♡MATATAH CE♡
♡♡♡♡♡♡
76
```second to the last page```
©Rabiatu sk msh
®NWA
Labari....Ilileee
www.babymsh.blogspot.com
Su Momie sun isa k'auyensu Saude, kai tsaye gidansu suka wuce, Momie da kanta ta shiga gidan tun daga soro ta fara k'wala sallama.
A tsakar gida taci karo da su Saude Gwaggo bilki na sanya mata jan lalle a k'afa, suna ta nishaɗinsu kamar basu ba, duk da Sauden ma tayi rama anma ko kaɗan babu alaman damuwa a tare da ita.
Ita ta amsa ma Momie sallamanta, taji daɗin ganinta don murna kamar taje ta rungumeta takeji don har Abada kallon uwa take mata.
Gwaggo ta gama saka mata laida a k'afan ta mik'e tana mata sannu da zuwa, "ku shigo daga ciki Hajia" ko kaɗan bata canja mata ba akan abunda sukama Saude
"A'ah Gwaggo nanma yaa isa kusa da y'ata,"
"tohh sannunku da zuwa, aikam kunsha hanya"
"aikam dai" saida ta kawo mata ruwa mai sanyi da zoɓon da take siyarwa, sannan ta zauna suka fara gaisawa kamar daa can yanda suka saba.
"kunyi Sa'a kuwa Mallam ɗin yana kasuwa, anma na aika yanzu za'a kirashi"
"to ai ba komi"
Ita da Saude dai sai er kunya, tunda ta gaisheta bata k'ara ɗagowa ba, sai wasa take da lallen hannunta, tanaso ta tambaya Momie Hafsat, anma ta kasa, da yake Gwaggo ta basu wuri sai dai ta tsinkayo muryar Momie.
"Saude kinyi mamaki da ganinmu ko? Mun kasa samun sukuni tun bayan tahowarki, tabbas mun miki laifi, mun sani saboda kullum cikin dana sanin abunda na miki nake, kin tunasar dani akan karna yanke hukunci cikin fushi, anma nai burus nahau dokin zuciyah na miki hukuncin da yafi qarfin laifin da kika aikata, hak'ik'a ke alkhairi ce, kuma Allah kaɗai yasan abinda yake ɓoye na shigowarki rayuwarmu, gani da k'ok'on barana, ina fatan zaki yafe mana abunda muka miki nida yarana Saudat"
"Haba Momie, kefa mahaifiyatah ce, duk abunda kika zartar a kaina dai dai ne, babu uwar da zata nema gafara a wurin er ta, ballantana ni ban taɓa rik'e iyalinnan a raina ba, kunmin abunda bazan taɓa mantawa ba, Alkharin da kukamun babu abunda zan iya saka muku dashi, tsakanina daku sai dai addu'ah"
"nagode Saudat, kyawawan halayenki basu misaltuwa, nayi bak'in ciki da cewar ke ba 'yatah bace, anma bazan iya rasaki a matsayin suruka ba" dammn gabanta ya faɗi, ta buɗa baki tana kallon Momie kamar bata ida yarda da maganarta ta k'arshe ba.
Bata iya cewa komai ba sai ga Kawu Ado ya shigo, da iyayen ledoji a hannunshi, Gwaggo ta tarbeshi ta amsa tana mishi sannu da zuwa, fura ce ya kawo a dama ma su Momie da nono mai yawa, harda gasassun kaji da lemuka, shima bai nuna mata wani sauyi a fuska ba suka gaisa faran-faran, sannan ta nema magana dashi suka shiga ɗaki, a saman kujeru suka zauna sannan aka k'ara gaisawa.
"tohh Malam, gani dai da k'ok'on barana, laifine an riga an yishi, basai anyi tone-tone ba, don Allah ayi hak'uri kuskurene irinna ɗan adam"
"haba Hajia, ai wannan magana tuni taa wuce, Allah ya yafe mana gaba ɗaya"
"Ameen"tayi shiru kuma tana tunanin yanda zata ɓullo da sauran maganar.
"tohm sai kuma idan babu damuwa, nazo ne ina neman alfarmar in koma da Saude a can ɗin dai"
"Can ina Hajia? Saude kam ai tazo gida" kawu ya faɗa ba bayan ya fara rage fara'arshi.
Rok'onshi ta shigayi, kamar ta durk'usa mishi bama kamar data faɗa mishi wai har da wakilan Najib ta taho a ɗaura aure kawai, ai kauda fuska yayi sam baisan da zancen ba. Don bazai manta da wulak'ancin da Yasseer ya musu ba har yanzu, aka tara mutane ya bashi auren Saude anma ya butulce musu a k'arshe.
Cikin damuwa take faɗa mishi halin da Najib ɗin ya shiga, tana faɗa mishi duk tausayi ya cika mishi zuciyah, ya share zufa yana fita da hular dake saman kanshi, ba haka yaso ba anma Hajia duk taa karyar mishi da gwiwa, bazaiso ya k'ara bada Saude inda za'a wulak'antata ba, don yanzu ji yake da ita kamar tsoka ɗaya a cikin miya.
"Shikenan Hajia, ni yanzu bani da ta cewa, sai abunda yarinya ta zaɓa, anma ni bazan tilastata akan abunda bataso ba"
Murmushin jin daɗi Momie tayi, "Nagode Mallam Allah yabar zumunci, ni zanyi magana da Sauden"
Tana daga waje, ba laɓe take musu ba, anma tana jiyo maganganunda suke, saida ta zubda k'walla data ji halin da Najib ya shiga, tabbas itama rayuwa bata mata daɗi da babushi, ita kaɗai zata kulle kanta a ɗaki tayi ta kuka idan ta tuna shikenan yanzu sun rabu, ba k'aramin daɗi taji ba da maganar da Momie tazo da ita ba, anma ta kanne kawai.
A gabansu Kawu Momie ke neman amincewar Saude, kanta a k'asa bata ɗago ba cikin kunya tace "bani da wani zaɓi sai abunda Kawu yace, koma miye zanyi biyayya a kanshi"
"karki damu Saude, banda burin k'ara tauye miki hak'k'i, don Haka zaɓinki shine nawa" inji kawu.
Momie tace "kada ki k'wari kanki, ki fito fili ki faɗa mana abunda ke ranki, wallahi bazan taɓa ganin laifinki ba Saudat" ita duk sun ɗaureta da maganganunsu, ta jawo hijab ta lulluɓe fuskarta, Murmushi sukai su duka sun Fahimceta.
Washe gari su Momie da wuri suka dawo aka ɗaura aure, don cewa tayi bazata tafi ko ina ba saida ɗiyarta, taron jama'a akai sosai wanda tunda ake ɗaurin aure ba'a taɓayin kamarsa ba a k'auyen, Kawu ya kashe kuɗi sosai akaci aka k'oshi harda masuyin guzuri, da wuri Momie ta ɗauka amarya suka wuce Abuja, tun kafin subar k'auyen ta fara kuka, yanzu son zama take sosai da su Kawu ko kaɗan batason rabuwa dasu. Don dai kawu yace bazai iya barin k'auyen ba, saboda shi ya saba tun kakanni anan ya tashi.
Kai tsaye Momie gidan da Najib da Saude zasu zauna da ta wuce da ita, daman taa saka an gama gyarashi, suna zuwa mai gyara Saude na jira aka shiga gyarata, cikin ɗan lokaci ta fito tsaf Amaryarta, kafin a gama gyarata daman Momie taa wuce gida lokacin har Magriba ta kusa.
Najib na zaune falo ya fara samun sauk'i, shida Ahmad ne yaazo dubashi suna zaune shima duk ya damu da halin daya ganshi ciki.
Su duka suka gaisheda Momie, sannan Najib yace "Momie ina kikaje harda kwana baki faɗamun ba?"
"neman aurenka naje, Alhmdlh dana dawo na iske ka fara samun sauk'i"
Ya kalleta da mamaki "aurena kuma?" ta ɗaga mishi kai cikin tabbatarwa. "koka manta kaa bani zaɓine?" yayi shiru.
Sannan ta kalla Ahmad "yauwah daman ko ban iskeka ba zan nemo ka ne, kazo ciki inason magana dakai"
"tohh Momie" tana shiga ya mik'e yabi bayanta.
Najib dai binsu yayi da kallo kawai, maganar Momie ma dariya ta bashi, a hakan za'a mishi aure dare ɗaya kawai?
Bai tashi shan mamaki ba saida yaga Ahmad yazo mishi da sabbin ɗinki, ya tsareshi saida yayi wanka, ya shirya shidai dariya ma suke bashi.
"wai kai wanne irin wasa ne wannan? Binku nake fa kawai inga inda zaku tsaya"
"tohm ai daman ango lallaɓashi ake"
Saude na zaune tsakiyan makeken gadonta, tana lulluɓe cikin mayafi ko ina k'amshi ne a jikinta, dare ya fara nisa duk a tsorace take, ta jiyo k'aran motoci, sannan ta saki ajiyar zuciyah.
Tananan Zaune taji an buɗe k'ofa, Najib dai tafiya yake kawai, duk da maganganun da sukai da Momie kafin ya tafo bai k'arasa yarda wai da gaske aure aka mishi ba.
Yana buɗe ɗakin dai-dai lokacin Saude ta yaye mayafin kanta saboda zafin da ake, ai suna haɗa ido yayo baya da gudu Ahmad na niyyar fita ya rik'oshi.
"Saudat ce, da gaske aure akamun?"
I m Apologising wanda auren Najib Da Saude bai musu daɗi ba, anma har idan Saude bata aura Najib ba sak'on da nakeson isarwa bazai kammaluba, bincike nayi sosai kuma dai duk maganar ɗayace, Auren Saude da Najib bai haramta ba koda kuwa Yasseer yana raye, harda hakan yasa ban kashe Yasseer ba kaman yanda wasu sukaso😄 inda a gaske abun ya faru fa? Don dai karin maganar nan ta hausawa (ana barin halak don kunya) anma ba wani haramcin zama a cikin auren Saude da Yasseer, Nagode sosai gareku Masoyana. Masu cewa zasu daina karantawa! Daman page ɗaya ya rage, ko babu wanda ya karanta Alhmdlh fatana dai Allah ya bani ikon kammalawa lafiya.😄
Inata yinshi a gurguje, kudai ci gaba da hak'uri dani plz, zan fara hidima ne, bazan samu lokacin typing ba shiyasa.
©Rabiatu sk msh
0 comments:
Post a Comment