New Post

Sunday, 5 March 2017

MATATAH CE 41-45

♡MATATAH CE♡
   ♡♡♡♡♡♡
           41-45

©Rabiatu sk msh
      ®NWA
                   
            Labari....Ilileee

www.babymsh.blogspot.com

   Rik'e hannuwanta yayi yana shafawa, sannan yayi murmushi,
   "Rabi'ah?" sautin dariyarta ne ya fita sannan ta sakeshi, bayan sun katse wayan.
   "Haba ko baki rufemun ido ba, ina shigowa gidannan jikina ya bani kina ciki"
   "Hhm ba waninnan, kaida kace bazakaje ka ganni ba, ni kaɗaice na damu da ganinka ma"
   "A'ah ai don nasan kina gidanne"
   "Hhm ka cika wayau"
      "Faɗin Gaskia dai"
  Sannan takai hannu ta kunna hasken,
   "Da alama kaa gaji Masoyi, bara in jiraka a fallo ka watsa ruwa"
   "aini nama manta da wani gajia fa tunda na ganki"
   "hhm tohh shknan, kayi sauri dai banso ka zauna da yunwa"
   Yayi daria "tohh ko zaki tayani?"
  Sai data tsaya tana ɗan tunani, sannan ta ware ido "I wish i could, anma ai akwai lokaci" tana mayar mishi da murmushinshi
   
Rabi'ah kenan, k'awar Husna ce tun suna sckul, harsun zama tamkar en uwa, suna gari ɗaya anma har kwana tanayi a gidansu Husna saboda Yasseer, tunma kafin su fara soyayya, har yaji shima tayi mishi ya bayyana mata sirrin zuciyarshi, ba wani ɓata lokaci ta amince mishi, yanzu haka babu wanda baisan da maganar soyayyarsu ba, itace ma wacce zai aura.

   Cikin mintuna kaɗan ya gama wankan ya fito, sannan ya zura kaya, zaune ya tardata saman carpet ta jera abincin tana jiranshi, lokacin an kira Sallahr Magrib, ya wuce masallaci itama ta shiga toilet ɗinshi tayo alwala.
  Bayan yaa dawo anan suka baje falo, tana zuba mishi abinci, ya kalleta sannan yace,
   "Da alama akwai magana bakinki"
   "Kuma akwai damuwa a zuciyana ba"
   "Duk meya kawo hakan?"
  Ta k'ara ɓata fuska, da alama abun na damunta sosae,
   "k'auyen can mana, Allah banison zamanka k'auyennan, daga bazaka daɗe ba, harfa cewa kayi bazaka zauna ba, anma shine kayi daɗewarnan"
   "to ai gashi naa dawo, duka wata nawa ya ragemun in gama duka?"
   "Hakane anma nidai don kak'i, anma wallahi tun farko da nayima Abba magana an barka nan"
   "A'ah ni nafison inyi bautar k'asarnan inda aka turani"
  "Saboda ka ringa ganin en matah ba"
  Ita maganarshi ma dariya ta bata, "K'auyene fa Rabi'ah"
   "k'auyen basu da idanune? Na tabbata ko duk makafine ka wuce ta inda suke dolema suji sunason mallakarka, kana dakyau Yayanmu, ka mallaki duk wani abu da mace zataso a wurin namiji, en k'auyen daka raina nasan suma rububinka suke"
  Har yanzu dariyar yake mata "kedai kin cika kishine kawai, anma plz ki daina wahalar da kanki akan en matan k'auye, ina laifi ma kiyi kishi da wayayyu en birni?"
   "Indai a kanka ne ban raina kishi da kowa ba, ina sonka da yawa ne, ni kaina bansan kalar son da nake maka ba dahar nakejin idanna rasaka zan iya rasa raina, kuma da inyi kishi da wata a kanka, k'aramun in rasaka, don bansan kuma halin dazan shiga ba"
    Mummunar faɗuwar gabane tazo mishi, shi sai yanzu ma ya tuna da yana da wata mata, yaya kenan idan Rabi'ah tasan shifa yanzu mai aurene? Gaba ɗaya jikinshi yayi sanyi, zufa duk taa jik'a mishi riga, bai iya bata amsa ba, sai dai yayi shiru kawai yana tura abincin dak'yar.

   Washe gari kowa yaa hallara a dinning suna break fast, Momie, Daddy, Husna, da Rabi'ar Yasseer, suna cin abinci sai satar kallonshi take, tana so su haɗa ido, anma ko kallonta baiyi ba, ganewa ne kawai Rabiah batayi ba anma tun jiya Yasseer cikin damuwa yake, ta k'asa ta sanya k'afa tana zunguroshi, ya ɗaga kai suka haɗa ido, murmushi ta sakar mishi, da sauri ya maida kanshi yana ci gaba da wasa da cokali,
    Murmushin mugunta tayi, sannan ta haɗa yatsunta biyu na k'afa, ta kamo yatsarshi ɗaya ta matse, har saida yaso yayi k'ara, ya ɗago kanshi da sauri ta tuntsure da daria, Husna naa lura dasu, daria take ciki-ciki, sannan ta shanye tace,
     "Wai yaya har yau naji shiru, nifa na k'ara biki yazo musha shagali, Gani k'anwar Ango kuma k'awar Amarya"
  Wani kallo ya watsa mata, "Ke! Ina wasa dake?"
     Can ciki tace "to ni ba k'awar budurwarka bace"
   "Kika ce?"
  "Ba komai, kawai ina tunanin Yaya Najib ne"
   "ai saiki bishi makarantar"
  Ta turo baki zata k'ara magana Daddy ya katsesu, "Ya isa hakanan!" ya kalla momie, "Daman maganar da nace miki inasonyi dashi kenan idan yaa dawo, tunda dai bautar k'asar ake jira ya k'are, sai a saka lokaci wata ɗaya bayan yaa gama"
   "Hakanma yayi Alhaji, Allah ya kaimu"
    Daɗine ya kama Rabi'ah, da gudu ta tashi ta tafi ɗakin Husna cikin jin kunya,
     "Ameen, kinga tare dana Husna kenan" itama tashi tayi tabar wurin, Daddy ya ɗaga kai yana kallon Yasseer daya haɗiye abincin daya saka baki dak'yar,
   "Bakace komi ba, hakan yaa maka dai-dai?"
   "eeh yayi"
      "Yauwah toh abinda nakeso ka gane, yarinyarnan tana sonka sosai, amanah ce a wurinka, don haka kaci gaba da rik'e amanarta, ban yarda da abinda zakai mata ka ɓata mata rai ba"
   Momie tace  "Gaskia ne Alhaji, an riga an tsayar da magana a tsakaninku, ban yarda da wata doguwar magana ba daga baya, kowanne zama ɗan hak'uri ne, don haka komai ya faru tsakaninku, kuna dai daitashi basai kowa yaji ba"
   "Insha Allah Momie, Daddy zan kiyaye" ya faɗa dak'yar, yana k'ok'arin ɓoye tashin hankalin daya shiga. Robar ruwan Faro mai sanyi ya ɗauka ya kafa a baki, saida ya shanyeshi tas baima sani ba sannan ya sauke robar, ko kan abincin bai k'ara bi ba ya wuce ɗakinshi yana tunani,
    Saude MATATAH CE, anma ko kaɗan banijin sonta a raina, Rabi'ah itace Masoyiyatah, kuma wacce ta dace dani, itace nake burin na k'are rayuwata da ita, anma abunda zai faru idanta gano ina da wata matar bamai kyau bane, banson na rasa Rabiah, itace burin zuciyatah, anma ya zanyi da auren Saude?

K'AUYE
  Daren Ranar da Yasseer ya tafi, dak'yar Saude ta iya barci ita kaɗai, sai rungumar filo take, tunaninshi kawai ya hanata ta runtsa, ji take daman yana tare da ita, ta k'ara lumshe ido tana rik'e da filo kamar yana tare da ita,
    "harda wani cewa kake 'Saude abunda kika bani ma ya isa har k'arshen rayuwatah bazan manta dake ba' Hmm ni kuma saika bani yanayin da bazan taɓa iya rayuwa babu kai ba, ka daure ka dawo da wuri, ina buk'atarka" tayi murmushi, ita kaɗai tasan yanda takeji akan Yasseer, cikin kewarshi barci ya ɗauketa,

   Tunda Safe bugun gidan da ake ya tasheta, ana dukan k'ofar kamar za'a ɓallata har saida ta tsorata, ta mik'e ta tafi tana tunanin ko waye? Tambaya tayi "Waye?"
    "Uwaki ce" saida gabanta ya faɗi da taji muryar Gwaggo Bilki, ko tunawa da itama batason yi, jikinta na kyarma ta bangajeta ta shiga gidan,
    "Lallai, kin samu wuri ko tunawa bakiyi damu, duk yacce zakiyi dai baki da kamarmu, shegiya mai bak'in hali," ita dai bin bayanta kawai tayi suka shiga gidan, ko gaisuwarta ma bata amsa ba, ta shige ɗakin,
   "naji ance mijinki yayi tafiya, abunda ya bar muki zaki ɗauko ki bani"
   "ai ba daɗewa zaiyi ba, babu abunda ya barmun"
   "k'arya kike! ni zakima k'arya? Tun kafin kiyi wayau muke ciyar dake, ke kinyi gidan miji zaki gujemu ko" sai faɗa take tana ɗage ɗage duk ta watsa en kayan dake cikin ɗakin, ta hankaɗa katifa bata samu komi ba, da taga dai babu kuɗin da take nema, ta buɗa kwalayen da kayan abinci suke ta kwashi son ranta,
   "idan kin hana kuɗi ai bazaki hana wannan ba" bata tanka mata ba, ta ɗauka hartaa fita ta dawo data tuna bata duba k'asan laida ba, tana ɗagawa kuwa sai ga kuɗi, ta ɗago tana kallon Saude,
   "Hinyeh! Munafuka, ni zakima k'arya ko?" takai mata rank'washi, sannan ta k'irga kuɗin,
    "Duk dubu Ukun ma zan tafi dasu, tunda ba daɗewa zaiyi ba kin gane" ta kalleta k'walla suka zubo mata, ta k'ara kai mata bugu "kin tsuramun k'attan idanunki kina kallona, muna fuka" ta gama zazzaga mata, sannan ta kaɗa buje tai gaba,

©Rabiatu sk msh

Related Posts:

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts