wanda suka saba, da yake taji ita Najib zai aura kuma dai yanzu bazata nuna mata wayewa ba, har abincikan data girka ta nemi ta koya mata, taji sun mata daɗi sosae, nan ta koya mata harma da wanda bata nema ba.
Dare ya fara nisa Yasseer yazo ɗaukan Rabi'ah, bai shiga ciki ba yayi parking wajen gidan sannan ya mata waya ta fito, yana zaman jiranta a mota cikin duhun daren Saudat tazo wucewa, cikin tafiyarta ta nutsuwa a hankali take saka k'afafunta, ta amso ma Husna sak'o mak'waftansu.
Hakanan yaji yanason ganin fuskar kowacece, ya bita da kallo cikin duhun darennan har lek'enta yake gashi ta juya baya, Rabi'ah na tsaye ta fito ga mota a kulle, sai k'wank'wasawa take baimasan da ita a wurin ba, gaba ɗaya taa gama k'ulewa. Saida ta dawo ta gabanshi sannan ya lura ya buɗe mata.
A harzuk'e ta shiga ta zauna sai maida numfashi take, juyawa tayi ta fara dukan k'irjinshi, "matah kake kallo ko, bakama lura ina tsaye ba" rik'e hannuwanta yayi sai k'ok'arin k'wacewa take.
"Waya faɗa miki mata nake kallo? Nifa ginin unguwarne suka burgeni, nake tunanin ko nan zamu gina gida idan mun dawo?"
"mak'aryaci, wallahi saika faɗamun ko wacece kake kallo"
"wa kikaga ina kallo nifa banmasan da wata mace a wurin ba"
"k'arya kake" ta k'wace hannuwanta taci gaba da dukanshi, duk ta hargitsa mishi tunani cikin motar dak'yar ya iya rik'eta, gam ya haɗata da k'irjinshi yana sumbatarta, bai saketa ba saida ta nutsu sannan, saida ta k'ara kai mishi duka a k'irji tana harara sannan ta gyara zama tana maida numfashi.
Kwana ɗaya suka k'ara, suka ɗaga moscow bayan Momie ta mishi gargaɗin ya daina daɗewa bai dawo ba,
Ranar da suka tafi, da yamma a ranar Husna ta haifi jaririyarta mace, ba k'aramin murna sukai da zuwanta ba, sai Saudat hidima ta k'aru, har ranar suna itace mai hidima da bak'i ko kaɗan bata nuna gajiyawarta, yarinya taci suna Maheera, kamar Najib na jira, washe garin suna yazo ya koma da ita, aka samo mata mai kula da ita da jaririn.
Ranar Monday ta koma makaranta SS1, gaba ɗaya hankalinta ta maidashi akan karatunta, soyayyarta da zuciyarta kuma duk ta mik'asu wurin Najib.
A moscow, tun komawar Yasseer abubuwa suka dawo mishi sabo, gaba ɗaya yanzu addu'anshi daya ɗaga hannu Allah ya nuna mishi Saude, yasan yaa cutar da rayuwarta kullum cikin nadama yake, so yake su haɗu kota yafe mishi laifin daya mata, gaba ɗaya ko wurin aiki baida sukunin yin komai, a gida ma yafison ya zauna shi kaɗai yana tunanin rayuwarsu ta baya, tohh idan Saude bata k'auyensu tana ina? Kullum tambayar da yake ma kanshi kenan.
Rabi'ah ta shigo ɗakin da wata irin shiga mai jan hankali, a kusa dashi tayima kanta masauki, ta saka hannu ta shafi fuskarshi cikin shauk'i.
"Yauma tunanin kake? Banson ganinka cikin damuwa, kuma kak'i faɗamun damuwarka"
"Rabi'ah plz, inason hutu" ya faɗa idanunshi a rufe da alama damuwan ta fara fin k'arfinshi.
"Yaushene ka fara korata a ɗakinka? Nifa damuwarka kawai na tambaya, ka faɗamin ko miye saimu zauna mu tattauna"
"babu abunda ke damuna, don Allah ki k'yaleni hakanan"
"bazan tafi ba, saika...."
Wani irin tsawa ya daka mata, "kece damuwatah! Ki fita na..." yanda ta zabura ya sanyashi shiru duk baiji daɗi ba, gaba ɗaya tunanin Saude ya fara zautashi.
Hannuwanta ya kamo ya rik'e, "don Allah Rabi'ah, ina cikin damuwa ki barni in samu kaɗaicewa kona ɗan lokaci ne" duka takai mishi, sannan ta mik'e ta fice daga ɗakin, binta yayi da kallo, ita dai dukan miji bai mata wahala, daya ɓata mata rai sai duka, Allah sarki Saude da ko magana yake mata kanta na a k'asa take saurarenshi.
Su Saude suna samun hutu Momie ta fidda ranar zuwa k'auyensu, Najib kamar ya jawo ranar yakeji, gani yake kamar anma riga da an bashi Sauden.
Daren ranar suna zaune a falo kamar kullum suna fira, kallon Ball yake taa biye mishi itama tana tayashi, gaba ɗaya hankalinshi na wurin.
"wai nida ball ɗinnan waka fiso?"
Aje remote yayi ya maida hankalinshi kanta, "karki k'ara haɗamun soyayyatah da wani abu, nafi sonki fiye da yanda nakeson kaina ma"
"luv uh as much dear, in hakane meyasa ka k'yaleni"
"farin ciki nakeji Saudat, wanda ban taɓayi ba, gobe zamuje k'auyenku kawu ya bani aurenki, idan harya bani ke babu sauran abunda zai min shamaki da mallakarki"
"ka ɗauka ma ya baka fa"
Fargaba ce kawai a ran Saude daren ranar, batasan yanda kawu zai amsa maganarta da Najib ba, tasan ya tsaneta komai zai iyayi don ya k'untata mata, kuskurenta tun farko data faɗa mishi Yasseer bai saketa ba ya gudu.
Ranar batayi barcin kirki ba, cike take da fargabar yanda gobe zatazo mata. Barci bai daɗe da ɗaukarta ba aka kira Sallah, a kasalance ta tashi tayi Sallah, ta jawo Qur'an ɗinta ta fara karatu, tana gamawa dai Addu'anta kawai Allah yasa komai yazo musu da sauk'i wurin kawu.
Bata samu komawa barci ba, Momie ta aiko mata ta fito idan taa shirya don safko zasuyi, Najib ne zai kaisu ita da Momie, da wuri suka kama hanya zuwa k'auyensu Saude.
©Rabiatu sk msh
0 comments:
Post a Comment