New Post

Sunday, 18 December 2016

HARAMTACCEN ZAMA 1-2

💖HARAMTACCEN ZAMA💖
     ♠♠♠♠♠♠♠
                   1-2
Rubutawa
      ©Rabiatu sk msh
              ®NWA
Labari
    Ilileeee

Kwance take a tsakiyar gado, tasha lullub'i da shiga ta alfarma, k'amshi ne yake tashi ta ko ina a jikinta, an mata irin lullu'bin da ake ma Amare danginta sai shirye-shiryen tafiya suke.

A cikin mayafin nata, wayar tace ri'ke a hannunta tana kan chatn sai murmushi take cikin farin ciki abinta.

Ibraheem ne Yace "Amarya kinsha 'kamshi.
    Sai da tayi fari da ido sannan ta fara typin
  Majeeda "Haba dear banson haka fa😭 ko ina amsa sunana Amarya ai sai randa na ganni a gidanka"
     Yace "hakane fa tawan, shiyasa ba wani kishi nake da wannan auren naki ba"
    Majeeda "Ay 'kara ka kwantar da hankalinka kam, don wannan auren nawa dashi da babu duk ɗaya"
    Yace "kedai ki kulamin da abinda nake matu'kar so, karki bari ya 'kwacemin a darennan plz"
  

A zuciyarta kamar ya soka mata wu'ka takeji, anma a zahiri sai tace "menene zan kula maka da?😉" cikin zolaya tayi maganar hakan ya sanya har sai da tayi dariya a zahiri.

Duk 'yan ɗakin saida suka jita hakan ya sanya wata Abokiyar wasanta tace "ikon Allah! Ni majeeda na tab'a ganin amarya irinki, ranar aurenki anma baki damu ba ko kukannan bazakiyi ba?" wata tace "kema kin faɗa, nima tun d'azu nake gulmarta a zuciyatah, ban ta'ba ganin Amaryar da batayi kuka ba ranar aurenta koda babu hawaye"

"Haba Aunty zaynabu, aure ai abin farin ciki ne ga masoya, ko wanda kika ga suna kukan don rabuwa da iyayensu ne"

Cikin lullub'in nata sai data gatsina sannan tace a ranta "Allah ya tsareni da zama Masoyiya da majeed, wlhy ko kad'an aurennan bai dameni ba tunda ba sonshi nake ba".

Saida kowa ya gama mata bankwana ya tafi, sannan ta yaye mahafin da aka mata lullu'bi dashi daman duk yaa dameta, hafsatul kiram ta zato ido tana kallonta "wai majeeda badai da gaske bakiyi kukan amarcin ba?" tace "ke banson iskanci uwar meye a cikin kukan amarcin? Aishi wlhy bai isa inyi kuka saboda aurenshi ba tunda ya yarda aka aura mishi ni".

Tace "Allah ya huci zuciyarki"  majeeda tace "Ameen" tana gyara kwanciya "sai yaushe zaki tafi?" hafsa tace "Yanzu fa don naga ma shirin korata kike" yanayin da tayi maganar ya bama majeeda daria tace "wace ni da korar Hafsatul kiram? Idan ma anan zaki kwana wlhy muyi kwanciyarmu anan"

Hafsat ta ri'ke baki "kinga rufamin asiri, Ya umar har ya iso sai waya yakemin" majeeda tace "yayi masoyan asali" ta rataya jikkarta tace "Tohm Asubah ta gari majeedar majeed" harara takai mata, don ta tsani a haɗa sunanta dana majeed, ko bankwanarta ma bata amsa ba.

Ta duba online har ibraheem ya sauka, ta kashe wayan kawai ta murgina ta kwanta idonta cike da barci ga gajia.

Sai da barci mai daɗi ya fara ɗibanta, kamar daga sama taji an jefo mata wani abu samanta, a firgice ta farka haɗe da tashi zaune tana shirin kurma ihu tayi ido huɗu dashi.

Cikin masifa ta sauko daga kan gadon "Miye haka majeed zaka wani jefo min Abu ina cikin barci na?" galala yake mata kallo sannan Yace "ke kin d'auka barci ne ya kawo ki gidannan?" sannan ya girgiza kai yana ta'be baki "tohh kima ajiye wallahi tunda kika yarda kika aureni, kazar amarci ce aka bani in kawo miki don nasan da kwa'danta kika kwanta".

"Allah ya kiyayemin, ba ro'karka nayi ba don haka ka kwasheta ka ficemin daga ɗaki, kuma wallahi ka sani kaine kayi kuskuren aurena"
       "ke kin isa in shigo da ita kuma in fita da ita? A cikin garar ne aka haɗo miki da ɗaƙinnan da zakice in fice miki daga ɗaki?
     "oho dai, kaima kasan nafi 'karfin ɗakinnan ai da duk wani abu daka mallaka"

Bai tanka mata ba ya juya zai fita, ta 'kwala mishi kira "kazo ka ficemin da ledar nan nace" bai ko juyo ba wani haushin ya 'kara zo mata iya wuya, daman abinda tafi tsana kenan a halayyar Abdul majeed koda suna gida, jin kai da miskilanci

A k'yamace ta saka hannu ta ɗan ɗauki ledar kamar wacce ta ri'ke abin k'yama, ta wuceshi ta riga shi fita ta tillar da laidar.

A zafafe ya juyo cikin jin haushi yana kallonta, itama kallonshi take ko ɗar babu a fuskarta tana maida numfashi.

Baiyi wata-wata ba ya nufi inda take ya ɗaga hannu ya kai mata wani wawan mari, cikin zafin nama ta kauce har tanajin hucinshi.

©Rabiatu sk msh

Related Posts:

  • HAKA SO YAKE 1-2💕💕  *```HAKA SO YAKE```* 💕💕             💗💗💗💗💗        &nbs… Read More
  • HAKA SO YAKE 3-4💕💕  *```HAKA SO YAKE```* 💕💕             💗💗💗💗💗        &nbs… Read More
  • HAKA SO YAKE 5-6💕💕  *```HAKA SO YAKE```* 💕💕             💗💗💗💗💗        &nbs… Read More
  • A YINI ƊAYA 41💀 *A YINI 'DAYA* 💀    👹💀            💀👹             &… Read More
  • HAKA SO YAKE 3-4💕💕  *```HAKA SO YAKE```* 💕💕             💗💗💗💗💗        &nbs… Read More

0 comments:

Post a Comment

Popular Posts