💖HARAMTACCEN ZAMA💖
♠♠♠♠♠♠♠
9-10
©Rabiatu sk msh
®NWA
Labari...
Ilileee
Haka rayuwah taci gaba da tafiya, babu jituwa sam tsakanin majeed da majeeda, tana da shekara 6 ko wucewa zatayi sai majeed ya saka mata 'kafa taa faɗi, gata da masifa ita ma ta ɗago suyi tayi dak'yar iyayensu suke rabasu.
Cikin haka kaka ya kwanta ciwon ajali, ya tara 'ya'yan nashi duka ya fara musu wasiyya sannan yace "na sanku da zumunci, da kuma son zumunci, ku k'ara rik'e junanku ko bayan raina, a duk lokacin da naga khadija da Abdul majeed sai wani abu ya zomin a raina, ji nake kamar nine da mahaifiyarku, naso ina da rai inga ranar aurensu, anma kumin al'kawari ko bayan rai na zakuyi musu aure"
Alhaji Sani Yace "Insha Allahu kaka bazaka mutu bama sai kaga auren nasu"
Kaka Yace "inaa Sani, kai dai kawai ku rik'e alk'awari, don ciwonnan nawa jikina yana bani bana tashi bane, ko bayan raina ban yafe ma duk wanda ya saɓa wannan alk'awarin ba a cikinku, majeeda itace matar majeed" tare suka haɗa baki "Insha Allah baba"
Maganar daya faɗa k'arshe kenan, sai dai yayi kalmatus shahada, rai yayi halinsa.
Sunji mutuwar mahaifinsu sosai, sunyi kuka, tare da k'ara jaddada maganarshi ta k'arshe suna k'ara ɗaukarta da muhimmanci.
Sai dai wani Abu, majeeda da majeed suna girma suna k'ara rashin jituwa a tsakaninsu, tun suna ɗaukar abun nasu yarinta ce, har sunkai lokacin da majeeda ta gama secondry school, majeed ma ya gama makarantarshi har ya fara aiki, Aunty zainab kuma anyi mata aure da shekara ɗaya.
Yau gidansu majeed ta shirya ta tafi, zahra nata yi mata tsegumin bata son zumunci sai dai ita tazo, yau dai ta shirya driver ya tafi kaita.
Tayi sallama falon ta shiga, babu kowa, saita wuce ɗakin umma ta gaisheta sannan ta fito ta nufi ɗakin da zahra take.
Hangota tayi ta k'urama t.v kallo da alama a tsorace take, lallab'awa tayi har inda take ko sanin taa shigo ma batayi ba, sannan ta k'wala k'ara saitin kunnanta.
Aikam ta mik'e a firgece daman duk a tsorace take, ko tsayawa kallon majeeda batayi ba ta zunduma waje a guje tama rasa inda zata nufa, itama majeeda tabi bayanta da gudu tana mata dariya sai so take ta rik'ota, anma ina tama k'i tsayawa wuri ɗaya sai dai taji tayi karo da mutum.
Da sauri taja da baya zuciyarta cike da fargaba ta ɗago idonta taga ko waye, suka haɗa ido da majeed yana mata wani irin mugun kallo.
Ganin shine itama taja tsoki kawai ta nufi wurin zahra da tayi tsuru-tsuru tana kallon majeed, tace "muje matsoraciya, kinsan bazaki iya ba kika saka film ɗin horror ke kaɗai a ɗaki kina kalla"
Tace "Tohh yana iya tunda ina son kallo? Film ɗinne yayi kyau" har lokacin zahra satar kallon majeed take daya kasa motsawa daga inda yake har lokacin.
Ya daka musu wata uwar tsawa "baku da ido ne da zaku bugi mutum da wasan banzanku na k'ananan yara kuma bazaku bashi hak'uri ba?" zahra tace "kayi hak'uri yaya" tana zungurar majeeda itama ta bashi hak'uri.
Majeeda tace "hak'urin me kike bashi? Shine fa ya shigo ta hanyarmu" ta murguɗa baki sannan ta juya taci gaba da tafiyarta.
Yace "lallai ma yarinyar nan, yauma rashin kunyar zakimun?" waiwayen ɗakin ta kamayi sannan ta ɗago idonta itama ta watsa mishi wani irin kallo sannan tace "babu yarinya anan"
"idan nazo na murɗe wannan shegen masifaffen bakin naki kyamun bayani"
Tace "zan zauna ne kamar sakara ka murɗemin baki? Kaima kasan ba tsoranka nake ba wallahi".
Nan fa faɗa ya kaure, majeed ya kasa wucewa ɗakinshi saboda yanda majeeda ke gasa mishi maganganun, ranshi yayi matuk'ar ɓaci shiyasa yarinyar ko ganinta bai sonyi, masifaffiya ce kuma tayi matuk'ar rainashi.
A zafafe ya nufeta da niyyar kai mata mazga, dai-dai lokacin umma ta fito jin hayaniya, majeeda na tsaye inda take ko gezau ba tayi ba
Umma tace "Aaaaah, majeed mezan gani haka? Abin naku ya wuce faɗa a baki har duka zaka kai mata?" cikin jin zafi yace "Umma zan tsaya k'aramar yarinya kamar wannan ina faɗa tana faɗa ne? Ai wallahi sai ta gane ni ba sa'anta bane".
Tace "ai sai dai in baka faɗa ba wallahi, donni bazan tsaya kana nunamin iko ba"
Umma tace "tohh kuci gaba kunji ko? Tunda a gabana ma bazaku bari ba, kana babba anma bazaka daina shiga harkar k'annan ka ba, zo ka wuce ɗakinka" tana nuna ma majeed hanyar ɗakinshi.
Ya wuce yana aika ma majeeda da harara, itama harararshi take harya wuce ɓangarenshi, sannan taja hannun zahra suka wuce ɗakinta.
©Rabiatu sk msh
0 comments:
Post a Comment