♡MATATAH CE♡
♡♡♡♡♡♡
74
©Rabiatu sk msh
®NWA
Labari....Ilileee
www.babymsh.blogspot.com
A hankali take tafiya, ko kallon gabanta batayi, harta kusan fita daga layin, tafiya kawai take tana jefa k'afa batasan inda take dosa ba, wayanta na k'ara a handbag anma batasanma tanayi ba, saida wani mai adaidaita sahu ya kusan ture ta sannan ta dawo hayyacinta, yanata faɗa ko kallonshi ma batayi.
Duk inda take tunanin zataje, tunaninta ya gama tsayawa akan komawa k'auye, domin kuwa bata da inda yafi can, bata tsaya wani ɓata lokacin tunani ba ta wuce inda zata shiga motan Katsina, gaba ɗaya zuciyarta taa dake, kukanma nemarshi tayi ta rasa.
Yasseer ne kwance a gadon asibiti yana kallon sama, hawayene kawai ke ratata a idanunshi, ko k'ifta idanu baya iyayi, anya kuwa ya kyautawa Saude da Hafsat? Anya kuwa hakk'in Saude zai barshi? Wannan rashin adalci har ina?
Najib ne ya share mishi hawaye, bayan ya zauna gefenshi, "Meyasa bruz? Meyasa zakayi saurin yanke wannan ɗanyen hukuncin?"
A hankali yace cikin zafin ciwo da kuma zafin da zuciyarshi ke mishi, "saboda ban cancanci Saude ba, ban cancanci kasancewa da ita ba, laifukana a wurinta sunfi k'arfin a lissafa, hak'urinta da kawaicinta yayi yawa, bazan iya ci gaba da tauye mata hakk'i ba, shiyasa da sauri na yarda da umurnin da Momie kemun, mezaisa naci gaba da rik'e igiyoyin aurenta bayan abubuwan dana mata a baya? Da bakinta ta faɗamun yanzu ta daina sona, kai take so"
Ɓata rai sosai Najib yayi, "ka dainama faɗar haka bruz, babu sauran soyayya tsakanina da ita, Na tsaneta, tsanar da ba'a taɓa ma wani halitta ba, bazan taɓa bari mace ta haɗani da ɗan uwana ba"
"ka daina faɗar haka, kuskurene tayi da babu wani ɗan Adam da yafi k'arfin yinsa, mutuniyar kirkice, kuma mace ta gari da babu kamar ta a duniyarnan"
Mik'ewa yayi ya fita daga wajen ɗakin da aka kwantar da Yasseer, don maganar Saude ma wani bala'inne yake k'aruwa a cikin zuciyarshi, bazai taɓa iya daina sonta ba, anma abunda ta mishi bazai iya mantawa ba, cikin zafin rai ya fiddo wayanshi ya fara neman layinta, saida ta kusan katsewa ta ɗauka bata ma duba ko waye ba, ta kara a kunne, ba tare da tace komai ba, tama manta data ɗauka wani kira, sai dai ta barshi da sauraren k'aran tafiyan Mota hakan ya tabbatar mishi da har taa tafi.
"Kin gama abunda ya kawoki kin tafi ko? Kin riga kin gama cutar da zuciyatah da soyayyarki, saida akazo wurinda bazan iya rayuwa babu ke ba zaki fitomun da asalin halinki, kin cutar dani Saudat, kin sakani nayi k'azamiyar soyayya da matar aure, kin cutar da farin cikina"
Wani irin numfashi taja cikin sark'ewar kuka, Buɗa baki take anma ta kasa magana, saida ya gama faɗa mata duk abunda yazo bakinshi, sannan ya kashe wayan ya barta da tarin bak'in ciki.
Lokacin data isa gidan dare yayi sosai, gaba ɗaya ta gama galabaita, dak'yar ta iya kai kanta gidan, yasha gyara yayi kyau kaman bashi ba, ta kwantar da kanta jikin k'ofar sannan ta fara k'wank'wasa, ta daɗe a haka kafin azo a buɗe, Kawu da Gwaggo ne sukazo buɗewa, ana buɗe k'ofan ta faɗa da yake jingine take a jiki, da sauri Gwaggo ta rik'ota tana sallallami.
Kamata tayi suka shigar da ita ciki, tambayarta suke meya faru gaba ɗaya hankalinsu ya ɗaga, kasa basu amsa tayi saidai kuka kawai, ga wani irin zazzaɓi daya rufe ta, sai wani irin numfashi mai zafi take fitarwa, su duka babu wanda bai tausaya mata ba, gwaggo ce ta samu zani da ruwa tana sanya mata a jiki, a haka harta samu barci.
Washe garima tana tashi sai kuka, idan tana tuna abubuwan da suka faru da rayuwarta ba k'aramun tausayama kanta take ba, dak'yar ta iya musu bayanin abunda ya faru ganin yanda hankulansu suka tashi.
Su duka suka saki salati, Kawu harda kuka bilhaƙƙi ya tausayawa ma Saude, karo na farko tunda ta taso a hannunshi, cikin kuka yake cewa.
"laifin mune, mu mukaja miki koma menene ya faru dake, bamu rik'e amanarki da kyau ba, kin rik'emu tamkar iyaye, anma muka mayar dake baiwah, muka lalata rayuwanki, mun cuceki Saude mun cutar da kanmu"
Da sauri Saude ta rufe mishi baki, "Don Allah ku daina faɗar haka kawu, kun rik'eni na tashi a hannunku, ku kuka ciyar dani kuka tufatar dani baku taɓa korata daga gareku ba har kuka zaɓamun miji kuka aurar dani, kunmin abunda ya dace, ku daina ɗaurawa kanku laifi"
"kayyah Saude! Tirr da hali irin nawa, dana kasa rik'e ɗiyar yayana, don Allah ki yafe mana Saude"
"don Allah ku daina kawu, ni ban rik'eku da komai ba"
Gwaggo da itama tunda suke magana kuka take, ta bala'in tausayawa rayuwar Saude, "Anma dai mutanennnan tirr da taimako irin nasu, Allah zai saka muki abunda suka miki"
"A'ah gwaggo karki musu Allah ya isa don Allah, mutanen kirki ne, sun rik'eni tamkar jininsu, na ɗauka abunda sukamun a matsayin ajizanci na ɗan adam"
Kawu yace "Naji daɗi da kika baro musu er su a can, domin kuwa babu mu babu su har abada, yanzu ne zasu san kema kina da gatanki"
Duk sai taji kamar an yaye mata kaɗan daga cikin damuwarta, daman tunaninta kawai yanda su kawu zasu amsheta, a ranar ya sanya aka gyara mata ɗaya daga cikin ɗakunan gidan da akayi da kuɗinta, donshi yanzu har sana'a yake da kuɗin data bashi, gatan da bata samu ba tana yarinya yanzu suke nuna mata, ko kaɗan basu son suga ta ɓata rai yanzu su duka zasu damu, wani kulawa sosai suke mata kamar er da suka haifa.
Kwanciyan Yasseer Asibiti, Rabiah da Najib ne ke kula dashi, ko yaushe tana tare dashi duk da bai wani bata fuskar da zata ɓata mishi rai, hakanan ma saiya rufe ido kaman yana barci, anma hakan bai hanata kula dashi ba, don ta samu labarin duk abunda ya faru, wani k'ara sonshi ma take da taji labarin ya saki Saude.
Satinshi biyu aka sallameshi daga asibiti, ya gama warkewa sai dai damuwa da baza'a rasa ba, tare da Rabi'ah suka koma gida Momie, tana k'ara kula dashi anma ko kaɗan bai sakar mata fuska, wani irin haushinta yakeji idan yana tuna da cikinshi da zata zubar, yasan halinta na tsayuwa akan magana ɗaya indai tace zatayi bazata fasa ba.
Ahmad Ya kalla Najib daya gama bashi labarin duk abubuwan da suka faru, domin kuwa shi amininshi ne, bashi da abunda zai iya ɓoye mishi, don tun dawowanshi ya lura yana cikin damuwa, bayan fasa auren da akayi.
"kana nufin yanzu ka daina son Saudat ne?"
Wani harara Najib ya mishi, "duk labarin dana baka tambayar da zakamin kawai kenan? Bazaka faɗamun Saudat bata kyauta ba, kaman ma baka damu da abunda tamun ba"
"indai bata kyauta maka ba, abunda aka mata ma ba'a kyauta ba, ka ɗauka kaine ita wanne irin hali zaka shiga a yanzu? Ka tausaya mata itama mana"
"Babu tausayi tsakanina da macen da taci amanatah, sauran tsakaninsu ne, ko kana so kacemun inci gaba da son matar da yayana ya aura?"
"Yasseer ya riga da yaa saketa, kuma a addinance aurenka da ita ba haramun bane duk kuwa da yana raye, kuna son junanku kai da Saude, ni banga wani laifi ba anan ciki"
"ko babu sauran mace a duniya bazan iya zaman aure da Saudat ba, ballantana akwai mata da yawa a ko ina"
"Yau kuma kaida bakinka? Kar dai kacemun kaa daina son Saudat"
Wani wuri a hannun Ahmad Najib ya nuna, "menene wannan?"
"tabon ciwo mana"
"yaa warke ba?" ya ɗaga mishi kai cikin rashin fahimta.
"kamar haka ciwon son da nake ma Saudat zai warke wata rana"
©Rabiatu sk msh
0 comments:
Post a Comment